Tatsuniyar ‘Yar ‘auta Da Kogin Rantsuwa

0
11

Ga ta nan, ga ta nanku.

Akwai wani mutum mai mata ɗaya da ‘ya’yansu tara maza da mata, waɗanda yake ƙaunar su ƙwarai. Kullum idan ya je kasuwa, sai ya sayo kifaye tara saboda yaran nan. Suna nan haka cikin annashuwa, sai wata rana da ya kai kifayen nan tara, ‘yar autar gidan ta ɗauki ɗaya ta cinye ba tare da ta tambaya ba.

Ta yi haka ne kuwa saboda wautar ƙuruciya. Da ya duba ya ga kifaye ba su cika ba, sai ya ce a tafi rafin Tantafane domin ‘yan ruwa su yi maganin wanda ya cinye kifin nan. Shi ke nan, da suka je sai babbar cikinsu ta fara waƙa tana cewa:

“Kogi, kogin Tantafane,

In ni na cinye kifin baba,

Ruwa ka tafi da ni,

Kar ka dawo da ni.”

Da haka ɗaya bayan ɗaya har takwas daga cikin yaran suka yi waƙa, amma ruwan bai cinye su ba, ya rage ‘Yar auta. Ita kuma tana can gefe tana shirme irin na yarinta, sai suka ce: “Saura ke, ‘Yar’autar iya da baba.” A nan dai ‘yan’uwan suka matsa sai ta yi, har ma suka ce idan ba ta yi ba za su kashe ta.

‘Yar’auta ta sa ƙafafunta a cikin ruwa, ta yi waƙa ƙafin ma ta gama waƙar ‘yan ruwa sun janye ta, wato ruwa ya tafi da ita. To, akwai wata tsohuwa da ta saba da ‘yan ruwan da suka kama ‘Yar’auta. Sun saba da ita ne kuwa saboda ta fi shekara sha uku tana zuwa rafin nan kamun kifi.

Saboda haka ba su cinye ‘Yar’auta ba domin sun ga kyakkyawa ce, sai suka ba tsohuwar nan ita riƙo. Yarinya ta bi tsohuwa kamar ita ce ta haife ta, ita kuma ta riƙe ta kamar ‘yarta. Ana nan, ‘Yar’auta ta girma, har masu neman aurenta suka fara fitowa, har mata fitar da ɗaya daga cikin manemanta, tsohuwa ta amince da zaɓen da ta yi.

To, amma sai ta ce da manemin yarinyar: “Ka je ka kawo buhun kwarkwata, wannan ne abin da za a ba ‘yan ruwa.” Nan da nan yaron ya je ya gaya wa mahaifiyarsa ita da danginta suka haɗa ƙarfi; washe-gari suka kai wa tsohuwa buhun kwarkwata cikakke har da toliya.

Ba tare da wani ɓata lokaci ba aka ɗaura musu aure, ‘Yar’auta ta tare a gidan miji. Ashe angon nan yayan ‘Yar’auta ne bai sani ba, amma ita ta gane, sai dai ta yi shiru ba ta faɗa ba. Duk sanda mazan gidan suka tafi gona, da ta fara dakan garin abincin da za ta yi musu, sai ta fara waƙa tana cewa:

“In daki turmin gidanmu,

In daki turmin gidanmu,

Tim, ƙwal, ƙwal.

A yau uwata,

Ta zama surukata.

Ubana ya zama surukina,

Ƙannena ne abokan wasana.

In daki turmin gidanmu,

In daki turmin gidanmu,

Tim, ƙwal, ƙwal.”

To akwai wata tsohuwa da takan zauna a zaure duk sanda mutanen gidan suka bar amaryar nan a gida, takan ji abin da amaryar kan faɗa. Rannan sai tsohuwa ta ce da mutan gidan: “Idan kun shirya tafiya gona, ku laɓe ku ji abin da amaryar nan za ta faɗa.” Suka kuwa karɓi shawararta, suka kuma aikata abin da ta ce su yi.

Ɗaya daga cikinsu ma ta koma cikin gidan, da amaryar ta gan ta sai ta ce da ita: “Me kike yi a gida?” Sai ta ce: “Na mance fartanyata ne na zo ɗauka, zan koma gona.” Da ta ɗauki fartanya, sai ta yi kamar ta kama hanyar gonar ne, jim kaɗan sai amaryar ta ɗauki turmi, ta hau daka tana yin waƙar da ta saba yi.

Sai ko gaba ɗayansu suka fito daga maɓoyarsu suka ce: “Ashe ‘Yar’auta ce?” Ita kuwa sai dariya take yi tana cewa: “E, ni ce.” Nan take suka rungume juna, kowa sai kukan murna yake yi. Daga nan kuma sai aka manta da zancen aure ta ci gaba da zama a cikin danginta. Kurunƙus.

Abubuwan Da Labarin Yake Koyarwa

  • Shugabannin ƙwarai su suke ƙoƙarin hukunta marasa gaskiya ko da a cikin iyalinsu suka fito.
  • Hukunta marar gaskiya ba zai hana shi zama mutumin kirki ba.
  • Aukawa cikin wata hulɗa ba tare da yin bincike ba yakan haifar da matsala.
  • Kwaɗayi mabuɗin wahala.
  • Kushewar baɗi sai baɗi.

Wannan tatsuniya an ciro ta ne daga littafin TASKAR TATSUNIYOYI wanda Bukar Usman OON ya wallafa.

Karanta Tatsuniyar Gwaidayara

Edita@rumasau-kallamu

labarin da ya wuceTatsuniyar Gwaidayara
Labarin na GabaTatsuniyar Kurege Da Biri
wikiHausa
wikiHausa kundin ilimi (insakulofidiya) ce da ke ilimantar da jama'a yara da manya da maza da mata wajen samun ilimi a saukake, cikin harshen Hausa.