Tatsuniyar Gwaidayara

0
3

Ga ta nan, ga ta nanku.

A can bakin Rafin Kada akwai wani mutum da yake zaune tare da matansa su huɗu; sai dukkaninsu suka sami ciki a lokaci ɗaya. Da watansu ya kama suka haifi ’ya’ya duka mata. Bayan mako guda na al’ada, ya raɗa wa uku daga cikin yaran nan sunaye. Ɗaya sunanta Halima, ɗaya Jummai, ta ukun kuma A’isha.

Amma sai ya ƙi rada wa ’yar matarsa ɗaya suna. Sai mahaifiyar tata ta tambaye shi: “Me ya sa ni ba za ka sa wa ’yata suna ba?” Bai dai amsa ba, amma ya ce zai raɗa mata suna. Haka dai ta riƙa tuna masa, har wata rana a cikin gatse ya ce: “Ki je sunanta Gwaidayara.”

Kwanci tashi, yaran nan huɗu suka data, suka isa aure, shi kuma ya tsaya ya tabbatar Halima da Jummai da A’isha kowacce ta sami mijin aure, watau ban da Gwaidayara. Kuma ya yi haka ne saboda bai cika son uwarta ba. Da uwar ta ga haka, sai ta durƙusa ta ce da shi: “Shin Mai gida, me ya sa ba za ka yi wa’yata aure kamar yadda ka yi wa ’yan’uwanta ba?”

Sai ya dube ta ya ce: “Ki gaya mata ta riƙa bi na daji.” Uwar Gwaidayara kuwa ba ta jinkirta wajen sanar da ’yarta abin da mai gida ya ce ta gaya mata ba. Haka kuwa aka yi. Duk sanda uban zai je daji sai ta bi shi. Kullum haka, abu kamar da wasa ya ɗore. Wata rana da suka je tsakiyar daji sai wani baƙin maciji ya wuce sululu ta gabansu.

Sai uban ya ce da Gwaidayara: “Ga mijinki nan, ki bi shi duk inda ya dosa.” To saboda biyayya irin wadda ta ga uwarta na yi wa mahaifinta, sai ta ce da shi: “To, Baba, na gode.” Daga nan ta dinga bin maciji, ba tare da jin tsoro ko shakka ba. To, ashe shi ba maciji ba ne, mutum ne kuma ɗan sarki.

Da ya ga yarinyar na bin sa kamar yadda ubanta ya ce ta yi, kuma ya lura uban yarinyar ya kama gabansa, sai ya rikiɗa ya koma mutum; sai ya tambayi Gwaidayara: “Baiwar Allah me kika zo yi a nan?” Ganin abin da ya faru, sai tsoro da ɗimaucewa suka sa ta kasa yi masa wani bayani.

Ya dai ji ubanta ya ce: “Bi macijin nan shi ne mijinki.” Da ƊanSarkin nan ya lura da ɗimautar da Gwaidayara ke ciki, sai ya ce da ita: “Kada ki dami kanki, ki ma daina jin tsoro; mu je garinmu a ɗaura mana aure, ai mahaifinki ya ba ni ke.” Sai shi da ita suka kama hanyar garin mahaifinsa; har suka isa, ta ga ana ta faɗuwa kasa ana gaishe shi.

Da ya shiga gida, ya kai ta ta huta, sai ya ce su je wurin mahaifinsa. Suka je suka gai da Sarki, sai ya tambayi dansa: “Yarima Babba, lafiya na gan ka da wata yarinya; wace ce?” Sai ya ce da shi: “Ka daɗe, mai duniya, wannan yarinya da na zo da ita, ina neman izininka ne in aure ta.”

A nan take kuwa Sarki ya amince. Bayan kwana biyu aka ɗaura musu aure, Sarki ya kawo dukiya mai yawa ya ba ɗansa da surukarsa. Ɗan Sarkin nan kuma ya ɗebi dukiyar ya je daji daidai inda surukinsa ya bar ’yarsa ya ƙanƙara gida suka tare shi da amaryarsa. Suna nan, wata rana sai uban Gwaidayara ya je gona, sai ya tarar da wasu mata na jan ruwa a rijiyar da ke kofar kataferen gidan nan.

Waɗannan mata kuyangin Gwaidayara matar Yarima Babba ne. Ya roƙe su ruwan sha, amma suka hana shi, tare da bayanin cewa: “Ko za mu ba ka sai mun cika duk randunan Gwaidayara.” Da ma Gwaidayara ta saba takan leƙa ƙofar gidan ta taga. Da ta leƙa sai ta hango mahaifinta yana magana da ’yan aikinta.

Sai ta kira ɗaya ta tambaye ta: “Me mutumin nan yake cewa ne?” Sai ’yar aikin ta ce: “Ya ce mu ba shi ruwan sha ne, muka ce sai mun gama cika randunanki.” Sai Gwaidayara ta ce: “Ku ba shi ruwan ya sha. Idan ya sha kuma ku ce ya shigo.” Bayan mahaifin Gwaidayara ya sha ruwa, sai ya ji a cikin ladabi ɗaya daga cikin kuyangin nan ta ce: “Gwaidayara matar Ɗan Sarki ta ce ka shiga gidan nan.”

Sai ko ya shiga ya zauna a zaure, yana jira ya ga abin da zai faru. Kafin ta aika a gaya wa mai gidanta cewa mahaifinta ya zo, sai ta ji motsin shigowarsa gida. Bai tsaya a zaure ba, ko da yake ya ga baƙon mutum, amma bai san ko wanene ba.Sai Gwaidayara ta tunkari mijinta bayan fadawa sun tsaya a soro ta ce: “Yaya ka wuce mahaifina ba ka gai da shi ba?”

Sai ya ce: “Yana ina? Ban gan shi ba.” A cikin karairaya irin ta matan da suka iya kissa ta ce da shi: “Ai shi ne a zaure, ai gara ku gaisa.” Sai mijin ya je suka gaisa, aka ba shi masauki irin na alfarma, ya yi wanka da ruwan ɗumi, ga tufafi sababbi an kawo masa; ya zaɓa, ya saka.

Bayan mahaifin Gwaidayara ya ƙara hutawa, can da la’asar surukin da matarsa suka kawo kyankyandi gomiya ɗaya da biyar, cike da tufafi da kuɗi, suka ba shi. Wasu kayan nasa ne, wasu kuma tsarabar da zai kai wa matansa ce. Ya yi mamaki da godiya; bayi da fadawa suka ɗauki kayan, aka raka shi har gida.

Da ya kai kayan tsarabar ya yi wa matan gidan bayani, sai suka ce: “Wannan tsarabar ’ya’yanmu ne suka aiko; wa zai ba Gwaidayara arziki haka?” Haka dai suka rabe kayan suka hana mahaifiyarta. Bayan ’yan kwanaki sai mahaifin su Gwaidayara ya shirya zai ziyarci sauran ’ya’yansa, wato Jummai da A’isha da Halima.

A gidan Halima ya tarar ita da mijin ba su da abinci idan ban da birrai da ɓeraye saboda tsananin talauci; jikinta ya yi kirci, ba ta da ko sabulun wanka. Hatta tabarmar kwanciya ma ba ta da ita. Bayan ya gama ziyararsu zai tafi, sai ta ƙunshe masa kan biri da jelar ɓeraye biyar a tsumma ya kai wa mahaifiyarta tsaraba.

Da uban ya je gidan Jummai, sai ya tarar ba su da wani abinci sai ganyen yaɗiya da gautan daji da tsamiyar ƙasa. Babu rumbu balle masussuka a gidansu. Bayan ya gama ziyararta, ita da mijin suka roƙo gaskami daga makwabta, ta sa a wani kata don ya kai wa mahaifiyarta tsaraba.

A’isha ce mijinta yake da ɗan ƙarfi, domin ɗan abin da yake da shi, har dusa yakan samo ta tuƙa musu tuwo. Wani lokacin kuma sukan ci zogale da wake, kuma tana da zane sakakke da turmi da tabaryar yin aikatau. Da zai tafi gida ta ɗebo dusa mai yawa ta ba shi ya kai wa mahaifiyarta tsaraba.

Da mijin ya koma gida, sai ya ce da matan nasa: “Ina so duk yaran nan kowacce ta zo da mai gidanta ranar Laraba mai zuwa.” Aka aika musu, kowacce ta ci ado, daidai arzilinta, ta taho tare da mijinta. Gwaidayara ce ta fara zuwa tun da sanyin safiya, ta shiga ɗakin mahaifiyarta da ke kusa da ƙofar gida, sauran matan gidan ba su san ma ta iso ba, tare da tarin kyankyandi cike da dukiya mai yawa.

Sauran kowacce ta zo dukkaninsu suna fama da rama da gajiya, ga shi ba su da suturar kirki. Kowacce ta shiga ɗakin mahaifiyarta wai suna jiran ganin mugun halin da Gwaidayara da mijinta suke ciki. Can kuma sai ga mazansu su ma sun iso. Mijin Halima ya sha lagen wani luru da ya huje; mai gidan Jummai kuma ba komai a jikinsa sai bante.

Mijin A’isha ne mai dama-dama, domin ya sa ’yar shara wadda ya aro a wurin abokinsa. Mijin Gwaidayara kuma ya tunkaro. Tun yana nesa ƙamshin turarensa ya cika gari, fadawa suna gaba, masu algaita na busa, makaɗa na ta kiɗa; sai kirari ake yi masa ana cewa: “Lafiya Yarima Babba Ɗan Sarki,angon Gwaidayara.”

Bayan kowacce ta fito tare da mijinta, sai iyayensu mata suka kama kuka da nadamar halin da Jummai da Halima da A’isha da ake so suka shiga a gidajen aurensu. Nan take suka ba mahaifiyar Gwaidayara haƙuri bisa matsa mata lamba da wulaƙancin da suka dinga yi mata a baya. Ita kuma ta ce ta yafe musu.

Gwaidayara ta kawo tufafi da kayan abinci da abin zaman gari mai yawa ta ba ’yan’uwanta kowacce da mijinta, ta ƙara wa kishiyoyin uwar kayan tsaraba waɗanda ba su taɓa jin labarin irinsu ba, suka yi godiya. Daga nan kuma uban ya ce ba sauran a wulaƙanta kowa a gidansa. Kurunkus.

Abubuwan Da Labarin Yake Koyarwa

  • Illar nuna bambanci da tsana ga ɗaya daga cikin ’ya’yan da mutum ya haifa.
  • Haƙuri da biyayya ga iyaye da jure wa ƙuntatawarsu abu ne mai kawo arziki da nasara a rayuwa.
  • Nuna wa yaro gatanci da shagwaɓa shi wata hanya ce ta lalacewa da talauci da shiga halin da-na-sani.
  • Allah ne kaɗai yake arzutawa kuma yake talauta wanda ya so.
  • Allah gatan kowa.
  • Mugun nufi ba ya kashe ɗan kurciya.

Wannan tatsuniya an ciro ta ne daga littafin TASKAR TATSUNIYOYI wanda Bukar Usman OON ya wallafa.

Danna nan don karanta Tatsuniyar ’Yan Mata Biyu

Edita@rumasau-kallamu

labarin da ya wuceTatsuniyar ’Yan Mata Biyu
wikiHausa
wikiHausa kundin ilimi (insakulofidiya) ce da ke ilimantar da jama'a yara da manya da maza da mata wajen samun ilimi a saukake, cikin harshen Hausa.