HEPATITIS B: (Ciwon hanta)
Ciwo ne daya ke kawo kunburin hanta ita kuma ƙwayar cutar hepatitis virus ne yake kawota tana yaduwa ta hanyar saduwa da mai ciwon ko idan jinin mai ciwon ya gauraya da wanda bashi da ciwon ko ta hanyar allura ko hatsari ko kiss.
HEPATITIS A & C:
Wadannan suma suna daga ciki ƙwayar cutar virus ne take kawo su,kuma suna saka hanta ta kumbura.
Domin karanta bayani akan Ciwon Zuciya Tsantsa (Heart Failure) Danna nan
Gonorrhoea:
Ciwon sanyi ne mai ta’adi wanda yakan kama mace ko namiji ta hanyar jima’i da wanda ke dauke da ƙwayar cutar ana kiran kwayar cutar Neisseria gonorrhoea.
CHLAMYDIA:
Ita ma wannan kamar ciwon gonorrhoea yake amma ya banbanta kadan da gonorrhoea kuma kwayar cutar dake kawo su ba iri daya bane. tana zuwa da alamomi kamar haka zubar da fararen ruwa, wata rana harda jini, da ƙaiƙayi da zafin saduwa da kuma yayin fitsari.
H.I.V/AIDS:
A Hausan ce ana kiranta cutar ƙanjamau itama ƙwayar cutar HIV virus ne yake kawota tana zuwa da alamomi da yawa kamar zazzabi mara yankewa, rama, gudawa mara tsayawa, ƙuraje a cikin baki, kasala,tari da yawan rashin lafiya da makamantan su.
Syphilis:
Itama wannan tana daya daga cikin su ƙwayar cutar bakteria ce take kawo shi,yana janyo ƙurajen gaba ga mace ko namiji,ko kuraje ga dubura,ko baki, kuma tana shafar ƙwaƙwalwa da idanu da kunnuwa da zuciya.
Yana dakyau kuranta Jan Hankali Ga Masu Cin Smoked Fish (Bandar Kifi)
CANDIDIASIS:
Ita wannan itama kusan tafiyar su daya ne da su gonorrhoea amma ita ƙwayar cutar fungal ce take haddasawa, kuma tanada wuyan sha’ani mafi ya tafi kama mata.
8.) TRICHOMONIASIS : Itama wannan na daya daga cikin su kuma tana zuwa da alamomi kamar na sauran kuma kwayar cutar fungal ne take kawoshi.
9.) HERPES : Cuta ce mai hatsarin gaske wanda kwayar cutar visus ke kawoshi tana zuwa da qurajene zasu iya fitowa a wajaje daban daban kama daga cikin baki, ko akan lebbe ko a cikin hanci da al’aura ko maqogwaro,suna da zafi.
10.) CANDIDA BALANTIS : Itama wannan na daya daga cikin su tana saka qurji akan zakari ko kaciyar namiji ya girma, ya janyo zubar ruwa yayin fitsari da jin ciwo har a cikin jiyojin zakari.
Sannan yana dakyau ku karanta wannan Kawar Da Fargaba Kan Dalilan Sanya Robar Hanci Ga Mara Lafiya