1. Watan cika ciki (Almuharram).
Bahaushe, yana yi masa wannan laƙabi ne, saboda abinci da ake ci a ƙoshi sosai, bayan an gama bikin sallah babba, Bahaushe yana ajiye awazar (ƙugun naman dabba) nama ko jela, har sai watan ya kama, sai ya ɗauko naman (raguwar naman layya), ya dafa shi sosai, a yi abinci sosai, sai taru a ci, a sha, sosai, shi ne yake yi masa suna da bikin sallar cika ciki.
2. Bawan watan cika ciki (Safar).
Shi kuma, wata ne wanda yake bin watan da aka yi cika ciki a cikinsa, idan akwai ragowar nama, wanda mutum bai cinye ba, to a watan ake gama cinyewa, saboda akwai wani bikin ma a gaba, wato watan maulid.
3. Tagwai “watan maulid” (Rabbiyul-auwal).
Shi kuma watan murnan maulidi ne, kuma ya yi masa laƙabi ne da “Tagwai”, saboda ma’anar sunansa ta tagwaye (wato watanni biyu masu suna a ɗaya a jere, Hassan da Usaini), wato Rabbiyul-auwal da kuma Rabbiyul-thani.
4. Tagwai “watan bawan maulid” (Rabbiyul-thani).
Wata ne, wanda yake bin watan da aka yi shagalin bikin maulidi a cikinsa.
5. Gambon wata (Jumada Auwal)
Wata ne, watan yake bin tagwaye (Rabbiyul-auwal da kuma Rabbiyul-thani).
6. Tankon wata (Jumada Thani).
Wata ne ,wanda yake bin gambo, shi kuma a cikinsa ana yin tanajin fara azumi ga tsofaffi.
7. Watan azumin tsofaffi (Rajab).
Wata ne, wanda tsofaffi suka fi yin azumi a cikinsa, saboda ƙara samun kusanci ga Allah gami da jure wahalar azumi, saboda yin azumin watan Ramadan lafiya. Amma yara ma suna yin azumi, sai dai tsofaffi sun fi yin azumi a cikinsa.
8. Watan sallar tsofaffi (Sha’aban).
Wata ne, wanda ake yin bikin sallah, saboda an gama azumin tsofaffi lafiya, sai a shirya kayan liyafa ta musamman, don warware gajiya.
9. Watan azumi (Ramadan)
Wata ne, wanda ake yin azumin farilla a cikinsa, wanda mafi yawan Hausawa musulmai ne bayan an rushe maguzanci daga gare su.
10. Watan ƙaramar sallah (Shauwal).
Wata ne, da ake yin bikin sallah, za a shirya kayan abinci na musamman da ziyarce-ziyarce da bukukuwa daban-daban, don murnar kammala azumi lafiya.
11. Watan bawan sallah ƙarama (Zulƙida)
Wata ne, wanda yake bin watan da aka yi bikin sallah a ciknsa, kuma wata ne wanda ake yin tanajin dabbar da za a yanka da babbar sallah.
12. Watan babbar Sallah (Zulhaj).
Wata ne, wanda ake yin bikin sosai, saboda wata ne na ƙarshe daga cikin jeren watanni, kuma Bahaushe yana yanka dabbobi sosai, don samun abin da za a ci gami da rabawa abokanan arziki. Saboda a cikin al’adar Bahaushe babu rowa a ciki, Bahaushe ya samu rowa ne daga Turawa, saboda shigowar ilimin boko.
Danna nan don karanta hanyar korar aljanu da kariya daga dawowarsu
Edita; Rumasa’u M. Kallamu