Bahaushe yana da fasahar duba marasa lafiya ta hannun bokaye, maxora, magori, ‘yan bori, ‘yanganye (herblists), wanzamai suna bayar da magani, ko duba maras lafiya.
Kamar wanzami, yana qaho (hujuma) da kaciya, maxori na xora karaya, magori, bokaye da ‘yan daganye na bayar da itatuwan magani.
Domin karanta bayani akan Bukukuwa Da Wasanni Da Nishadi Na Bahaushe Danna nan
SUFURI
Kafin zuwan ababen hawan zamani, Bahaushe na tafiya da qafafu duk nisan tafiya, ko amfani da dabbobin ni’ima, irin su dawakai, jakkai da rakuma. Bayan zuwan Turawa kuma, Bahaushe na iya siyen motoci, Babura, kekuna har da jirgin sama. Su kuma dabobin sufuri, kamar doki, aka taqaita amfani da su, sai a lokutan bukukuwan sallah, ko hawan daba