Bukukuwa Da Wasanni Da Nishadi Na Bahaushe

0
26

Bahaushe yana da bukukuwan gargajiya tun kafin zuwan  addinin Musulunci, daga ciki akwai na bauta, raya  al’ada, aure, suna da mutuwa.

Daga cikin bukukuwan  gargajiya akwai bikin buxin dawa, bikin shan kabewa,  fashin ruwa, bikin noma, tuwon daji, tuwon qunshi,  bikin sana’o’i (festival). 

Bayan zuwan addinin Musuluci, Bahaushe ya qara da  bukukuwan idin qarama salla (azumi) da babbar sallah  (layya), maulidi, takutaha, daba (don tunawa da wani  al’amari). 

Domin karanta bayani akan Fasahar Bahaushe Danna nan 

Bayan zuwan turarawa, party ko picnic (na tunawa da  ranar haihuwa ko na bikin aure), qaddamar da ko buxe  gini wallafa (launching/grand opening) da sauransu. 

Wassani da Nishaxi  

Bahaushe yana wasannin langa, iyon ruwa, tsiren gudu,  kokawa, dambe, tauri, was an voyo, yara na ‘yar tsana,  rawa, gaxa, carafke,. Bayan zuwan turawa aka sami  karta da lido, sai kwallon qafa, da tseran babur, mota da  keke. 

Bayan zuwan addinin Musulunci kuma, Bahaushe ya  qirqiri wasan tashe a lokacin azumi, domin tashin  mutane sahur, hana albozaranci ko don nishaxantarwa (Ahmed, 1985).

Domin karanta cikekken littafin Danna nan 

 

labarin da ya wuceBahaushe Da Tattali Arziki
Labarin na GabaSutura Da Kwalliyyar Bahaushe