Ga ta nan, ga ta nanku.
Akwai wata Marainiya a wani gari. Sanda iyayenta suka rasu ba su bar mata komai ba, sai wani turmi. Turmin kuwa wani shu’umi ne mai ƙwanƙwamai, to amma sauran mutanen gari ba su san haka ba. Sai turmin ya ce da ita: “To, tun da ba ki da uwa, ba ki da uba, ni ne zan tsaya miki a madadinsu.”
Wannan magana ta faranta wa Marainiyar nan rai. Sai ta dafa wa turmi ta ce: “To, na gode. Yanzu watau duk abin da nake so za ka ba ni?” Turmi ya ce da ita: “Ba shakka, zan ba ki duk abin da kika nema.” Yarinya ta ci gaba da zama da turmi.
Suna nan, suna nan, sai wata yarinya ta ji labarin yadda Marainiyar da turmi suka yi, sai ta ce za ta gwada ta ga gaskiyar batun. Sai ta dafa shinkafa, ta je gidan Marainiya da ita ta ce mata: “Kin ce turmin gidanki zai iya ba ki komai ko? To, ya dafa miki shinkafa mu gani in ba ƙarya ba.”
Marainiya na jin wannan, sai ta gaya wa turmi a cikin waƙa:
“Turmi, turmi, tangariya,
Gori ake yi min, Turmi tangariya.”
Turmi ta ce: “Gorin me ne?”
Marainiya ta ce: “Gorin shinkafa, Turmi tangariya,
In da shinkafa, Sai ka ba ni, Ka ba ni shinkafa, Turmi tangariya.”
Kamar abin dabo sai ga shinkafa har ta fi ta baƙuwar yarinyar yawa da kyau. Da baƙuwar yarinya magulmaciya ta ga haka, sai ta ce: “Na ga wannan, amma zan sake gwada turmin nan.” Can daf da lokacin faɗuwar rana, sai ta je gidan Marainiya da zinariya mai yawa a ƙulle a haɓar zanenta, sai ta ce da Marainiya: “Na zo da zinariya, idan Turmin nan ya isa ke ma ya ba ki.”
A nan ma Marainiya ba ta yi shakkar komai ba, ta je ta dafa Turmi, ta rera wannan waƙar neman biyan buƙata: “Turmi, turmi, tangariya, Gori ake yi min, Turmi tangariya.” Turmi ya ce: “Gorin mene ne?” Marainiya ta ce: “Turmi gorin zinariya, Turmi tangariya. Idan da zinariya, Turmi ka ba ni.”
Kafin ta gama rufe baki sai ga zinariya tsibi-tsibi, har da wani tarin zinariya kamar girman ƙwan kaza. A wani tarin kuma kamar girman dutsen murhu. Wuri duk ya haske, algungumar yarinya kuma nan take ta suma saboda mamaki.
Amma da ta farfaɗo maimakon ta saduda, sai ta ce: “Na ga wannan ma bari in kawo saurayina, ke kuma ma Turmi ya ba ki naki mu gani.”Sai ta kawo saurayi har ƙofar gidan. Ita kuma Marainiya ta shiga ta gaya wa Turmi. Sai Turmi ya ce da ita ta rufe idanunta, sannan ta buɗe bayan ta yi ƙirga ɗaya zuwa bakwai.
Da ta yi haka; tana buɗe ido sai ta ga wani tsulelen saurayi kyakkyawan gaske, wanda har magulmaciyar yarinyar da kanta ta ce: “Ban taɓa ganin kyakkyawan saurayi kamar shi ba.” Sai baƙin ciki da kishin abin da Turmi ke yi wa Marainiya suka sa magulmaciyar yarinyar ta kashe kanta.
Da labari ya bazu a gari, sai aka taru ana kallon gawarta, ana mamakin abin da ya kai ta ga faɗawa wannan asara. Kurunkus.
Abubuwan DaLabarin Yake Koyarwa
- Ɗa nagari ba ya rama mugunta da sharri sai da alheri.
- Nuna ƙyashi da baƙin ciki a kan baiwar da Allah ya yi wa wani mutum halaka ce da ta sa a yi mummunan ƙarshe.
- In Allah ya rufa wa bawa asiri, ba mai tona masa.
Wannan tatsuniya an ciro ta ne daga littafin TASKAR TATSUNIYOYI wanda Bukar Usman OON ya wallafa.
Karanta Tatsuniyar Janniya
Edita@rumasau-kallamu










