Hadisai A Kan Kada A Goyi Bayan Mai Laifi

0
281

Hadisi Na Ɗaya A Kan Kada A Goyi Bayan Mai Laifi

An karɓo daga Abdullahi ɗan Umar (Radiyallahu Anhu) ya ce: Na ji Manzon Allah (Sallallahu Alaihi Wasallam) yana cewa: “Duk wanda alfarmarsa ta hana a yi wani hukunci na Allah, haƙiƙa ya kishiyanci Allah Ta’ala, kuma duk wanda ya yi husuma a kan ƙarya yana sane, zai kasance cikin fushin Allah Ta’ala, kuma duk wanda ya yi wa wani mumini ƙage, Allah zai zaunar da shi a dagwalon Khabalu (Tafkin da surƙamin ‘yan wuta yake taruwa) har sai ya janye abinda ya faɗa.
Abu Dawud da Hakim ne suka ruwaito shi.

Ƙarin Bayani

Wannan hadisi ya ƙunshi abubuwa uku muhimmai:

1- Duk mutumin da ya hana a hukunta mai laifi; saboda matsayinsa to haƙiƙa ya yi daidai da mai ƙalubalantar Allah da kishiyantar sa. Wato ya mayar da kansa kamar wani kishiya ga Allah.

2- Wanda yake ba da kariya ga mai laifi alhali ya san ba shi da gaskiya; Allah zai ta yin fushi da shi har sai ya janye jikinsa ya bar shari’a ta yi aikinta. Wannan ya haɗa da iyaye da ‘yan uwa da lauyoyi; da sukan kafe su yi ta jayayya a kan kare wanda su da kansu sun san ba shi da gaskiya.

3- Masu yi wa mutane ƙage da sharri suna cikin babban hatsari; za a jefa su cikin dagwalon da ake tara da tafasa ruwan ciwo da ƙuraje na ‘yan wuta a ranar lahira; har sai sun daina yaɗa shi wanda tun daga nan duniya za a yi hakan in kuwa aka yi sake aka je lahira to fa sai yadda ta yiwu.

Hadisi Na Biyu A Kan Kada A Goyi Bayan Mai Laifi

Wani abu da yake kawo cikas ga ci gaba da nagartar kowace gwamnati da al’umma; shi ne neman alfarma da masu faɗa a ji sukan yi, domin a ƙyale masu laifi; ko kuma a sassauta hukuncin da ya dace a yi musu, ta yadda koda an yi hukuncin, sai ya zama kamar wasa. Wannan sai ya ƙarfafa guiwar ‘yan gata su yi ta tafka ta’asa son ransu; har ma aikata laifi ya zama wata burga da nuna isa, wato iya matsayinka ko gatanka, iya damarka ta aikata laifi, ka kwana lafiya. To shi me Manzon Allah (Sallallahu Alaihi Wasallam) ya faɗa kan nemawa masu laifi alfarma a ƙyale su?

Wannan bayanin an ciro shi ne daga Littafin Shugabanci A Musulunci (Hadisai Tamanin Da Biyu A kan Shugabanci); wanda Shehu Mansur Dala ya wallafa shi. Domin karanta cikakken Littafin danna nan.

Domin karanta cikakken bayani a kan Hadisi Na Ɗaya A Kan Haramcin Goyon Bayan Azzaluman Shugabanni danna nan

labarin da ya wuceYadda Ake Yin Tasbihi A Ruku’u
Labarin na GabaFalalar Adalci, Tausayawa Mabiya Da Illolin Gallaza Musu