Tatsuniyar Makauniya Da Ɗanta

0
3

Ga ta nan, ga ta nanku.

A wani ɗan ƙauye da ke yamma da Dajin Kurege, akwai wani manomi da matarsa makauniya. Suna cikin zama irin na rufin asiri, sai Allah ya yi masa cikawa. A lokacin kuwa tana goyon jariri mai suna Zama. Uwar tasa kuwa ta sha wuya wajen renonsa. Kullum sai ta je ta yo bara kafin ta ciyar da kanta da ɗanta.

Mijinta kuma bai bar dukiya ba sai shanu biyu kawai da Zama ya gada. Ita kuma mace ce mai tsinkaye da riƙon amana, sai ta kai shanun nan wani garke, a rugar wasu makiyaya da ke kusa da ƙauyensu. Ta yi haka ne da nufin a kiwata su, idan yaron ya girma, kuma shanun sun yaɗu, ta nuna masa abin da ubansa ya bar masa.

Kuma duk abin da ɗanta yake so takan je ta barato masa. Sannu a hankali, yaro ya girma ya isa aure. Wata rana bayan sun ci abincin dare, sai uwar ta kira shi tace: “To, Zama, da ma ina jira ne idan ka yi hankali sosai in danƙa maka abin da ka gada daga mahaifinka. Amma na kai su garke ne, a rugar wasu makiyaya.”

Da ya ji lafazin mahaifiyarsa, sai ya tambaye ta: “Menene? Wane irin abu ne?” Ta ce: “Shanu biyu ne ya bar maka, amma ban sani ba ko yanzu sun ƙaru?” Sai ta kama hannunsa ta ce: “Mu je inda aka kai shanun, mu jiyo labari.” Ta yi masa kwatancen hanyar da za su bi; suka kama hanya, har ya kai su.

Mai garke ya yi musu maraba suka gaisa kamar yadda ya kamata, sai makauniya ta tuna masa shanun da ta kawo masa kiwo tun shekarun baya da suka wuce. Sai mai garke ya ce: “Haka aka yi kuwa. Ai yanzu shanu sun hayayyafa, har ma sun kai ashirin.” Da ta ji haka sai ta yi masa godiya, ta ce da shi: “To, ga magajinsu ya kawo ƙarfi, buƙatu sun taso, shi yasa muka zo mu kora su.”

Sai mai garke ya ware musu shanunsu; suka kama hanyar gida, Zama yana kora su har suka je gida. Bayan sun ɗan huta da kwana biyu, sai uwar tace da Zama: “Ya kamata yanzu kam ka yi aure domin ina so in sami jikan da zan rinƙa wasa da shi.” Sai ya ce da ita: “To, amma fa ni ba zan yi aure a ƙauyen nan ba sai dai daga birni.”

A kwana a tashi, wata rana sai Zama ya shiga birni, ya je kasuwa; sai ya tarar an sa wata kyakkyawar yarinya a gaba, makaɗa na cashewa, ana yi mata kirari, da waƙe- waƙe. Sai ya tambayi wani ɗan kallo da cewa: “Me yasa aka kewaye wannan yarinya mai kyau kamar aljana, ana yi mata kiɗa da waƙa?” Sai ya ce da shi: “Saboda kyauta ne uwarta tace duk mai son ta, sai ya ba ta duk dukiyar da ya mallaka, kafin ya aure ta.

Duk masu dukiyar da ke garin nan kuma sun kasa.” Da ya ji haka sai ya yi tsaki, ya ce: “Ni zan aure ta.” Sai ya matsa kusa, ya sa aka yi he!, ya ce: “A gayawa uwar yarinyar cewa ni zan aure ta, kuma zan ba da duk dukiyar da na mallaka.” Wani daga cikin danginta ya ce: “To me ka mallaka?” Zama ya ce: “Ina da riƙaƙƙun shanu ashirin.”

Sai dangin ya ce: “To, ka je ka kawo su za a ba ka ita.” Da Zama ya ji haka, sai kurum a cikin ɗoki ya koma gida ya gaya wa mahaifiyarsa cewa ya sami wadda zai aura. Uwar ta ce: “Wane sharaɗi iyayenta suka sa maka?” Sai ya ce: “Sun ce sai na ba su duk dukiyata kafin su ba ni ita.”

Uwar daga farko ta yi murna, amma da ta yi tunani kaɗan sai ta ce: “Kai ɗan nan, wannan fa shi ne iyakar abinda ka mallaka, babu hikima a ce ka ba su ita gaba ɗaya.” Wannan magana dai ba ta shigi yaron ba. Sai kawai yace shi fa sai ya auri wannan yarinyar. Sai uwar ta ce: “Shi kenan, yi abin da kake so.”

Yaro ya tashi ya kwance shanu ya kora su gidan iyayen yarinyar da zai aura. Suka karɓa suka kuma ba shi yarinyar, aka ɗaura aure ya ɗauki matarsa ya kai ta gidansu, ya je kuma ya sanar da mahaifiyarsa. Ita kuma ta ce da shi: “Ai ya kamata ka kai ni in yi mata barka da zuwa.” Bai yi wata-wata ba ko sai ya kama sandarta ya kai ta har ɗakin amaryar.

Amma da ta ga mahaifiyar Zama makauniya ce, sai ta ƙi yi mata magana, ta nuna cewa ai ba ta yi wa makafi magana. Uwar kuma ba ta nuna damuwa a kan halayyar surukarta ba, saboda haƙurin da Allah ya ba ta. Ana nan, bayan ’yan kwanaki sai amarya ta ce da Zama: “Ni fa na gaji, ba zan iya ci gaba da girki a gidan nan ba.”Sai ya ce: “To, yaya kike so a yi?”

Ta ce da shi: “Mai dafa abinci za ka nemo mini.” Da ya ga matarsa ta kafe a kan haka sai ya gayawa mahaifiyarsa. Ita kuma ta ce da shi: “Ba komai, ni zan ci gaba da dafawa; ai da ma tun kafin ta zo, ni nake dafawa.”Haka ta ci gaba da yi musu girki, surukarta kuwa ta ci gaba da zaman ƙwambo.

Ana nan, sai wata rana matar Zama ta tambayi mijin inda ya samo shanun da ya kai gidansu ya aure ta. Sai ya kwashe labarin yadda ya ci gadon mahaifinsa, ya gaya
mata. Da ta ji haka sai ta ce: “Ai ba ka da wayo, mahaifiyarka ta cuce ka domin ta ɓoye sauran shanun. Ka je ka bincike ta da kyau, za ta gaya maka inda sauran suke.”

Nan da nan ya tashi ya je ya sami mahaifiyarsa, ya fara yi mata rashin ladabi da faɗa, wai sai ta fito masa da sauran shanunsa. Ita kuma ta ce da shi: “Haba ɗana, ban ɓoye maka komai ba.” Haka dai Zama ya yi ta yi wa mahaifiyarsa rashin ladabi har tsawon wasu ’yan kwanaki.

Da matar Zama ta ga bai yi wa mahaifiyarsa wulaƙanci kamar yadda take so ba, sai ta ce da shi: “Ni fa zan koma gidanmu; domin na gaji da zama da makauniya a gidan nan. Yanzu lallai sai ka san inda za ka kai ta, ko kuma ni in tafi gidanmu.” Sai ya ce: “Kada ki damu. Yanzu faɗi yadda kike so a yi da ita.”

Jin haka fa ya sa ta yi murmushi ta ce: “Ina son ka kai ta cikin jeji inda kuraye suke shan ruwa, sai ka ce ta jira ka, kai kuma ka gudo gida. Washegari sai ka je ka kwaso ƙasusuwanta bayan kuraye sun cinye ta. Daga nan sai ka gaya wa mutane cewa ta yi ɓatan kai ne a jeji, kuraye suka cinye ta.” Ya ce: “Idan na yi haka za ki haƙura da komawa gidanku; za ki zauna da ni?”

Sai matar ta kashe murya, ta dube shi, ta ce: “Ƙwarai kuwa. Idan ka yi haka, ba inda za ni.” Zama ya je ya ce da mahaifiyarsa: “Yanzu na yi wani tunani ina son ki zo mu je in kai ki inda za ki sami maganin makantarki.” Sai ta ce: “To.” Nan da nan ta shirya a cikin murna, suka kama hanyar daji, har suka kai tsakiya inda kuraye kan taru, ya ajiye ta a gindin wata bishiya, ya ce da ita:

“Zauna nan, ni kuma zan je neman wani itace da za a haɗa maganin. Idan ban dawo ba, kada ki motsa daga nan.” Ta ce da shi: “To. Na gode Zama, ka kyauta da ka kawo ni
gidan masu magani.” Shi ko bai ma damu da godiyar da take yi masa ba, sai kawai ya kama hanya ya koma gida ya baro ta a wannan dajin.

Ita kuwa ta zauna tana jiransa har dare ya yi. Idan ta ji motsi sai ta ce: “Zama ne? Ka dawo?” Sai ta ji kukan kura a bayanta, amma ba ta razana ba. Wannan dajin kuma bayan kuraye da sauran namun da ke dajin, akwai aljanu a wurin da yawa. Aljanun ne ma suka zagaye ta, suna mamakin abin da ya sa ta zo wuri mai hatsari haka.

Can sai ɗaya daga cikinsu ya rikiɗa ya je ya ce: “Ke matar nan me ya kawo ki nan?” Sai ta ce: “Ɗana ne Zama ya kawo ni, don neman maganin makantar nan tawa.” Sai aljanin nan ya ce: “A a, nan fa mutane ba sa zuwa, domin tsakar daji ne, amma zan taimake ki yadda za ki tafi gida.” Sai ta ce: “A a ɗana ya ce in jira shi a nan; idan na tafi zai yi mini faɗa.

Gara in jira shi ai zai zo ya same ni.” Da tausayi ya kama aljanin nan, sai ya gaya mata cewa za su warkar mata da makantar. Kamar da wasa, da suka yi wani siddabaru irin nasu, sai kawai ta ga ta fara gani. Buɗe idonta bai sa ta yi niyyar tafiya ba, har gari ya waye ta farka daga barcin da ta yi, ta shiga jiran ɗanta.

Kafin ya zo sai ta ga shanu masu yawa, garke-garke, ta tambayi aljanin nan da ya rikiɗa ya zama mutum, ko shanun nan na wanene? Sai ya ce da ita, ai nata ne duka, sun ba ta kyauta. Makauniyar nan tana zaune can sai ga Zama ya iso. Ya kuma zo ne don ya kwashe ƙasusuwan mahaifiyarsa saboda ya tabbatar da kuraye sun cinye ta a cikin dare.

Maimakon haka, sai kawai ya ji ta kira shi daga nesa, saboda jikinta ya ba ta cewa ɗanta ne, ko da yake dai ba ta taɓa ganin sa ba sai wannan rana. Har ya juya zai gudu sai
ta ce: “A a, kada ka gudu mana. Ni ce mahaifiyarka.” Da ya isa kusa da ita, sai ta kwashe duk labarin abinda ya faru tsakaninta da mutumin da ya taimake ta, ga idanu sun samu, kuma ga shanu.

Zama ya kora shanu, shi da mahaifiyarsa suka koma gida. Da matarsa ta gan shi da garken shanu, kuma ga mahaifiyarsa tana gani raɗau, sai haushi da mamaki suka kama ta. Shi kuma Zama ya kwashe labari ya gaya mata. Jin haka ya sa ta ce ita ma dole ne ya kai uwarta dajin nan idan yana son zama da ita.

Sai ya ce: “To, zan yi duka binda kike so, saboda ina son ki.” Bayan kwana uku da dawowar uwar Zama daga dajin mutuwa, matarsa ta tafi garinsu, ta ɗauko uwarta, domin ita ma a kai ta can ta samo shanu. Haka kuwa aka yi ya ɗauke ta ya kai ta daji ya baro. Da ta ji kukan kura na farko, sai ta kiɗime ta kama ihu, ta tsure.

Nan take kuwa kuraye suka far mata suka cinye ta. Da gari ya waye Zama da matarsa suka kama hanyar daji domin su koro shanun uwar matarsa, amma da suka je inda suka kai ta, sai suka tarar sai ƙasusuwanta; kuraye sun cinye ta, kuma ba shanu. Tun daga dajin matar Zama ta kama kukan baƙin ciki, ta kasa komawa gida ta tare a gindin wata kurna tana ta sharar kuka. Kurunkus.

Abubuwan Da Labarin Yake Koyarwa

  • Gaskiya da riƙon amana su ne maganin makirci da makirai.
  • Hassada da ganin ƙyashi su suke sa a faɗa kogin da-na- sani.
  • In za ka gina ramin mugunta, gina gajere.
  • Tun ran gini, tun ran zane.

Wannan tatsuniya an ciro ta ne daga littafin TASKAR TATSUNIYOYI wanda Bukar Usman OON ya wallafa.

Danna nan don karanta Tatsuniyar Sandar Arziƙi

Edita@rumasau-kallamu

labarin da ya wuceTatsuniyar Sandar Arziƙi
wikiHausa
wikiHausa kundin ilimi (insakulofidiya) ce da ke ilimantar da jama'a yara da manya da maza da mata wajen samun ilimi a saukake, cikin harshen Hausa.