Bahaushe yana qiran mutuwa da sunaye kusan 20, daga cikin akwai rasuwa, fakuwa, qaura, tafiya, rigaya/margayawa, kauwa da sauransu.
Bahaushe ya yi imani da mutuwa, dole ce, ta sanadin tsufa, rashin lafiya, hatsari, kisa, camfi, annoba, rantsuwa da sauransu. Bahaushe na gane mutum ya mutu ta sanyin jiki, farin ido, buxewar baki, qafewar ido da sandarewar jiki (Abdullahi, 2008).
Kafin zuwan addinin Musulunci, Maguzanwan Hausawa ba sa binne gawa sai bayan kwana 3 da mutuwa (Ibrahim 1982), a kan xorawa cikin mamaci dutse, ko takobi ko wani abu mai nauyi da zai hana cikin kumbura kafin a je a binne shi.
Domin karanta bayani akan Bukukuwa Da Wasanni Da Nishadi Na Bahaushe Danna nan
Za a xebo ruwa kwarya a wanke mamaci, sai a cika kwarya da hatsi da (wasu) kayan mamaci a baya mai wanka gawa, dama can Bahaushe na haqa rami ya binne gawar mamaci, da warkinsa a gindi, za a shafa masa shuni da nufin in ya je lahira ya ba wa mutuwa tsoro don kar ta dawo ta xauki wani.
Idan miji ya mutu, za a bawa matar sanda tana yawo da ita, saboda a da an yi imani da fatalwa, wai ko da zai dawo, sai ta doke shi. Za a zubar da ruwan cikin randar gidan, a kife su, a sawa yara toka ko baqin bayan tukunya a zagayen idonsu don zama makarin mafarki da matacce.
Bayan binne mamaci, Bahaushe yana da tsarin zaman makoki, idan za a zo ana yi wa iyalan mamaci gaisuwar mutuwa (ta’aziyya), a wasu wuraren a kan xauki kwanaki uku, wasu huxu, wasu sati (kwana bakwai). Bayan zuwan addini aka ce bidi’a ne, wasu suka daina, amma har yau ana yi a wasu wuraren.
Domin karanta bayani akan Jinya Da Likitancin Bahaushe Danna nan
Ta vangaran gado kuwa, kafin zuwan Musulunci Bahaushe bai ba wa rabon gabo muhimmanci ba, idan ya Bahaushe ya tsufa ne, ya kan qoqarin raba dukiyarsa ga iyalansa sabo da gudun rigima, (Abdullahi, 2008), idan kuma bai raba ba har ya rasu, akan xauki lokaci mai tsayi ba a raba, wani lokacin kuma idan akwai babban xa tsayayye, sai yadda ya yi da ita, babban wa uba ne. zai raba gonaki wa maza, dabbobin kiwo kuma ga mata. A wasu wuraren kuma, mace ba ta da gado, sai na
mahaifiyyarta kawai, Musulunci ne da ya zo ya yi wa mace gata. Idan kuma ‘ya’ya ne suka rasu, za a raba gadonsu har ga kishiyoyin gidan, da ‘ya’yansu. Bahaushe yana alfahari da bajintar iyayensa da kakaninsa.