Bayani Akan Tsarin Abinci Ga Masu Ciwon Suga (Diabetes Mellitus)

0
45

Tsarin abinci na da matuƙar muhimmanci ga masu ciwon suga domin kusan kimanin kaso 50 cikin 100 na masu ciwon suga tsarin abincine yake shawo kan matsalarsu fiye da amfani da magungunan rage suga a cikin jini da kuma amfani da allurar sinadarin insulin,abincin da muke magana anan ya hada da duka nau’ikan abinci masu ƙwaya, ganyayyaki, ‘ya’yan itatuwa da kuma dangin abinci masu maiko da kuma gina jiki

Wadanan nau’ikan abincin ana amfani da sune daidai da buƙatar jikin dan-Adam, da yawa daga cikin wadannan nau’ikan abincin suna aiki kaitsaye ga masu ciwon suga nau’i na biyu idan har sun kasance bisa tsari kuma suna taimakawa wajen rage yawan sugan dake cikin jininsu da kuma hana afkuwar wasu jinyoyin da ciwon ke kaiwa zuwa garesu irinsu ciwon koda, gushewar tunani da kuma bugawar zuciya wanda ke haifar da yawan mace-macen da yakai kaso 70-80 cikin 100 na masu ciwon suga. 

Muhimman Dankokin Abincin Da Ake Tsarawa Masu Ciwon Suga 

Kabohaidret (Carbohydrates)

Kusan kaso 80 cikin 100 na nau’inkan abincin da muka fiya ci a kasarnan karbohidrat ne shi kuma karbohidrat shine nau’in abincin da yake dauke da kaso mafi yawa na suga da jikinmu yake sarrafashi zuwa gulukos dan yai aiki dashi a matsayin makamashi, yawan wannan sinadarin acikin jini shike haifar da ciwon suga, akalla kaso 45-65 na karbohidrat a jikin mutum ne ke samar da karfi, mafi yawanci ana samun kabohaidret a nau’lkan abinci masu ‘kwaya, kayan marmari da kuma ‘ya’yan itatuwa. 

Karanta cikekken bayani akan menene Nausea (Tashin Zuciya)

Karbohidrat Nau’i Biyu Ne:
  • Wanda yake ƙunshe da sinadarin suga da yawa a cikinsa da aka sarrafa a inji da ake kira da (refined/simple carbohydrates), sarrafashi da a kayi yasa ya zama an samu raguwar wasu sinadarai masu amfani ga jiki irinsu fat, furotin da kuma faiba da suke taimakawa jiki wajen rage zu’kar suga hakan yasa ake samun taruwar suga sosai a cikin jikin mutum, masu ciwon suga nau’i na biyu ba’a yadda su na amfani da irin wannan nau’in na kabohaidret ba a abincisu.
  • Wanda yake da karancin sinadarin suga a cikinsa wato (complex carbohydrates), shi kuma yana kunshe da sinadaran fat, furotin da kuma faiba a cikin sa wanda suke taimakawa jiki wajen rage zu’kar suga, samuwar wadannan sinadaran zaisa sugan dake cikin jini yayi dadai da buƙatar jikin mutum, irin wannan nau’in na kabohaidret aka yadda masu ciwon suga nau’i na biyu su dinga amfani dashi a nau’ikan abincisu. Abin nufi anan shine masu ciwon suga zasu rage cin abincin da yake da karbohidrat sosai aciki sukoma amfani da wanda yake da ‘karancin karbohidrat a ciki.
Fat da Furotin (Fat And Proteins)

Wadanan sune dangin nau’ikan abinci masu mai’ko da kuma gina jiki, a’kalla kusan kaso 36-40 cikin 100 na abinci me mai’ko ke samar da ‘karfi ga jiki, bisa la’akari dashi mai’kon (fat) akwai wanda yake kasancewa daidai da buƙatar jiki dakuma wanda yake haifarwa da jikin mutum matsala wajen ƙara yawan sinadarin kwalesterol a jiki wanda yawansa ga mai ciwon suga ke haifar da ‘bullar cututtukan zuciya, sabo da haka yasa a keso masu ciwon suga dasu rage cin abinci me mai’ko sosai, su kuma dinga cin nau’inkan abincin da suke gina jiki wato furotin wanda yawansa yakai kimanin 0.6g/kg a kullum.

Domin karanta bayani akan Bayayanar Nau’in Abinci Mai Gina Jiki A Cikin Fitsare (Proteinuria) Danna nan 

Faiba (Fibre)

Faiba bagarene na kabohaidret kuma daya daga cikin nau’ikan abincin da ba’a iya narkawa a ciki, ana samun faiba a ganyayyaki, ‘ya’yan itatuwa da kuma abubuwa masu Ƙwaya, wannan nau’in na abinci na taimakawa masu ciwon suga musamman masu nau’i na biyu na ciwon ta hanyar rage saurin tafiyar suga yayin da ake zukeshi zuwa sassan jikin dake bukatar suga, a kullum ana bukatar ayi amfani da a kalla giram 30-38 na faiba.

Jerin sunayen ire-iren abincin da suka hada wadancan dangogin abincin da muka ambata da ya kamata masu ciwon suga su dinga ci

  • Naman kaza
  • Kwai
  • Kifi sadin
  • Soyayyiyar gyada
  • Goruba da aduwa
  • Rake
  • Lemo
  • Kankana da karas
  • Kayan ganye irinsu salak, kabeji dasuransu
  • Abinci mai ƙwaya irinsu wake, alkama da waken suya
  • Mai irinsu man zaitun
  • Albasa
  • Tafarnuwa
  • Tumatiri da kuma dankali
  • Biredi
  • Gurasa
  • Taliya da aka sarrafa da alkama
  • Sugan da aka yi shi don masu ciwon suga irinsu Aspartame
  • Kayan gwangwani da ba’asa suga a cikiba irinsu madarar waken suya, lemo ko ‘ya’yan itace da aka tace na roba, kwalba ko gwangwani
Jerin Sunayen Abincin Da Masu Ciwon Suga Zasu Nisanta
  • Farin sugar
  • Farar shinkafa
  • Farar taliya da kuma biredin da aka yi shi bada alkama ba
  • Shan kankana da abarba mai yawa
  • Kayan ci da sha na kwalba, roba ko gwangwani da akasa suga aciki
  • Cin gishirin da yawansa ya wuce miligiram 2300 a rana
  • Shan giya
  • Fulawa wacca ba ta alkama ba
Illar Yawan Cin Abinci Ga Masu Ciwon Suga Da Kuma Wanda Basu Dashi

Cin abinci fiye da kima na bawa jikin dan-Adam wahala wajen sarrafa abinci da kuma daukar abubuwa masu amfani a cikin abincin zuwa inda yadace, sakamakon yawan hidama da ake ba saifa da kuma sinadarin insulin wanda hakan ke haifar da barna mai yawa cikin jikin dan-adam, amma idan mutum ya lazamci cin abinci dai-dai kima, to zai taimakawa kansa wajen daidai ta sinadarin suga a cikin jininsa sannan kuma zai taimakawa sinadarin insulin dinsa yayi aiki cikin sauki, shi yasa wash masana ganin cewa yana da kyau ace masu ciwon suga sudinga yin azumi na sa’oi 5-8 a’kalla sau biyu a mako domin daidai tuwar suga a cikin jini. 

Dayawa masu ciwon suga na shan wuya a karon farko kafin su saba da tsarin canjin abinci, a har kullum abin da ake bukata a garesu shine juriya da mantawa da yanayin tsarin rayuwarsu ta baya, sannu a hankali abinda duk mutum ya sa a gabansa to zai cimma burinsa idan ya jure. 

Karanta cikekken bayani akan menene Nausea (Tashin Zuciya)

labarin da ya wuceMedical Check-Up
Labarin na GabaTsarin Iyali { Family Planning) Rubutu Na (2) (Intrauterine Device