Tatsuniyar Maye Da ’Ya’yansa

0
7

Ga ta nan, ga ta nanku.

Akwai wani mutum a wani gari da ke gabas da garin nan. Yana da mace ɗaya da ’ya’ya biyu mata. Da suka isa aure Allah ya ba su masoya, aka yi musu aure aka kai kowacce ɗakinta. Bayan ’yan shekaru kowacce ta haifi ’ya’ya. Ana nan, sai aka aika musu uwarsu ta rasu; sai dai su ba su san cewa ubansu maye ne ba, kuma shi ne ma ya cinye uwar tasu.

Shi ke nan yaran nan suka je gidan ubansu saboda zaman makoki, amma sai suka tarar uban nasu ya cinye gawar uwar tasu, domin yunwar maita ta kama shi, kuma babu wanda zai ci sai gawar. Da ya ji muryar ’ya’yansa, sai ya kulle kansa a cikin ɗaki don kada su gani, su gane.

Duk sanda suka kai masa abinci, sai yace su ajiye a ƙofar ɗaki. Bayan sun yi kwana biyu a gidan, sai a dare na uku ya tara su, ya fara zaro harshe yana haɗiyar yawu. Sai suka gane cewa shi ya cinye babarsu, kuma yana so su ma ya cinye su. Da man sunan ɗaya Nkwa, ɗaya kuma Sektiraye.

Sai ya fara kiran su yana cewa: “Nkwa da Sektiraye duk da ’ya’yanku, Ku jira ni ina zuwa, Zan cinye ku, Da man ina jin yunwa.” Da suka ji haka sai suka kama ’ya’yansu suka ɓuya, kuma suka ajiye kabewa a kan gado suka lulluɓe ta. Da dare ya yi tsaka, sai
kawai ya tashi ya kama cin kabewar da ke kan gado.

Da ya gane ba nama ba ne, sai haushi ya kama shi. Can kuma sai ɗaya daga cikin jikokinsa ya fara kuka a inda suka ɓuya. Da ya gane inda suka ɓuya, sai ya yi kukan kura ya auka musu, amma bai cafki ko ɗaya ba. Sai ’ya’yan nasa da jikokin suka fito da gudu, suka kama hanyar dajin da ke kusa da garin, shi kumayana bin su.

Suna cikin gudu a dawan nan sai ya kama ɓarin jikinsa ya cinye, har dai ya zama saura ƙashi a jikinsa kawai. A hakan yake bin su da gudu yana cewa: “Dun kwalak, ka dun kuci kal.” Da suka isa wani guri a cikin dajin, sai suka tarar wuta tana cin ciyawa, sai suka keta ta cikin wutar a guje.

Saboda yawan wutar, har ta kama cin hanya. Da uban nasu wanda ya zama ƙwarangwal
ya isa wurin wutar nan, sai ya faɗa cikinta, wuta kuwa ta cinye ƙasusuwansa, ya ƙone ƙurmus. ’Ya’yan nan nasa da jikokinsa sun sami tsira. Da gari ya waye, sai wasu mata masu neman tokar miya suka tarar da tokar wannan maye a kan hanyar, ba su san ta mutum ba ce.

Sai ɗaya daga cikinsu ta ce su deɓi tokar miya. Sai suka ɗiba, suka koma gida. Sai ɗaya daga cikin matan ta haɗa tokar za ta yi miya da ita. Bayan ta ɗora tukunyar miya da tokar a ciki a kan wuta, sai ta ji miyar tana cewa: “Ki juya ni a hankali, domin wuta ta ƙona ni da yawa.” Da ta ji haka ba ta ce uffan ba, kuma ba ta daina girki ba, har sai da ta gama.

Da ta gama, ta zuba, ta kai wa mijinta abincinsa a akushinsa. Data je ajiye akushin sai ta ji an ce: “Idan za ki ajiye ni, ki ajiye ni a hankali don wuta ta ƙona ni da yawa?” Da mijin ya ji, sai ya kira matarsa ya ce mata: “Na ji kamar miyar tana magana.” Sai ta dubi mijin tana murmushi ta ce: “Kai anya, ba kunnenka ba ne kuwa?”

Sai mijin ya sa hannu zai buɗe akushi ya fara cin tuwo da miya, sai miyar ta ce: “Idan za ka deɓe ni, ka deɓe ni a hankali, don wuta ta ƙona ni sosai.” Da mijin ya ji haka, sai ya dubi matar ya ce: “To ashe ke mayya ce ban sani ba.” Sai matar ta ce: “A a ai a cikin jeji na samo tokar miya.”

Sai mijin ya ɗauki miyar ya kwara mata a ƙirji. Nan take ƙirjinta ya fitar da haƙora gatso-gatso, abin gwanin ban tsoro. Da mijin ya ga haka, sai ya kore ta, sai ta shiga daji, ta koma can da zama. Duk wanda ya je dajin da take zai tarar da ita tana yawo, tana cin fari da kwaɗi. Kurunƙus.

Abubuwan Da Labarin Yake Koyarwa

  • Kwaɗayi mabuɗin wahala.
  • Tsautsayi ba a sa maka rana.
  • Mai mugun hali tun a duniya sai ya ɗanɗana kuɗarsa.
  • Aikin da ba a yi shi da kyakkyawar niyya ba ƙarshensa nadama.

Wannan tatsuniya an ciro ta ne daga littafin TASKAR TATSUNIYOYI wanda Bukar Usman OON ya wallafa.

Karanta Tatsuniyar Binta ’Yar Sarki

Edita@rumasau-kallamu

labarin da ya wuceTatsuniyar Binta ’Yar Sarki
Labarin na GabaTatsuniyar Awa Da Dawi
wikiHausa
wikiHausa kundin ilimi (insakulofidiya) ce da ke ilimantar da jama'a yara da manya da maza da mata wajen samun ilimi a saukake, cikin harshen Hausa.