Fitsarin jini alamace dake nuni da cututtuka na mafitsara abune wanda mutun yakamata yadamu sosai matuka
Menene Yake Kawo Fitsarin Jini?
- Sanyin mafitsara
- Sanyin Koda
- Duwatsun Koda
- Rauni a Koda
- Ciwon BPH
- Kansar mafitsara ko Koda
- Cututtukan jini
- Magunguna kamar magungunan Kansa ko penicillin
- Tsargiya
Sanyin Mafitsara:
sanyin mafitsara sanyi ne dake shafar mafitsararka,idan kana dashi,toh zaka runka yawan fita fitsari akoda yaushe musamman da daddare(sau biyu zuwa uku).
Domin sanin menene Ciwon Suga.(Diabetes) Shiga nan
Alamominsa Sun Hada Da:
- Yawan fitsari
- Tashi da daddare yin fitsari (tashi cikin dare sama da sau biyu)
- Jin zafi lokacin yin fitsari
- Ganin jini acikin fitsari
- Ciwon gefen ciki bayan ciwon mara
Mutun na kamuwa da sanyin mafitsara alokacin da aka samu kumburi ko kwayar cuta tashiga cikin mafitsara, mata sunfi saurin kamuwa da wannan ciwo akan maza.
Hakazalika masu ciki da wanda al’adar su ta dauke suna da saurin yiwuwar kamuwa da wannan ciwo.
Sanyin Koda:
Sanyi ne na koda (infection) yana faruwa ne alokacin da kwayar cutar bacteria tashiga cikin koda yakanzo da wadannan alamomi bayan ciwon ciki daga gefe:
- Ciwon baya
- Rashin son cin abinci (anorexia),
- Amai ko tashin zuciya
- Zazzabi.
- Yawan fitsari ko zafin fitsari
Duwatsun Koda:
Duwatsun koda na daga cikin cututtukan dake kawo fitsarin jini, wadannan duwatsu dai wadansu duwatsu ne dake fitowa a koda daga daskarewar datti da gishiri dake cikin kodar.
Alamomin Sa Sun Kunshi:
- Yawan fitsari
- Azababban ciwon mara
- Ciwo a gefen mara wanda yake zuwa har cinya
- Rashin iyayin fitsari
Rauni A Koda:
A lokacin da mutun yayi rauni a koda ta hanyar faduwa, buguwa,hatsari,yakan fuskanci wannan matsala ta fitsarin jini har sai wannan rauni ya warke.
Ciwon BPH
Wannan ciwo ne da mutun ke samunsa a lokacin da ‘prostrate dinsa’ (prostrate shike samar wa sperm cells sinadaran dasuke bukata wajen gudanar da aikinsu ajiki) ya kumbura,mutun kan iya kamuwa dashi alokacin da ya haura shekaru 50.
Alamomin Sa Sun Kunshi:
- Yawan fita fitsari da rana da dare
- Jin azababban matsin fitsari
- Rashin iya rike fitsari
- Jin wahala idan akazoyin fitsari
- Fitowar fitsari da kyar
- Jin raguwar fitsari acikin mara
Kansar Mafitsara Ko Koda
Kansar mafitsara ko koda kan sa mutun yayita fitsarin jini.
Alamomin Ta Sun Kunshi:
- Zafin fitsari
- Yawan fita fitsari
- Kumburin mara ko gefen ciki
- Rama
- Rashin san cin abinci
- Konewar jini
- Haki
- Ciwon baya da sauransu.
Tsargiya.
Tsargiya na daga cikin abubuwan dake kawo fitsarin jini,ana kamuwa da itane a lokacin da mutun yake yawan wanka a cikin kududdubi ko kogi.bayan fitsarin jini takanzo da alamomi irin na sanyin mafitsara
Yana dakyau ku karanta wannan Yan Mata Masu Shirin Yin Aure Da Amare Da Kuma Masu Sabon Ciki Karkuga Kamar Na Takura Muku Da Maganar Folic Acid
Maganin Fitsarin Jini
Abu mafi muhimmanci shine aje asibiti domin samun kulawa ta musamman daga kwararru,magani ya danganta da abubuwan dake kawo fitsarin jinin binciken da za ayi maka a asibiti dan gano asalin meke saka fitsarin jini.
- Gwajin fitsari
- Hoton mafitsara da Koda
- Gwajin jini
Amafi lokuta abubuwan dake kawo fitsarin jini suna bukatar a kwantar a asibiti domin yin cikakken magani.
Fitsarin jini ba abubane wanda zakayi wasa dashi ko ka tsaya karbe karben magungunan gargajiya, ab,un daya fi dacewa shine aje asibiti a ga likita.
Domin karanta bayani akan Cutar Mafitsara (UTI) Danna nan
[…] Yana dakyau ka karanta bayani akan Fitsarin Jini (BLOOD IN UTRINE) […]