Ga ta nan, ga ta nanku.
Akwai wasu ’yan mata su goma sha biyu ƙawaye. A cikinsu har da wata ’yar Sarki mai suna Kanta. Ita kaɗai ce a wurin mahaifiyarta. Ita ce kuma ta fi kyau a tsakanin duk ’yan matan garin. Kowane saurayi a garin yana so ya aure ta, amma ta ƙi. A cikin waɗanda suke son ta har da wani maciji wanda ke zaune a cikin kogin da ke kusa da ƙauyen.
Sauran ’yan matan suna kishin Kanta saboda farin jininta da kyauta. Saboda haka suka haɗa baki cewa za su ja ta zuwa kogin nan domin su kashe ta. Mahaifiyar Kanta ta gane duk ƙulle-ƙullen da ’yan matan suke yi game da ’yarta, saboda haka ta yi ta ƙoƙari ta kare ta.
Duk lokacin da ’yan matan suka zo neman Kanta, sai ta ce da su ba ta nan. Wata rana sai uwar Kanta ta tafi wata unguwa ziyara. Ganin haka ’yan matan nan suka je har cikin gidan Sarki suka ja hankalin Kanta har ta amince za ta bi su kogin nan. Ta bi su da sunan kamun kifi za su.
Da suka isa kogin, sai suka ga wani mangwaro mai ’ya’ya, kuma suka yanke shawara za su hau domin su tsinki na sha. Kanta ta ƙi hawa, amma suka matsa mata, har dai ta hau. Kowaccensu ta roƙi Kanta da ta tsinko mata mangwaro. Macijin da ke kogin nan ya ji hayaniya ta yi yawa, sai ya fito.
Ya nufi inda ’yan matan nan suke. Da suka gan shi suka gudu, suka bar Kanta a sama. Macijin ya hau itacen ya same ta. Can daga baya ’yan matan suka koma wajenta, suka ga halin da take ciki. Da suka iso sai suka kama waƙa, suna cewa:
“Kai macijin nan don Allah,
Ka sassauta wa Kanta ta sauko,
Kai macijin nan don Allah,
Ka sassauta wa ƙawarmu Kanta ta sauko.”
Kanta kuwa sai hankalinta ya tashi. Da mahaifiyarta ta dawo ba ta gan ta a gida ba, sai ta shiga nemanta. Ta shiga nan ta shiga can har dare ya yi ba ta gan ta ba. Ƙawayen Kanta kuwa suka koma gida dab da almuru, suka baro ta a kan mangwaron nan na bakin kogi.
Allah da ikonsa sai ga wani ɗan tsuntsu fari ya zo ya sauka kusa da Kanta; sai ta roƙe shi, ta ce: “Kai ɗan farin tsuntsun nan, don Allah ka taimake ni ka kai saƙona ga iyayena. Babana shi ne Sarkin garin. Ka gaya musu cewa ina cikin matsala. Ƙawayena duk sun gudu sun bar ni da wani maciji wanda yake so ya haɗiye ni.
Ina nema su kawo mini gudunmawa da wuri don su kuɓutar da ni daga wannan matsala.” Ɗan tsuntsu ya yarda; ya tashi sai fadar Sarki. Da ya isa gaban Sarki sai ya ce: “Mai martaba, na zo ne in ba ka saƙo daga ’yarka.” Da jin haka sai mamaki ya kama Sarki da matarsa.
A gigice Sarki ya ce da ɗan tsuntsu: “Yi maza ka gaya mana saƙon.” Ɗan tsuntsu ya ce: “Mai martaba, ’yarka ce tana can dogon daji; tana kan wata babbar bishiyar mangwaro, kuma wani babban maciji ya kusa ya haɗiye ta.” Da jin haka, ba tare da ɓata lokaci ba Sarki ya tattara dogarawansa suka tafi ɗan tsuntsu na nuna musu hanya.
Da suka isa sai suka tarar macijin ya fara barci. Ba tare da yin wani motsi da zai farkar da maciji ba, suka ce ɗan tsuntsu ya yi ƙoƙari ya goyo Kanta, ya sauko da ita. Ɗantsuntsu ya je wajen Kanta ya gaya mata zai goye ta. Ya juya baya ta ɗare, ya tashi fir, yana nishi, da ƙyar ya kai ta fada.
Dogarai suka sulale, suka bar maciji na barci, suka isa fada lafiya. Washe-gari Sarki ya sa a kirawo duk ƙawayen ’yarsa. Suka zo fada. Da aka bayyana duk abubuwan da suka faru, sai ƙawayen Kanta suka tuba, tare da yin alƙawari ba za su sake yin irin wannan abu ba har abada.
Suka roƙi Sarki ya yafe musu. Sarki ya yarda, ya yi musu afuwa. Ya kuma sa wasu samari su auri ’yan matan. Aka yi babban biki a fadar Sarki. Har yanzu waɗanda suka san an yi wannan biki sukan ce ba su taɓa ganin biki mai armashi da ƙayatarwa kamarsa ba.
Amma fa wani abu shi ne, duk da shagalin da aka yi lokacin bikin nan cikin farin ciki, Sarki bai huce baƙi ɗaya ba; sai da yasa aka je aka kashe macijin nan. Zaratan da suka kashe macijin suka ɗauko mushensa suka kai fada. Maciji ne mai tsawon gaske, kuma ba wanda ya taɓa ganin irinsa a ƙauyen.
An ce ya halaka wasu daga cikin zaratan da Sarki ya tura suka kashe shi. Sarki ya yi wa waɗanda suka mutu wajen kashe macijin alheri, wanda aka ba iyalansu, kuma waɗanda suka dawo lafiya daga cikinsu ya yi wa kowannensu aure. Mutanen garin kan yi bikin tunawa da waɗanda suka rasu saboda bajintar da suka yi. Kurunkus.
Abubuwan Da Labarin Yake Koyarwa
- Ba a rama kirki da mugunta.
- Kowa ya ci amana sai amana ta ci shi.
- Wayo ya kada sarkinsa.
Wannan tatsuniya an ciro ta ne daga littafin TASKAR TATSUNIYOYI wanda Bukar Usman OON ya wallafa.
Danna nan don karanta tatsuniyar Tatsuniyar Dila Da Zomo
Edita@rumasau-kallamu









