Sutura Da Kwalliyyar Bahaushe

0
23

Al’adun Bahaushe suna kamancecceniya da na Larabawa  da Habashawa da Kanuri wajen suturta jiki, wataqila  saboda alaqa uwar harshe da suka haxa (a tunanina).

Tun  kafin zuwan addinin Musulunci, Bahaushe yana qoqarin  suturta al’aurarsa, da bantai, taguwa (riga ‘yar ciki da  babbar riga), wando tsala, takalmi fele, hula kube, zanin  mata, gyale/mayafi da kallabi (Lawi, 2017).

Domin karanta bayani akan Bukukuwa Da Wasanni Da Nishadi Na Bahaushe Danna nan 

Bahaushe ya sami baqin sutura daga Larabawa da Turawa  da sauran qabilun da ke kewaye da shi. Bahaushe ya xauko  jallabiyya, abaya daga Larabawa, sai kwat, siket, nek tayal,  gown daga Turawa. Sai hulunan Kanuri, damanga, zanna  bukar da sauransu. 

Bahaushe mutum ne mai gyaran jiki da tsafta, yana wanka  a kogi, ko gulbi, ko makewayi, yana aski, da gyaran fuska da yanke farce. Mata kuma na qunshi da lalle, kitso.  

Domin karanta cikekken littafin Danna nan 
labarin da ya wuceBukukuwa Da Wasanni Da Nishadi Na Bahaushe
Labarin na GabaJinya Da Likitancin Bahaushe