Taƙaitaccen Tarihin Samuwar Waƙoƙin Baka a Ƙasar Hausa

0
494

Waƙoƙi : Masana sun yi ƙoƙarin bayyana asalin samuwar waƙoƙi baka a ƙasar Hausa.

Daga ciki akwai ra’ayin Satatima (1999:30) inda ya bayyana cewa: “Al’ummar ƙasar Hausa sun sami basirar kiɗa..

Harda waƙa daga tsofaffin daulolin Ghana da Mali da Songhai wanda wasu sassa na ƙasar Hausa suka kasance ƙarƙashin mulkinsu

kafin ƙarni na sha tara.

Masu wannan ra’ayi har sun kai ga cewa daga waɗannan tsofaffin dauloli Hausawa suka samu kayan kiɗa irinsu kakaki, wanda aka samu daga Songhai cikin ƙarni na sha shida. Algaita kuwa an samo ta ne daga Songhai da Mali”.

A wurin Gusau (2003:5-6) kuwa, ya kawo hasashe guda uku waɗanda yake ganin su ne asalin waƙar baka.

Waɗannan hasashe kuwa su ne:

Ra’ayi na farko, suna ganin ana jin ɗan’adam ya ƙagi waƙa ne tun lokacin da ya fara neman abinci ta hanyar farauta, daga nan ya gano noma sai waƙa ta ƙara haɓaka.

Ra’ayi na biyu kuwa, an nuna cewa, ana ganin waƙa ta samo asali ne daga wani maroƙi ‘Sasana’.

Domin haka, a wannan ra’ayi ana jin makaɗan Hausa jikokin wannan mutum ne.

Domin karanta cikakken bayani a kan Ma’anar Kiɗa da Makaɗi danna nan

labarin da ya wuceAbin da Bincike Ya Gano Game Da Matsalolin Aure A Ƙasar Hausa
Labarin na GabaMaimaituwar Jinin Haila A Wata Ɗaya