Maganin Mallaka

0
28

Kamar yadda kowa yake fafutukar neman maganin farin jini, haka kuma ake ta faman neman maganin mallaka, mace tana so ta mallake mijinta, shi ma yana so ya mallake ta, abokan ciniki kowa so yake ya mallake abokin huldarsa. 

Garin neman buƙatar waɗansu, har shirka su ke yi. To ɗan uwa ga maganin mallaka a taƙaice: 

  1. Ka guji musu da jayayya da mutane. 
  2. Ka girmama ra’ayin mutane da fahimtarsa, ka da ka ƙaryata kowa, ka da ka yawaita bayyana kura-kuran mutane. 
  3. Idan ka yi kuskure ka yarda ka yi. 
  4. Kasance mai sauƙin kai, ka bar fushi da tsananta wa mutane. 5. Yi ƙoƙari ka toshe duk wata kafar sabani tsakaninka da mutane. 6. Ka da ka ba da umarni kai tsaye, a a yi umarni a fakaice, kamar “don Allah miƙo min” ko kana da lokaci ka raka ni da sauran su. 
  5. Idan za ka ba da umarni ka fara da godiya da yabo. 
  6. Ka ganar da mutum kuskurensa a fakaice. 
  7. Kafin ka faɗi kuskuren mutum, ka yi shimfiɗa da fara faɗar naka kuskuren, ka yarda kai ma mai kuskure ne. 
  8. Yayin jayayya, ka ba da dama ga mutum ya kare kansa. 
  9. Ka tabbatarwa da mutum kan amfanin aikin da kake so ya aikata. 12. Kasance mai sauƙin kai da ƙaskantar da kai. 

Ɗan uwa waɗannan ƙa’idoji in ka bi su, za ka mallaki kowa ba tare da ka ɓata masa ba, kuma cikin sauƙi da raha. Sai fa an gwada akan san na ƙwarai. A nan zan dakata, da fatan Allah ya ba mu zaman lafiya da kwanciyar hankali a duniya da Lahira. Amın summa Amin.

Domin Karanta Cikekken Littafin Danna nan

labarin da ya wuceMaganin Farin Jini
Labarin na GabaSahihin Sirrin Iza Ja’a