VAGINAL DISCHARGE (FITAR DA RUWA AGABAN MACE)

0
40

VAGINAL DISCHARGE: a takaice itace fitar da ruwa a gaban mace shi ake kira vaginal discharge.

Abin da ya kamata mu sani shi ne ba ko wacce irin fitar da ruwa a gaba shine infection ba.

LAUNUKAN RUWAN DA YAKE FITA A GABAN MACE

Akwai launuka daban daban wadanda a dalilinsu ne ma ake iya rarrabe nau’o’in ruwan da ke da matsala da kuma mara matsala, gasu kamar haka :

1- White discharge (Vaginal Lubrication) : Akan sami dan farin ruwa kadan yana fita a gaban mace, dab da fara al’ada wannan ba matsala bace.

– Tsinkakken farin ruwa mara Kaikayi da  yake fita a gaban mace Yana da amfani na tsaftace gaban mance da tabbatar da lafiyar gabar mace a kowanne lokaci.

 Yadda halittun gaban mace take kullum iya kokorin  kawar da matattun qwayoyin jiki da sauran qwayoyin cuta dake kwance a gabanta ko bakin mahaifa shi yasa ma cikin gaban mace ba bukatar dole dole a ansaka sabulu an wanketa.

2- Thick White : Farin ruwa mai yauki da kauri kamar majina mafi yawa ana ganin wannan bayan Al’ada da kwana 6 zuwa 10  wannan yana nuni ne da cewa lokacin Ovulation ne (Lokocin da mace tagama kyenkeshe koi) shi ma ba wata matsala ba ce.

3- Blushed deep pink: a likitance mance idan tagama Al’ada , kamar yadda mukai bayani a sama gaban mace tana tsaftace kanta , shine dalilin ganin wannan pink discharge bayan gama al’ada.

Kuma masu sabon ciki sukan yi wannan pink discharge alamace ta ciki shima ba matsala bace.

Sannan yana dakyau ku karanta wannan Kawar Da Fargaba Kan Dalilan Sanya Robar Hanci Ga Mara Lafiya

Kuma wani lokoci pink Vaginal discharge zai iya zama matsala idan yazo da alamomi kamat haka :

1- Karni

2- Kaikayi

3- Tsananin ciwon ciki.

4- Yellow – Green :  Wannan itama wani lokocin takan faru ta dalilin matsalar abinci ko karancin wassu daga cikin sinadaran vitamin.

Shima idan yazo da alamomi kamar :

Kaikayi 

Karni 

Ciwon ciki 

Yakamata aga likita kai tsaye domin matsala ce.

5- Gray or dark discharge: wannan kai tsaye maatsala ce Wanda kwayar cutar bakteria take haifarwa tana zuwa da alamomi kamar haka :

Kaikayi

Ciwon ciki

Karni

Zapi 

Yana dakyau kuranta Jan Hankali Ga Masu Cin Smoked Fish (Bandar Kifi)

ME YAKE KAWO INFECTION NA MATA

1- Bacteria Vaginosis : wannan wani kwayar cutace dake rayuwa  cikin farji yakan haddasa matsalar Sanyin mata .

2- Candidiasis : wannan wata kwayar cutace Wanda yake haddasa Sanyin Gaba. Wadannan kwayoyin cutar suna zama cikin farji kuma basu cika cutarwa ba, wadannan kwayoyin cutar suna son waje mai gumi domin su girma dan yaduwa.

3- Trichomonas Vaginalis  : wannan itace wacce take yaduwa ta hanyar jima’i. Ita wannan kwayar cutar parasite ce take kawoshi .

4- Irritation Vaginitis : ita wannan ana kiranta da Allergic , wassu abubuwanda jikin mutun bai daukesu ba, anasamunsa wajen amfanida kamar su condom, sabulu , ko maganin shafawa.

YAYA MACE ZATA KARE KANTA DAGA KAMUWA DA INFECTION NA MATA

1- Avoid Vaginal Douching : A cikin Farji akoi wassu kwayoyin bakteriya wadanda basa cutarwa kuma sunada amfani , amfaninsu shine suna taimakawa wajen bada kariya ga Farji , sai kaga wassu matan sukan wanke Farji da Sabulu ko detol haka , wadannan abubuwanda ake amfani wajen wanke farji yakan kashe bakteriya masu amfani na Farji , Sai masu cutarwa su samu daman shiga.  A kiyaye wanke Farji Da Sabulu dakuma wadansu abubuwa Wanda bamusan Kansu ba.

Domin karanta bayani akan Ciwon Zuciya Tsantsa (Heart Failure) Danna nan 

2- Uses of Underwear : Amfani da wandon pants , wassu matan sukan bar wandonsu yayi datti , Barin datti ko amfani pant masu datti yakan bawa kwayoyin cuta daman shiga Farji.

A Tsaftace wanduna.

3- Cleaning Faeces : wajen wanke bahaya mafi yawa mata sukan dauki kwayar cutar da take dubura zuwa Farji, wanda basa yiwa dubura illa amma sukan yiwa Farji illah.

 Shawara shine afara wanke Farji kafin a wanke dubura.

4- Sharing of Underwear:  amfani da pants na wassu , ta yiu wacce kuke amfani da pants daya tanada cutar Sanyi idan kinyi amfani da nata kema zaki iya dauka.

5- Sexual intercourse : mutun yakan iya daukan wannan cutar lokocin saduwa da namiji shawara itace adinga amfanida Condom lokocin saduwa.Ga wanda suke da tambaya zasuyi join Tambaya and answer sai suyi aciki za abasu answers Aciki.

Karanta Kadan Daga Cikin Cuttukan Da Ake Dauka Ta Hanyar Saduwa (Jima’i) (Sexually Transmitted Diseases

labarin da ya wuceKadan Daga Cikin Cuttukan Da Ake Dauka Ta Hanyar Saduwa (Jima’i) (Sexually Transmitted Diseases
Labarin na GabaBAYANI GA MAZA MASU MATSALAR HAIHUWA SANADIYYAR ƘARANCIN MANIYYI [LOW SPERM COUNT]