Sahihin Sirrin Iza Ja’a

0
27

Iza ja’a (Suratun Nasri), ita ce sura ta (110) a jerin surorin Alƙur’ani mai girma guda ɗari da sha huɗu (114), kuma tana ɗaya daga cikin surorin da aka saukar a Madina, sannan kuma ayoyinta uku ne. Ga su kamar haka: 

Da sunan Allah mai rahama mai jin ƙai: 

Idan taimakon Allah da buɗi ya zo(1) 

Kuma ka ga mutane suna shiga Addinin Allah jama’a – jama’a(2) 

To ka yi tasbihi da godiyar Ubangijinka, kuma ka nemi gafararsa, haƙiƙa shi mai yawan karɓar tuba ne(3). 

Wannan sura ta zo wa da Manzon Allah (Sallallahu Alaihi Wasallam) da albishir ɗin samun taimakon Allah da buɗi a kan abokan gabarsa. 

Haka aka yi Musulunci ya yaɗu aka rinjayi kafirci da kafirai. 

Domin karanta Neman Aure Bisa Koyarwar Musulunci Danna nan

Bayan haka, wannan sura ta tabbatar wa da Manzon Allah (Sallallahu Alaihi Wasallam) cewa, aikin da aka aiko shi yi na isar da saƙon Musulunci ya kammala ya cika, kuma lokacin komawarsa ga Ubangijinsa ya ƙarato. 

Sannan kuma wannan sura ta koyar da Musulmai lazimtar tasbihi da godewa Allah tare da neman gafararsa, musamman wanda shekarunsa suka yi nisa, lokacin komawarsa ga Ubangijinsa ya kusanto. Ƙari akan haka, ga mai son ya sami buɗi da taimakon Allah (Subahanahu Wata’ala) to ya tsayu da taimakon Addinin Allah. 

Waɗannan saƙonni su ne sahihan sirrin surar: “Iza Ja’a”. Kuma duk Musulmin da ya tsayu da abubuwan da ta koyar ya kuɓuta ya tsira duniya da lahira.

Bayan haka, daidai ne ga wanda ya karanta wannan sura yana iya raka ta da yin addu’a akan buƙatarsa; tare da neman taimakon Allah da samun buɗi cikin al’amuransa na alheri da ya sa a gaba. Saboda yin hakan tawassuli ne da zancen Allah (Subahanahu Wata’ala) wannan ke nan. 

Sannan kuma babu wani sahihin dalili da ya zo da cewa a yi salla raka’a kaza, da Iza ja’a ɗari kaza, har tsawon wata kaza, ko kwana kaza, domin cimma wata buƙata ta musamman. 

Domin Karanta Cikakken Bayanin Abubuwan Da Sai Da Su Aure Yake Zama Karɓaɓɓe Danna Nan

Haka kuma cewa a rubuta Iza ja’a sau ɗari kaza, ko kwana kaza,don samun biyan wata buƙata, ba shi da asali sahihi a Musulunci. 

Bayan haka, buɗa wani baƙi (harafi) daga cikin baƙaƙen wata sura, ko aya ta Alƙur’ani a rubuta wani abu can daban a cikinsa, ko kuma a cire wa aya ɗige-ɗigenta, canja zancen Allah ne daga yadda yake, don haka yin hakan haramun ne, kuma ba a neman biyan buƙata da haramun. 

Ya Allah ka tsare mu keta alfarmar littafinka don neman wata biyan buƙata. Amin. 

Kuma Manzon Allah (Sallallahu Alaihi Wasallam) ya ce: “Wanda ya aikata wani aiki a shari’a ba tare da umarninmu ba, ba a karɓi aikin ba.”Muslim ne ya rawaito shi. 

Sannan kuma batun sai an haɗa Iza ja’a da kurman goro, ko saiwar rimi, ko ruwan tsohuwar rijiya, ko ƙasar ƙofar Masallacin Juma’a, ko wanin waɗannan, sannan a ga tasirin Iza ja’a kan samun biyan wata buƙata, shaci-faɗi ne da kuma kundin ka. 

Allah ka tsare mu da bin hanyar shaiɗan. Amin!

Domin Karanta Cikekken Littafin Danna nan

labarin da ya wuceMaganin Mallaka
Labarin na GabaHukuncin Kallon Talabijin Da Fina-Finai