Waye Bahaushe?

0
51

A yanzu sanin kowa ne ne Bahaushe na asali sai an yi ƙoƙarin tantancewa, saboda irin cuɗanyar da Hausawa suka yi da wasu ƙabilu wadda ta yi sanadiyar sauyawarsu. Don haka siffa ko harshe ba ya tabbatar da Bahaushe.

Hausawa sun yi cuɗanya da ƙabilu masu yawa ta fuskar kasuwanci da ƙodago da addini, kamar, Fulani da Barebari da Buzaye da Nufawa da Yarabawa da Jukunawa da wasu ƙabilu na Afirka masu yawa ciki har da Buzaye da Larabawa.

Wannan cuɗanya ta haifar da auratayya da cakuɗuwar al’adu a tsakaninsu da Hausawa, wanda hakan ya yi sanadiyyar mayar da wasu Hausawa ta fuskar harshe da al’ada duk da cewar hakan bai hana su iƙirarin asalinsu ba. Za a iya fahimtar Hausawa ta waɗannan fuskoki:

1. Hausawa ta fuskar harshe waɗanda babu kwata a bakinsu (tsamin baki wajen kasa furta wasu sautuka a harshen Hausa)

2. Hausawa ta fuskar muhallin zama. (gari ko yankin da suke zaune)

3. Hausawa ta fuskar addini. Yawancinsu musulmi ne ko maguzawa.

4.Hausawa ta fuskar halayya da al’ada.

5. Hausawa ta fuskar asali. Waɗanda suke iƙirarin su Hausawa ne iyaye da kakanni.

Don haka a yanzu Bahaushe shi ne mutumin da yake ba shi da wani harshe sai harshen Hausa, kuma al’adunsa na Hausawa ne, ko da kuwa yana iƙirarin wani asali daban, yana zaune ne a ƙasar Hausa ko a wajen ƙasar Hausa. A yanzu kalmar Hausa ta zama ta harshe ba ta ƙabila ba. Domin kalmar ƙabila, kamar yadda Zarruk da wasunsa (2009) suka bayyana na nufin:

“… al’umma mai asali ɗaya, da yare ɗaya, da ƙirar jiki kusan iri ɗaya, da al’adu iri ɗaya, da falsafa ko ra’ayin zaman duniya iri ɗaya. Bayan haka cikin al’ummar kowa zai riƙa alfaharin shi ɗan ƙabilar ne.”

Ƙasar Hausa ta asali tana yankin Afirka ta Yamma a farfajiyar da ke a Arewacin Nijeriya da kuma Kudancin Jamhuriyar Nijer. Daga Gabas ta yi iyaka da yankin Mangawa da Badawa a gabas kaɗan da garin Haɗejiya ta Jihar Jigawa, daga Yamma ta yi iyaka da ƙasar Zabarmawa daidai doron Kogin Kwara, daga Arewa ta yi iyaka da ƙasar Agadas wato yankin Buzaye (Auzinawa) a Kudancin ƙasar Nijer.

Sannan daga Kudu ta yi iyaka da ƙasar Gwari da wasu ƙananan ƙabilu da ke Kudancin ƙasar Zazzau (Zariya) a jihar Kaduna. Manyan garuruwan ƙasar Hausa a yanzu sun haɗa da Kano da Katsina da Daura da Sakkwato da Kebbi da Zazzau (Zariya) da Gusau da Haɗejiya da Bauci da Azare (ƙasar Guddiri) a arewacin Nijeriya, da kuma Damagaran da Maraɗi da Filinge da Dogon Dutse da Ƙonni a jamhuriyar Nijer.

A taƙaice ƙasar Hausa ta asali, daula ce da ta wanzu a tsakanin daular Borno daga gabas da kuma daular Songhai daga yamma, ko da yake tarihi ya fi ganin yankin a matsayin daular birane, inda kowane sarki yake da ikon cin gashin kansa, wato babu wani shugabanci da ya haɗe yankin a matsayin dunƙulalliyar daula.

Domin karanta mutuwa da rabon gadon Bahaushe danna nan

Edita; Rumasa’u M. Kallamu

labarin da ya wuceAsalin Hausawa
Labarin na GabaYaron Da Ke Ƙin Shan Nono