Nasiha Mai Tsoratarwa

0
52

BISMILLAHIR RAHMANIR RAHEEM.

Tsira da aminci su tabbata bisa Annabin ƙarshe, da dukkan iyalansa da sahabbai baki ɗaya.

Yazeedur Raqqashiy ya karɓo Hadisin daga Anas bn Malik (R.A) yana cewa:
Watarana Mala’ika Jibrilu (A.S) ya zo wajen Manzon Allah (S.A.W) a wani lokacin da bai saba zuwa masa ba. Ya zo, gaba ɗayan launin fuskarsa ya canza. Sai Manzon Allah (S.A.W) yace masa “MAI YASA NA GA LAUNIN FUSKARKA DUK YA CANJA HAKA?”

Yace “Ya Muhammadu (S.A.W) na zo maka ne a wannan lokacin da Allah ya yi umarni da masu hura wuta su ci gaba da hura ta. Duk wanda ya san cewa Jahannama gaskiya ce, wuta gaskiya ce, azabar kabari gaskiya ce, kuma azabar Allah ita ce mafi girma, to bai kamata ya yi wani farin ciki ba har sai ya tabbatar da cewa ya samu tsira daga wannan”.
Sai Manzon Allah (S.A.W) yace masa “YA JUBREELU INA SO KA SIFFANTA MUN YADDA
JAHANNAMA TAKE”.

Sai yace “Na’am. Haƙiƙa Allah maɗaukakin Sarki yayin da ya halicci Jahannama, ya sa an hura ta tsawon shekaru DUBU. Har sai da ta zama JA -JAWUR. Sannan aka sake hura ta tsawon Shekaru DUBU har sai da ta zama FARI – FAT!! Sannan aka sake hura ta tsawon shekaru DUBU har sai da ta zama BAƘA – ƘIRIN!!! Tana nan har yanzu BAƘA ƘIRIN ce, mai tsananin duhu ce. Harshen balbalinta ba su mutuwa ballantana garwashinta.

Na rantse da girman Ubangijin da ya aiko ka da gaskiya, da a ce za a buɗe misalin ƙofar allura daga wutar Jahannama, Wallahi sai dukkan ma’abotan doron duniyar nan sun ƙone baki ɗayansu saboda tsananin zafinta.

Na rantse da girman Ubangijin da ya aiko ka da gaskiya, da a ce za a ratayo tufafi guda ɗaya tufafin ‘Yan wutar Jahannama a maƙalo shi a tsakanin Sararin Samaniya, da sai dukkan ma’abotan doron ƙasa sun mutu baki ɗayansu saboda tsananin warin wannan tufafin. Da kuma zafin da ke tattare da shi. Babu wanda zai yi saura a cikinsu don tsananin abinda za su riska na zafin wannan tufafin.

Na rantse da girman Ubangijin da ya aiko ka da gaskiya a matsayin Annabi, da a ce za a ɗauko zira’i guda na Sasarin nan na ‘yan wuta (wato sarƙa ɗin da ake ɗaure su da shi sannan a riƙa jan su akan fuskarsu). Wannan wanda Allah ya ambata a cikin Alqur’ani, a ɗora shi bisa wani dutse daga duwatsun duniyar nan, da sai dutsen ya narke ya zagwanye har zuwa ƙasa ta bakwai.

Na rantse da girman Ubangijin da ya aiko ka da gaskiya a matsayin Annabi, da a ce za a ajiye wani mutum a mafaɗar rana ana yi masa azaba, da sai wanda yake mahudar rana ma ya ƙone ƙurmus saboda bala’in zafinta. Zafinta mai tsanani ne. Zurfinta mai nisa ne.
Tufafin cikinta na ƙarfe ne. Abin shan cikinta HAMIMU ne (tafasasshen ruwan azaba) da kuma ruwan gyambo.

Mayafan cikinta kuma an yanko su ne daga Wutar”. Tana da ƙofofi guda bakwai, kowacce ƙofa tana da wani yankin cikinsu da aka tsaga mata (za su shiga ta cikinta) daga mazaje da mataye. Sai Manzon Allah (saww) yace: “SHIN KOFOFIN NAN IRIN NAMU NE?”
Sai Jibrilu yace: “A a sai dai ita ƙofofin a buɗe suke, wata ƙofar tana ƙasan wata.
Tsakanin kowacce ƙofa da wata ƙofar, tsawon tafiyar shekara SABA’IN ne.

Kowacce ƙofa ta ninka wacce take sama da ita a tsananin azaba har ninki SABA’IN.
Za a riƙa kora maƙiyan Allah cikinta. Kuma duk sanda aka koro wasu (‘Yan wuta) zuwa wata ƙofa, Zabaniyawa ne za su tarbe su da sarƙoƙi da sasarai. Za a zira musu sasari (chains) ta cikin bakinsu sai ya fito ta duburarsu. Sannan za a ɗaure hannunsa na hagu a jikin wuyansa, hannunsa na dama kuma za a fasa ƙirjinsa da shi a turo shi ta cikin zuciyarsa sai ya fito ta bayan kafaɗarsa. Sannan a haɗa a ɗaure da waccan sarƙar.

Kowanne ɗan Adam za a haɗa shi tare da shaitani guda a cikin sarƙar sasarin, Sannan a riƙa jan sa akan fuskarsa (a cikin garwashin wutar da kuma dagwalonta) mala’iku kuma suna jibgar su da gudumomin baƙin ƙarfe. Duk lokacin da suka nemi fita daga cikinta saboda baƙin ciki da wahala, sai a sake dawowa da su cikinta. Sai Annabi (S.A.W) yace ma Jibreelu (R.A) “SHIN SU WANENE MAZAUNAN CIKIN WAƊANNAN ƘOFOFI?”

Sai Mala’ika Jibreelu yace: “Ka ga amma ƙofar nan wacce take can ƙarƙashin ƙasa, ita ce mazaunar munafukai da kuma waɗanda suka kafirce daga mutanen Annabi Isa (A.S) (Waɗanda aka ce kar su ɓoye abinci amma suka yi taurin kai suka ɓoye). Da kuma mutanen Fir’auna. Ita wannan wutar sunanta “HAAWIYAH”.

Sai kuma ƙofar nan ta biyu, waɗanda za su shiga cikinta su ne MUSHRIKAI. Kuma sunanta “AL-JAHEEM”. Ƙofar ta uku kuwa masu bautar taurari ne za su shiga ta cikinta. Su ne mazaunan cikinta. (a wani wajen an ce za su zauna tare da masu wasa da sallah). Kuma sunan wannan wutar “SAƘAR”.

Ƙofar wuta ta huɗu, ta nan ne IBLIS (L. A.) zai shiga cikinta tare da mabiyansa da kuma
Majusawa masu bautar Wuta. Kuma sunanta “LAZAA”. Kofa ta biyar kuwa ta cikinta YAHUDAWA za su shiga. Kuma sunanta “ALHUTAMAH”. Kofa ta shida kuwa, NASARA ne za su shiga ta cikinta. kuma sunanta “SA’EER”.

Daga nan kuma sai Mala’ika Jibrilu ya sunkuyar da kansa ya yi shuru, ya kasa ci gaba da magana saboda jin kunyar Manzon Allah (S.A.W). Sai Manzo (S.A.W) yace masa “SHIN BA ZA KA BA NI LABARIN KO SU WAYE MAZAUNAN CIKIN WANNAN KOFAR TA BAKWAI ƊIN BA?” Sai Jibrilu yace: “Su ne ma’abotan manyan zunubai daga cikin al’ummarka. Idan har suka mutu ba su tuba ba” Nan take Sai Sayyidina Rasulullahi (S.A.W) ya faɗi YA SUMA!!!
Sai Mala’ika Jibrilu ya ɗauki kansa ya ɗora akan cinyoyinsa har sai da ya farfaɗo sannan
yace:

“YA KAI JIBRILU LALLAI MUSIBA-TA TA GIRMA! KUMA BAKIN CIKINA YA TSANANTA!!! YANZU ASHE AKWAI WANDA ZAI SHIGA WUTA DAGA CIKIN AL’UMMATA?” Sai yace “Eh amma ma’abotan manyan zunubai daga cikinsu”. Daga nan Sai Manzon Allah (S.A.W) yasa kuka, Mala’ika Jibrilu ma yana kuka…!!!” Ibnu Katheer ya kawo wannan hadisin da ruwayoyi daban-daban a cikin littafinsa mai suna AN-NIHAYAH FIL FITAN WAL MALAHIM. A cikin babin da ke magana akan wuta da azaba cikinta.

Allah (S.W.T) Ya yafe mana zunuban mu manya da ƙanana. Amin. Manzon Allah (S.A.W) ya na cewa mutanen da ke kusa da ni a ranar tashin Alƙiyama su ne masu yawan yi min salati! Allahumma salli Ala Muhammad wa sallim!

Domin karanta Nasiha Tsakanin Musulmi danna nan

Edita; Rumasa’u M. Kallamu

labarin da ya wuceSunayen Watanni Da Hausa (Gargajiya)
Labarin na GabaAuren Annabi SAW Da Nana Khadija