Ga ta nan, ga ta nanku.
Akwai wata mata mai ɗa wai shi Janniya. Suna zaune ita da kishiyarta tare da mijinsu cikin lumana. Wannan mata kuma tana da garken shanu. Bijimin da ke cikin shanun kuma yakan yi magana kamar mutum. Ana nan, ana nan, wata rana uwar Janniya da kishiyarta suna zaune suna taɗi, sai ta ce da kishiyar: “Ina jin fa na kusa mutuwa. Idan na mutu ki kula da Janniya.”
Da kishiyar ta ji haka sai ta ce: “Haba! Ai ko ba ki faɗa ba ma zan kula da shi, ai ɗana ne.” Sai uwar Janniya ta ce: “To, na gode da kika yi wannan alwashi.” Bayan kamar kwana huɗu da yin wannan zance, sai uwar Janniya ta ce ga garinku nan! Ita kuwa kishiyar sai ta mallaki shanun da uwar Janniya ta bari.
Suna nan, kullum sai ta zuba wa Janniya magunguna na asiri iri-iri a cikin abincinsa. To amma duk sanda Janniya ya zo cin abincin, sai wannan bijimin sa ya gaya masa, kuma ya hana shi ci. Sai ya rinƙa rera waka yana cewa:
“Janniya Jannati,
Janniya Jannati.
Kishiyar uwa Janniya, Jannati, Janniya,
Ba uwabace Janniya Jannati.
In za ta ba ka tuwo,
Tuwo damagani, Janniya Jannati.
In ta ba ka, Janniya Jannati,
Ka tona rami, Janniya Jannati,
Agindin turkena, Janniya Jannati.
Ka binne tuwon, Janniya Jannati.
Kar ka ci, Janniya.”
Kullum haka, amma duk da rashin cin abinci kamar yadda ya kamata, wannan bai sa Janniya ya rame ba. Yau da gobe sai kishiyar uwar ta gane wannan san ne ke tona mata asiri, sai ta matsa wa mijinta ya amince a yanka san nan mai magana. Shi kuma san duk ya ji abin da aka shirya, sai ya ce da Janniya: “Idan an yanka ni, ka ce a ba ka kai da ƙafafuwana da kayan ciki.
Sai ka binne su. Yin haka zai karya duk wani makaru da za ta yi maka.” Shi ke nan da aka yanka sa, sai Janniya ya roƙi a ba shi duk waɗannan abubuwan. Aka ba shi, shi ko ya je ya binne. Sai kishiyar uwar ta ci gaba da ba shi sammu iri-iri, to amma saboda ya yi abin da san nan ya faɗa, sai duk makarun da take yi ba wanda ya kama shi.
Kullum sai haske yake ƙarawa, ita kuma baƙin ciki na damunta. Wani Falke ya ce, baƙin ciki kan kashe irin waɗannan mutane. Haka ko aka yi. Ta ci gaba da lalacewa, har dai a ƙarshe bakin ciki ya kashe ta. Kurunkus.
Abubuwan Da Labarin Yake Koyarwa
- Duk wanda yace zai canza hukuncin Allah ƙarshensa nadama da halaka.
- Mugun nufi ba ya kashe ɗan kurciya.
Wannan tatsuniya an ciro ta ne daga littafin TASKAR TATSUNIYOYI wanda Bukar Usman OON ya wallafa.
Danna nan don karanta Tatsuniyar Maharbi Da Zaki
Edita@rumasau-kallamu










