Ga ta nan, ga ta nanku.
Gizo ne yana yawonsa sai ya tarar da tarin kashi a wani wuri. Bai tsaya ba, ya tsallake ya yi tafiyarsa. Jim kaɗan sai Kura ta bi ta wurin, ita ma ta ga kashin, sai ta kama da ci, kuma ta ji kashin yana da daɗi, sai ta ce: “Lallai duk wanda ya yi kashin nan, namansa zai zama mai daɗin gaske.”
Nan fa ta yanke shawara a kan sai ta gano wanda ya yi kashin. Saboda haka ta hau wani kututture ta shiga jira. Ta daɗe amma ba ta ga kowa ba. Haka ta haƙura; a cikin fushi ta kama hanyar barin wurin. Tana cikin tafiya sai ta ga wani tarin kashin a ƙarƙashin wata bishiya.
Wannan kashi ya tayar mata da kwaɗayi; nan take dai ta cinye shi sarai. Ta yi gaba, sai kuma ga wani kashin. Shi ma ta cinye shi duka. Haka dai ta dinga tarar da kashi tsibi-tsibi tana cinyewa, ba ta rage ko kaɗan ba. Amma har yanzu tana mamakin wanda yake yin sa, saboda haka sai ta sake hawa wani kututture mai tudu tana jira.
Nan ma ba ta ga kowa ba. Ganin haka, sai ta sake dabara, ta tona rami ta shiga fako. Nan ma ba ta ga komai ba. Daga nan sai ta buɗe bakinta, wai komai kashin ya zo ya shiga ciki ta cinye shi. Ba ta jima da bakinta a buɗe ba, sai Gizo ya je ya yi kashi, kashin kuma ya faɗa bakinta.
Ta ji kashin Gizo da daɗi ta ce: “Ashe da man Gizo ne ke yin wannan kashi. Ko ina yakan sami naman da yakan ci ya sa kashinsa ya yi daɗi haka?” Kura dai ta ga gara ta ci gaba da fakon Gizo, sai ta sake hawa sama, ta shiga jiran komawarsa. Shiru, shiru. Gizo bai je ba sai washegari.
Ya sake zuba kashi; yana gama yi sai Kura ta sauka ta yi kansa. Ta kama shi ta riƙe gam-gam; sai ta tambaye shi inda yake samun naman da yake ci. Da fari Gizo ya ce ba zai gaya wa Kura ba don yana tsoron kada a kashe shi idan ya faɗa. Kura ta ce: “Ko ka gaya mini ko kuma in kashe ka.”
Saboda tsoro, sai Gizo ya ce: “To, za mu yi alƙawari a yau kawai. Wato zan gaya miki.” Kura ta amince; suka kama hanya Gizo ya kai ta inda yake samun naman. Da zuwansu wurin sai ya ce: “Buɗe, buɗe, buɗe.” Sai wata ƙofa ta buɗe, suka shiga. A ciki sai ga gwafanni da sanduna a kafe an rataye nama ba iyaka a jikinsu.
Da shigarsu sai Gizo ya ce: “Rufe, rufe, rufe.” Nan take ƙofa ta rufe. Da yake masu tsaron ƙofar sun saba ganin Gizo, ba su hana su ba, kuma ba su nemi sanin abin da ya kawo su ba. Gizo ya kwaso nama da yawa ya ba Kura, ta ci, ta yi guzurin wani mai yawa. Daga nan suka fita, suka kama hanyar gida.
Da dawowarsu gida Kura ta shiga tunanin komawa wurin naman nan ita kaɗai. Bayan kamar mako guda sai ta sami labarin Sarki ya tafi rangadi. Sai ta sami ’yar rakiya daga cikin danginta bisa cewa za su je ziyara ne. Suka kama hanya har suka isa inda suka je cin nama tare da Gizo.
Ta yi irin maganar da ta ji Gizo ya yi a wancan lokaci: “Buɗe, buɗe, buɗe.” Sai ƙofa ta buɗe. Suka shiga, suka ci nama har suka ƙoshi, suka lafci wanda za su tafi da shi
gida, sun ga banza ta faɗi. Ba da dadewa ba Sarki ya dawo daga rangadi. Ya tarar
naman da ya yi tanadi ya ragu ƙwarai.
Ya tambayi masu tsaro, amma suka kasa yin bayani mai gamsarwa. Sarki ya sa aka tara mutanen garin duka. Ya gaya musu ya yi alƙawari duk wanda ya gaya masa wanda ya sace masa nama zai aura masa ’yarsa. Gizo ya san masu gadi kan iya tona masa asiri, sai yace ya san wanda ya yi ɓarnar.
Fadawa suka ce ya faɗa. Nan da nan ya nemi izini, aka ba shi domin ya je ya zo da wanda ya yi wannan ta’adi. Bai zame ko’ina ba sai a ƙofar ramin Kura. Da ya tambaya aka ce ta yi tafiya, sai ya ce: “Kash, ashe ba za ta sami irin naman da Sarki yake ba jama’ar da ya tara a fada ba kenan.
Idan ta dawo a gaya mata ta je fada Sarki zai yi rabon nama mai yawa.” Da jin haka sai Kura ta fito daga inda ta ɓuya ta ce: “Gani. Ba inda na je. Mu tafi in sami rabona.” Suka fita. Ba su tsaya ba sai a fada. Da isarsu ’yan tsaron nama suka ce: “Ba shakka, Kura ce ta cinye naman Sarki.”
Kafin ta farga, tuni an hau ta da bugu. Da aka kai ta ƙarshe, sai aka farke cikinta. Hanji da tumbi da uwar kashi da tubura da huhu da zuciya da kashi, duk suka zuba. Kura dai a taƙaice nan ta mutu. Sarki kuwa dama mai jan girmansa ne. Nan take ya cika alƙawari, watau Gizo ya zama surukinsa. Suka yi zamansu lafiya. Kurunƙus.
Abubuwan Da Labarin Yake Koyarwa
- Kwaɗayi mabuɗin wahala.
- Iya gani iya ƙyalewa.
- Alƙawari kaya ne.
- Mai rabon shan bugu, ba ya jin kwaɓa.
- Kowa ya daka rawar wani, ya rasa turmin daka tasa.
Wannan tatsuniya an ciro ta ne daga littafin TASKAR TATSUNIYOYI wanda Bukar Usman OON ya wallafa.
Karanta Tatsuniyar Tasalla Mai Kifi
Edita@rumasau-kallamu










