Larurar  Gaggartowar Saurin  Balaga (Precocious Puberty)

0
23

Firikoshiyos Fubati: Wani yanayi ne na tangarɗar halitta dake haddasa gaggawar bayyanar balaga tsakanin kananun yara mata kafin su cika shekara 8 aduniya, da kuma kananun yara maza tun kafin sukai shekaru 9 da haihuwa.

Toh saide anfi gani kuma a shaida matsalar nan da nan a yara mata duba da halittunsu sune suke kusan bayyane ƙarara (nono) saɓanin rukunin Maza.

Waďannan Suffofin Balagar Da Ake Gani A Yara Mata Sune:
  • Bayyanar girman nonuwa a kirji
  • Bayyana kurajen pimples
  • Bayyanar gashin hammata
  • Bayyanar gashin gaba, da kuma
  • Fara jinin haila

Duk ana ganinsu ne tun kafin yarinya ta cika shekara 8 aduniya kamar yadda na fada. Domin karanta Bayani Mai Mahimmanci Zuwa Ga Mata Akan {Ovulation} Shiga nan

Yayin Da Aɓangaren Yara Maza Alamun Da Iyaye Kan Fara Gani Sune:
  • Girman jakar ƴaƴan maraina yaro (scrotum)
  • Gashin gaba cunkus (Pubic hair)
  • Girman azzakari kamar na babba
  • Gashin hammata dana fuska
  • Karyewar murya zuwa ta manya

Duk wadannan na faruwa ne ga yaro tun kafin ya cika shekaru 6 aduniya.

Meke Haddasa Irin Wannan Saurin Balaga

Hakan na faruwa ne sakamakon tangardar aikin wata halitta a kwakwalwa da ake kira FITUITARI GILAN (pituitary glands) wanda shike kunshe da rassa  kimanin shida.

Wanda rassan shida kowannensu da abunda yake samarwa, Kama daga samar da sinadaran dake taimakawa wajen jima’i, narkar da abinci, tace jini, girman jiki, ƙwarin ƙashi, daukar ciki, girman nonuwa, tsatstsafowar ruwan nono, fitsari, naƙuda, jinin haila, samuwar maniyyi da sauransu.  

Toh guda 1 cikin rassa 6 dinne na fituitary sai reshen dake samar da sinadaran haihuwa, sha’awa, jima’i maniyyi, wankin mahaifa da jinin haila ke samun matsalar dake sashi fara sakin duk wadancan sinadarai na (istrojin, furojesteron,) wanda zasu bayyanar da wadancan alamomin cikar halittar mace ko namiji tun kafin lokacin da ya dace su fara bayyana wato tsakanin shekaru 12 zuwa 16 na rayuwa.

Wannan shine gaggawar balaga, wanda ya bambanta da saurin balaga.

Shi Kuma Saurin Balaga [Early Puberty]

Kamar yadda nace a hannu guda kuma baya ga FIRIKOSHUYOS Akwai kuma wata makamanciyar matsalar da akewa laƙabi da Early puberty wato saurin balaga. Shi kuma precocious kamar gaggautowar balaga.

Anan shi ELI-FUBATI shi ma duk ana ganin wadancan suffofin na bayyanar nonuwa tsir-tsir a kirjin yarinya, koma kila inta matsa kan taga hadda ruwa, fara haila, canzawar warin jiki, pimples da bayyanar gashin jiki ga mace. 

Haka ma girman ƴayan maraina, karyewar murya, fitar maniyyi, girman azzakari da duhun matse-matsi, gami da canzawar warin jiki ga yaro namiji.

Sai dai  anan za’a samu yarinyar ta baiwa shekaru 8 baya, wato tana tsakanin shekaru 9 zuwa 11, yayin da ashi kuma namiji zai zamto bayan yaba shekaru 9 baya amma bai kai 14 ba. In kun lura kenan shekaru ne suka bambanta amma duk alamun daya ne.

Shi ma wannan waccan matsalar ta tangardar halittar da nace itace de kan taka rawa wajen faruwarta anan ma. 

Toh Saidai Anan Sauran Abubuwa Da Dama Da Akan Alaƙanta Faruwar Hakan Dasu Sune: 
  • Hutun rayuwa da samarwa yaro abunda duk ya nema ko bai nema ba naci ko sha, batare da ana sashi yana motsa jiki ba
  • Ciye-ciyen abinci marasa kyawu ga jiki wato junks foods; irinsu pizza,samosa,burger, dognut da sauran abubuwan zaƙi da maiƙo batare da ana  motsa jiki ba yadda za’a konasu ba, da kuma yaran da ke yawan basu abincin waken suya suna ciki kullum-kullum saboda tasirin pyoestrogen dake kunshe ciki.
  • Da kuma samuwar sabbin hanyoyin girki da dumama abinci na zamani irinsu: ovun, teflone cookwares, nonstick wrappers, chemicals da ake amfani dasu wajen gine-ginen zamani da fenti, rashin kwanciya bacci da wuri ga yaro abarsa yaita kalle-kallen tv ko video game dade sauran abubuwa wanda mukan iya ci, shaƙa ta iska ko sawa afatar jikinsu cikin kayayyakin kwalliyar da ake shafawa yara,
  • Da kuma karikitai da iyaye mata suka duƙufa amfani dasu da sunan karin ni’ima ajika da sassake-sassake na herbal concussion wanda mata basa fasawa koda suna dauke da juna biyu… wanda wani abun na rashin kan gado sai ciki ya samu ma ake farwa… wanda yawanci wannan abubuwan suna da abunda ake kira TERATOGENIC EFFCTS domin suna iya kutsawa shiga mahaifarki inda jariri ke kwance su barshi da illah. 

Shyasa zakuga ko maganin asibiti in mace nada ciki bakowanne aka yadda tasha ba.  

Shi yasa ko yaushe nakance mutane susan abu kafin kasa shi jikinka ko cikinka, bawai kurum don kaga kowa nayi ba. Wani zaiji asama na ambaci hadda madarar waken suya ko irinsu awara yai mamaki…. 

Kya iya kita bawa yarki kuma Allah yasa hakan bai faru ba wannan kuma ya danganta da yadda jikin kowa ke maida martanin abu, domin akwai wanda jikinsa ko ya yaji bakon abu zai canza. 

Babban misali allurar Kulorokuin ai ba kowa take sawa kaikayi ajika yaita susa ba, wani ko nawa akai lfy zai zauna, wani ko babu lafiya in akai masa, 

Haka wani zai iya cin gyaɗa ya kwana lafiya wani ko inyaci sai makabarta inbai sami tallafi ba saboda Allergic reaction ko borin jini, wani zaisha ruwan sanyi lafiya, wani inyasha ba lafiya sai tari da mura… zaman lafiya ya kiyayesu, toh haka abun yake.

Toh duk wadancan canje-canjen bai dace ace sun faru ba kafin kaiwa shekarun da aka saba ganinsu. 

Domin Mu A Lafiyance Kuma Kimiyance

Abunda aka saba gani shine; fara bayyanar tasowar nonuwa tsakanin shekaru 11 da haihuwa, da kuma soma haila tsakanin shekara 12 zuwa 14 yawanci a ýaýa mata. kadan ke kaiwa 15 zuwa 16 kafin fara haila.

Yayin da duk macen da takai shekaru 16 bayan bayyanar nonuwa batare da ta fara ganin haila ba hakan na nuna akwai matsala, ko kuma akaga takai har 15 babu bayyanar nono babu kuma haila… nan ma kwai matsala, kwai buƙatar atuntubi likita.

Amma ganin yarinya da nonuwa tundaga shekaru 11 wannan duk normal ne saide ace ya dan yi wuri. Wasu ma nonuwan na jinkirin tasawa har sai sun rufe shekara 20 alhalin suna haila, suna da gashi a lokunan jikinsu normal amma kirjin ne kamar anjera kwai wannan ma babu abun damuwa galibi.

Menene Illar Hakan

Idan alamun firikoshuyos ya bayyana toh babban mahimmin abun sani shine; Irinn wadannan yaran (Mace ko Namiji) kasusuwansu zasuyi saurin kammala ƙwarinsu tun kafin lokaci yayi wanda hakan ke nuna bazasuyi tsayi ba kamar sauran,mafi yawan mutane matukar ba’a kai musu dauki ba, basa wuce tsayin kafa hudu da ďan wani abu.

Haka zalik irin wadannan yaran ka iya fuskantar ciwo na rushi saboda damuwa, musamman wasu inba iyaye sun tsaya tsaye ba yan uwansu yara ka iya  tsokanarsu ko yi musu wasan banza

Matakin Dauka
  • Da farko dai in anga haka ya dace dukkan iyaye da manya agida su fahimci cewa wannan tangarda ce, a taimaka asami lokaci akaisu suga likitan yara wato PEDIATRICIAN a babban asibiti, yayin da likitan yara zai aiki hannu da hannu da likitan sinadaran jiki ENDOCRINOLOGIST wanda dukkansu ana iya samunsu ne a manyan asibitoci wato SPECIALIST, FMC, ko TEACHING HOSPITAL ko kuma asibitocin yaran ma kai tsaye wato PEDIATRIC HOSPITAL
  • Kada iyaye su jahilci wannan al’amari akai ga ganganci cewa za’a cirewa yarinya nonuwa… ko za’a nemo wani mai maganin hausa ko wanzami ya tsagasu a zare… kul don ya rasulillahi musamman iyayen mu na karkara kar ai haka, karma afara irin wannan mugun tunanin,shyasa nake sadaukar da lokacina domin wayar dakai,kusani wajibi ne kanku basai ma’aikacin lafiya ba in kunji ana shirin yiwa irin wadannan yara aika-aika ku tsawatar inkunga da gaske iyayen sunƙi daukar shawara don Allah kaje ka sanar da wani babba agari, ko kuwa jami’an tsaro don tsawatarwa…
  • Kada atsaya baiwa yaran wasu jike-jike ko magungunan shafawa a nonon… Sam babu bukatar haka.
  • Azo ga likitoci kurum, inma a asibitocin karkara ka sami irin wannan case din ka sanar dasu cewa in wannan abune da kunsan yana faruwa amma suyi kokari ga irin asibitin da zasuje kuma za’ai abunda ya dace. Aita wayarma da mutanen mu, saboda yanzu matsalar ta fara yawaita…. kuma hakan bai rasa nasaba da duniyar shaye-shayen tarkacen komi da komi da mata suka dorawa kansu… Domin hatta irin su hulba din nan da kuke rainawa a likitance munsan kwai estrogen cikinta… bai kamata mace me ciki ta rika ta’ammali dasu ba. 
  • In anzo asibiti likitoci zasu bada maganin da zai dakile cigaban saurin alamun balagar… tare da bata maganin da zai hana kasusuwan saurin kwari domin su samu su cimma tsayinsu kamar sauran mutane.
  • A sanya ido akan abokan wasa tare da  mutane daga irin wadannan yaran don tseratar dasu daga tsokana ko cin zarafin mutanen banza cikin al’umma, domin da za’a sadu dasu zasu dau ciki kai tsaye, koda jaririya ce kuwa ta sami wannan yanayin inda za saka mata ruwan halittar namiji ciki zai iya shiga bare wanda suka tasa.

Dmin karanta Amfani da Kuma Illar Magungunan Kara Karfin Maza (Male Sex Enhancement Supplements ) Danna nan

labarin da ya wuceAmfani da Kuma Illar Magungunan Kara Karfin Maza (Male Sex Enhancement Supplements )
Labarin na GabaCiwon Ciki (Stomach Pain) Da Yadda Za A Magancesa