Author: Sanusi Iguda

  • Tarihin Malam Ɗankwandarai

    Tarihin Malam Ɗankwandarai

    An haifi Malam Isa Ɗankwandarai a garin Sankara a Ƙauyen Kwandarai. Ya yi tafiye-tafiyen neman karatu har Ubangji Maɗaukakin Sarki Ya hore masa Alƙur’ani; kuma ya yi fice tsakanin makaranta a wannan fage.

    Ya je ƙasar Bima neman karatu har ya kwashe wani lokaci a can. A lokacin da shahararren masanin Alƙur’ani nan Gwani Hamad ya bayyana a birnin Kano; Malam Isa Ɗankwadarai na cikin malaman da suka zama almajiran sahun gaba a wurinsa.

    Wannan ya sa shi yin fice a fagen karatun Alƙur’ani bisa ƙa’i’doji karatu da ilimi Tajwidi har sai da mahaddata suka riƙa zuwa gari da gari don naƙaltar wan nan ilmi a wurinsa.

    Malam Ɗankwandarai ya shahara wajen sanin girman malamai, domin shi ne ya yi wa Gwani Hamad kyautar doki da kayan abinci da sauran hidima akai-akai har sai da ya samu matsayi a wurinsa Ya kasance mutum ne mai taushin hali, ba ya fushi, ga yawan ciyarwa ga almajirai. Ya kasance yana yawan yiwa ‘ya’yansa da almajiransa wasiyya da riƙe Alƙur’ani.

    Saboda kyakkyawar dangantakar sarakuna da makaranta Alƙur’ani kuwa an ce Sarki Sunusi ne ya dawo da shi Kano; ya ba shi wuri don ya gina tsangayarsa.

    Cikin manyan almajiransa akwai Gwani Ɗanbirni da Gwani Saleh Ɗanzarga Ya rasu a zamanin mulkin Sarkin Kano Ado Bayero a shekara ta 1984.

    Domin karanta cikakken bayani a kan Tarihin Gwani Ɗanbirni danna nan.

    Domin karanta cikakken bayani a kan Taƙaitaccen Tarihin Kamilu Almajirin Mawaƙa danna nan.

    Wannan bayanin an ciro shi ne daga Littafin Tsarin Tsangayun Alƙur’ani A Arewacin Najeriya; Tarihin Su Da Zamantakewar Su Da Hanyoyin Raya Su wanda Dr. Sunusi Iguda Ƙ/Nasarawa ya wallafa shi; domin karanta cikakken Littafin danna nan.

  • Tarihin Malam Attahiru Shehu Na Liman (Limamin Masallacin Shehu)

    Tarihin Malam Attahiru Shehu Na Liman (Limamin Masallacin Shehu)

    An haifi Malam Attahiru a farko-farkon sarautar sarkin musulmi Abubakar na uku. Malam Attahiru ya taso cikin tarbiyyar addini wurin mahaifinsa.

    Kasancewar gidansu gida ne na ilmi da yaɗa shi, ya sa shi gadar wannnan sana’a ta koyar da Alƙur’ani da ilmi. Duk da cewa a halin yanzu Malam Attahiru shi ne Limamin Masallacin Shehu da ke Sakkwato, duk da haka makarantarsa ba ta gushe ba ta na yaɗa addini a cikin garin Sakkwato tare da taimakon ‘yan uwansa musamman ma Malam Abubukar da Malam Ibrahim da Malam AbdurRahman da Malam Ahmad Zaruƙu.

    Malam Attahiru Na Liman tsatson Alƙali Abubakar Ladan Rame ne, wanda ɗan Gwaggon Shehu Usmanu Ɗan Fodiyo ne. Wannan zuriya mai albarka ta cigaba da jiɓintar koyar da addini da alƙalanci har zuwa kan Malam Attahiru Shehu Na Liman (Limamin Masallacin Shehu da ke Sakkwato na yanzu).

    Domin karanta cikakken bayani a kan Tarihin Malam Buhari Siriddawa (Sarkin Malaman Sakkwato) danna nan.

    Domin karanta cikakken bayani a kan Falalar Adalci, Tausayawa Mabiya Da Illolin Gallaza Musu danna nan.

    Wannan bayanin an ciro shi ne daga Littafin Tsarin Tsangayun Alƙur’ani A Arewacin Najeriya; Tarihin Su Da Zamantakewar Su Da Hanyoyin Raya Su wanda Dr. Sunusi Iguda Ƙ/Nasarawa ya wallafa shi; domin karanta cikakken Littafin danna nan.

  • Tarihin Alaramma Malam Salihu Ɗangalinja

    Tarihin Alaramma Malam Salihu Ɗangalinja

    An haifi Malam Salihu ɗan Dawuda a girin Galinja da ke Kanon Dabo a shekarar 1920 zamanin Sarkin Kano Usman. Mashahurin mahaddaci mai baiwar tilawa da kaifin basira.

    Malam Salihu Ɗangalinja ya yi tafiye-tafiyen neman karatu cikin ƙasar Gumel da Haɗeja; da garuruwa irin su Mainabindi da Kalali da Unguwar Jibrin.

    Bayan Malam Ɗan Galinja ya samu AIƙur’ani, sai kuma ya tsunduma cikin fannonin ilmin Fiƙhu da tajwidi. Ya karanta littafai irinsu Hidayatul Rahman wajen malaminsa Shehu Rabi’u Ɗantinki da Malam Husaini Gwauron Dutse. Saboda irin baiwarsa ta karatu an ce a lokacin ƙuruciyarsa zai yi wuya a lissafa manyan tsangayun da ya je ya sha fari ya tashi; Wannan ya sa sa’o’insa su ka sallama masa.

    Malam Salihu mutum ne mai yawan haƙuri da kawaici da kyautatawa ga almajiransa. Bayan girma ya kama shi sai ya kafa tsangayarsa da ke garin Ƙarfi a inda makaranta ke turuwa don sanin Alƙur’ani daga gare shi. Wadda hakan ya canza yanayin rayuwar mutanen Ƙarfi saboda maƙwabtakar da suka yi da ma’abota Alƙur’ani.

    Malam Salihu Ɗan Galinja ya kasance yana yi wa ‘ya’yansa da almajiransa wasiya da riƙo da Alƙur’ani da kaucewa kwaɗayin duniya.

    Malam Salihu ya rasu a shekarar 1997 ya bar ‘ya’ya da dama, kaɗan daga cikin mazan su ne:-

    • Halifansa Malam Kabir Ɗan Galinja
    • Malam Nafiu Ɗan Galinja
    • Malam Ɗahiru Ɗan Galinja, da ‘ya’ya mata guda tara.

    Domin karanta cikakken bayani a kan Tarihin Mahiru Sharif Bala danna nan.

    Wannan bayanin an ciro shi ne daga Littafin Tsarin Tsangayun Alƙu’ani A Arewacin Najeriya; Tarihin Su Da Zamantakewar Su Da Hanyoyin Raya Su; wanda Dr. Sunusi Iguda Ƙ/Nasarawa ya wallafa shi; domin karanta cikakken Littafin danna nan.

  • Tarihin Alaramma Malam Salisu Ɗanruwantsa

    Tarihin Alaramma Malam Salisu Ɗanruwantsa

    An haifi Alaramma Malam Salisu ɗan Malam Ahmad ɗan Usmanu ɗan Ahmad a garin Ruwantsa. An ce asalin zuriyarsu sun fito daga ƙasar Mali, Alaramma Malam Salisu ya taso a garin Ruwantsa a inda ya fara karatu a wurin Malam Abdul’Aziz ɗan Malam Ibrahim.

    Lokacin da ya ƙara datawa kuma idonsa ya yi ƙwari, sai tsananin kwaɗayinsa ga Alƙur’ani ya ƙaru, ya ƙara duƙufa. Malam Salisu ya kasance tun ƙuruciyarsa ba ya zama wuri guda face yana tsakanin wancan gari da waccan tsangaya izuwa waccan cibiya ta makaranta. Wannan ya ba shi damar huɗuwa da gwarazan malaman zamaninsa irin su Malam Haruna Ningi wanda a wurinsa ne ya haddace AIƙur’ani Mai Girma.

    Koda Alaramma Malam Salisu ya sami labarin bayyanar Gwani Hamad a garin Taura kuwa; sai ya zabura ya haɗa kayansa ya nufe shi kuma ya kamfata daga marmaron ilmin Gwani Hamad. Daga nan kuma ya wuce garin Malamawa wurin Bajimin malami Malam Abdullahi. Malam Sal ısu bai gushe ba yana kutsawa cikin kowane loko da saƙo na ƙasar Kano da kewayenta; har sai da ya dangana da garin Insharuwa cikin Jamhuriyar Nijar.

    Bayan Dawowar Malam Salisu daga ƙasar Nijar ne ya yi aure a mahaifarsa. Daga nan ne ya taso tare da Wani adadi na almajiransa ya dawo Kano ya sauka Unguwar ƙofar Wambai; wurin Malam AbdulKarim inda ya karanta ilimin Tajwidi da Fiƙihu. Manyan malaman Malam Ɗanruwantsa sun haɗa da Shehin Malami Rabi’u Ɗantinki da Shehu Mai Hula. Bayan nan ne kuma ya sake zabura izuwa garin Ɗabbatta wurin babban malami Malam Adam; don sanin ilimi littafin Shaɗibiyya da ilmin Rasmu.

    Sannan ya sake dawowa birnin Kano karo na biyu a inda ya sauka a wurin Malam Garba Tudun Nufawa.

    Ya zauna shekaru biyu a wurinsa yan karantar Alfiyyar ɗan Malik. A lokaci guda kuma, shi Malam Garba Tudun Nufawa (Malam Abubakar Ramadan) yana koyon ilmin Tajwidi da Kira’o’i a wurinsa; Daga nan ne ya koma Unguwar Yakasai ya kafa makarantarsa a shekarar 1945.

    Bayan ya tumbatsa da ilmi da Alƙur’ani; daga bisani kuma ya koma Gwauron Dutse kusa da Masallacin Juma’a na Sheikh Is’haka Rabiu a matsayin Na’ibin Limamin Masallacin.

    A takaice dai zamu iya cewa Malam Salisu Ɗanruwantsa shi ne magajin kambin Shehi Rabiu Ɗantinki a fagen ilmin Alƙur’ani; da ƙira’o’i a faɗin Kanon Dabo. Tsangayarsa ta shahara da tsare-tsare masu ban sha’awa tare da sanya cigaban zamani a Wasu ɓangarori daban-daban. Alal misali, akwai tsarin azuzuwa inda ake sanya yara goma sha bakwai; a Kowane aji ana biya musu rabin sumuni da safe har sai sun haddace. Da yamma kuma a ƙara musu rabi don a samu kyakkyawar haddar AIƙur’ani.

    Domin karanta cikakken bayani a kan Tarihin Alaramma Gambon Takai danna nan.

    Wannan bayanin an ciro shi ne daga Littafin Tsarin Tsangayun Alƙu’ani A Arewacin Najeriya; Tarihin Su Da Zamantakewar Su Da Hanyoyin Raya Su; wanda Dr. Sunusi Iguda Ƙ/Nasarawa ya wallafa shi; domin karanta cikakken Littafin danna nan.

  • Tarihin Alaramma Malam Aliyu Ɗan Kadawa (1868-1998)

    Tarihin Alaramma Malam Aliyu Ɗan Kadawa (1868-1998)

    An haifi Malam Aliyu a zamanin Sarki Abdullahi a garin Kadawa cikin ƙaramar Hukumar Warawa da ke Jihar Kano. Hamshaƙin malamin Alƙur’ani, ma’abocin zaumunci da kyauta.

    Malam Aliyu ya yi tafiye-tafiye na neman Alƙur’ani har sai da ya dangana da ƙasar Maiduguri, baya ga lokacin da ya ɗauka yana gwagwarmayar neman karatu tsakanin Gaidam da Gayan da ke garin Haɗeja.

    An ce a lokacin da Turawa suka fara zuwa Kano, Malam Aliyu na rubuta AIƙur’aninsa na biyu. A lokacin kuwa da Gwani Hamad ya bayyana a birnin Kano. Malam Aliyu Ɗankadawa na daga cikin Gwanayen AIƙur’ani da suka sanya allo a gabansa don ɗosana daga hasken da Ubangiji Ya ba shi na ilmin tajwidi da ƙira’o’i.

    Saboda irin shaharar da Malam Aliyu ya yi wajen sada zumunci kuwa, ya kasance duk da girma ya kama shi; ya kan yi shiri wani lokaci ya yi tafiya mai nisa da ƙafa cikin wasu garuruwa don kai ziyara ga tsofaffin alarammomi abokan karatu tun lokacin ƙuruciya.

    Game da karamcinsa kuwa, ya lazimta wa ‘ya’yansa zuwa gidajen aminansa da ke kusa; domin gaishe su a kowace safiya da yi musu wasu ayyuka kafin ma su gaishe shi ya amsa. Alaramma Malam Aliyu ba ya shigar da wani abu na sadaka gidansa har sai ya rabar da shi ga almajransa. Almajiri ba ya samun fada a warin malam sai in kaɗai ya rungumi Alƙur’ani ka’ in da na’in.

    Game da baiwar Alƙur’ani da rubuta shi kuwa; Alaramma Malam Aliyu Ɗankadawa ya kasance hatta a lokacin tafiya ba ka rasa shi da kayan rubutun AIƙur’ani. Da ya samu wata dama ko yaya ta ke to, sai ya cigaba da rubuta Alƙur’ani abinsa. Da haka ya ribaci rayuwarsa ta hanyar amfanı da lokaci komai ƙan-ƙantarsa.

    Kaɗan daga cikin almajiransa sun haɗa da:-

    • Malam Yalwa
    • Malam Musa Gurgu Takai
    • Malam Abubakar
    • Malam Garba Kurna
    • Malam Rabi’u Gezawa
    • Malam Isa Ringim

    Ubangiji Maɗaukaki Ya yi wa Malam Aliyu Ɗankadawa tsawon rai don ya rasu a shekarar 1998 yana ɗan shekaru 130; ya bar ‘ya’yaye waɗan da suka haɗa da:-

    • Malam Ya’u
    • Malam Ɗayyabu
    • Malam Tasi’u da
    • Malam Haruna

    Domin karanta cikakken bayani a kan Tarihin Sheikh Malam Mahammad Ɗan Almajiri danna nan.

    Domin karanta cikakken bayani a kan Taƙaitaccen Tarihin Waƙafi A Musulunci danna nan.

    Wannan bayanin an ciro shi ne daga Littafin Tsarin Tsangayun Alƙur’ani A Arewacin Najeriya; Tarihin Su Da Zamantakewar Su Da Hanyoyin Raya Su wanda Dr. Sunusi Iguda Ƙ/Nasarawa ya wallafa shi; domin karanta cikakken Littafin danna nan.

  • Tarihin Shehun Malami Muhammad Rabi’u Ɗan Tinki (1897-1959)

    Tarihin Shehun Malami Muhammad Rabi’u Ɗan Tinki (1897-1959)

    Malam Rabi’u ɗan Yunusa ɗan Alhasan ɗan Baru. An haife shi a garin Tinki a cikin ƙaramar hukumar Bici da ke Jihar Kano cikin shekarar 1897.

    Malam Rabi’u ya taso ciki ƙuruciya manisanciyar wargi da wasanni irin na matasa. Ya yi karatu a gaban mahaifinsa. Muhammad Rabi’u Ɗan Tinki ya kasance mutum ne mai yawan haƙuri da kawaici da yawan sabo da jama’a. Ya haddace Alkur’ani tun yana ɗan shekara goma sha huɗu. Sannan ya fara karatun littatafai irin su Ahalari da lziyya.

    Daga nan ya nemi izinin muhaifinsa ya bi wani baƙon mashahurin malami da ake kira Malam Kunta. Bayan ya zauna tsawon lokaci a wurinsa, sai ya nemi izini zuwa wajen Mahiru Kalla mutumin Damagaram cikin Jamhuriyar Nijar.

    Ya zauna a wajensa tsahon lokaci har ya sauke litlatafai da yawa a fannin ilimin ƙira’a da Tawhid da litlafai irinsu Nuniyar Sakawiy da Hidayatussibiyan da Tuhfatul adfal da Mukaddimat Jazary, da Shadibiyya da Lamiyyatul Kira ‘at.

    Shaihun malamin bai gushe ba yana kutsawa cikin fagagen ilmai da gogayya da malamai har sai da ya dangana da garin Maiduguri ya yi karatu a wurin Mahiru Ahmad. Daga nan ya dawo Kano ya sauka Haɗejiya ya kara dukuta a gaban Malam Is’hak daga bisani ya dawo Kano ya cigaba da koyarwa.

    A lokacin da Malam Ɗantinki ya samu labarin Mahiru Hamid, sai ya nemi izinin ya zama almajirinsa. A nan ma ya karanta littafai da dama musamman fannin dabti wanda shi ma ɓangare ne na ilimin Rasmu da ilimin wasullan Alkur’ani.

    Abokan karatun Shehi Rabi’u wurin Gwani Hamid sun haɗa da Malam Ɗan Gunduwawa da Malam Aliyu Mai Kwaro da Malam Ɗan Karofin Yashi da Malam Yunus Ɗan Gumel da Malam Ɗan Kanuri da Malam Isah Ɗan Kwandarai da Malam Sabo Ƙofar Wambai da Malam Umar Ɗan Mai-Rigar-Fatu.

    A halin yanzu tsangayarsa ta cigaba da bunƙasa kuma ta yi rassa a hannun ɗan sa Halifa Sheikh Is’haka Rabi’u.

    Domin karanta cikakken bayani a kan Tarihin Gwani Saleh Danzargu danna nan.

    Domin karanta cikakken bayani a kan Taƙaitaccen Tarihin Samuwar Waƙoƙin Baka a Ƙasar Hausa danna nan.

    Wannan bayanin an ciro shi ne daga Littafin Tsarin Tsangayun Alƙur’ani A Arewacin Najeriya; Tarihin Su Da Zamantakewar Su Da Hanyoyin Raya Su wanda Dr. Sunusi Iguda Ƙ/Nasarawa ya wallafa shi; domin karanta cikakken Littafin danna nan.

  • Tarihin Gwani Saleh Ɗanzargu

    Tarihin Gwani Saleh Ɗanzargu

    An haifi Gwani Saleh ɗan Abdullahi jikan Abdullahi a Ƙasar Jahun. Mahaifin sa ya rasu yana ƙaramin yaro, don haka sai mahaifiyar sa ta koma da shi garin Zarga ta kuma kyautata tarbiyar sa.

    Gwani Saleh ya taso da kaifin basira da son Alƙur’ani. Don haka ya lazimci makarantan garin Zarga irinsu Malam Abdullahi har Ubangiji Ya hore masa Alƙur’ani ya haddace shi yana ɗan shekara tara (9). Gwanin Alƙur’ani ma’abocin ƙan-ƙan da kai da gaskiya da riƙon amana. An ce tun yana ɗan shekara sha biyu ya sha fari.

    Gwani Saleh ya yi tafiye-tafiye na neman karatu a inda yazo Kano ya sauka a tsangayar Gwani Nadudu. Daga bisani kuma ya lazimci mashahurin malami Malam Aliyu Basakkwace ya karanci Fiƙhu da Hadisi da tafsiri Shaharar da tsangayarsa ta yi ya sanya makaranta daga nisan duniya yin takakkiya don ɗosana daga haskenta. Manyan abokanen karatun Gwani Saleh sun haɗa da:-

    • Gwani ɗan Kwandarai
    • Gwani Ɗan birni
    • Gwani Daudu

    Game da yawan almajiran da suka samu Alƙur’ani a hannun sa kuwa, wannan ɗan littafi ba zai ɗauke ambaton su ba, sai dai mu yi ishara ga waɗansun su:

    • Malam Muktari Abdullahi
    • Yayan sa Gwani Yahuza da Gwani Lawi
    • Malam Husaini Rijiyar Lemo
    • Malam Sham’unu
    • Malam Ibrahim Maidarasu

    Gwani ya rayu cikin karamci da girmamawa daga maƙwabtan sa, musamman ma Alhaji Sunusi Ɗantata da al’umar Unguwar ƙoƙi da kewayenta. A halin yanzu wannan tsangaya tana ƙarƙashin kulawar ɗan sa Gwani Yahuza inda ta ƙara bunƙasa ta hanyar shigo da tsarin ilmin zamani, ɓangaren firamare da sakandare. A lokaci guda kuma, ga tsohon tsarin tsangaya na gudana da makaranta da mahaddata.

    Gwani Yahuza ya samu gogayya da wayewa ta zamani a inda ya dangana da ƙasar Masar don karatun sa na digirin farko. A halin yanzu Gwani Yahuza ɗaya ne daga manyan alƙalai na musabaƙar Alƙur’ani ta ƙasa. Gwani Yahuza shi ne ɗan Najeriya na farko da ya karɓi kyautar girmama mahaddata Alƙur’ani daga ƙasar Saudi Arebiya. Baya ga wannan rassa na makarantar akwai majalisai a unguwannin Gwammaja da Kurnar Asabe da Ƙoƙi.

    Ita wannan makaranta ta Gwammaja, Gwani Lawi ne ya kafa ta mai suna Ma’ahad Gwani Lawi Litahfizil Ƙur’anil Karim.

    Gwani Lawi ya yi babbar Diflomarsa a Jami’atul Ƙur’anil Karim da ke Sudan, kuma shi ne wan da ya kafa ƙungiyar Mahaddata Alƙur’ani ta farko a Najeriya, mai suna Rabiɗatul Huffazil Ƙur’ani, Nigeriya. Gwani Sale Ɗanzarga ya bar ‘ya’ya goma sha biyu, maza da mata.

    Domin karanta cikakken bayani a kan Tarihin Malam Ɗankwandarai danna nan.

    Domin karanta cikakken bayani a kan Tarihin Farko Na Nijeriya (1500 BC- 500 AD) danna nan.

    Wannan bayanin an ciro shi ne daga Littafin Tsarin Tsangayun Alƙur’ani A Arewacin Najeriya; Tarihin Su Da Zamantakewar Su Da Hanyoyin Raya Su wanda Dr. Sunusi Iguda Ƙ/Nasarawa ya wallafa shi; domin karanta cikakken Littafin danna nan.

  • Tarihin Sheikh Malam Muhammad Ɗan Almajiri

    Tarihin Sheikh Malam Muhammad Ɗan Almajiri

    An haifi babban malami Muhammad ɗan Malam Adamu a Ƙasar Kazaure. Malam Muhammad ɗan Almajiri ya fara karatu a gaban mahaifinsa Malam Adamu.

    Malam ya yi tafiye-tafiyen neman Alƙur’ani har sai da ya dangana da garin Bajanwa a ƙasar Katsina wajen Malam AbdusSamad a inda ya yi karatun Alƙur’ani wurinsa. Daga nan ne Malam AbdusSamad ya tafi da shi izuwa garin Rawayau wurin mashahurin malamin nan Malam Goji. Daga Rawayau, ya bazama izuwa Unguwar Ciranci cikin Birnin Katsina don ƙara gogewa da Alƙur’ani.

    Malam Ɗan Almajiri ya zo Kano a inda ya sauka a unguwar Fagge wajen babban malami Malam Ibrahim Badamagare a inda ya karanci fiƙhu da Nahwu. Malaman Sheikh Ɗan-almajiri a Kano sun haɗa da Malam tijjani Zangon Barebari. Malam ya rasu a shekarar 1960.

    Makarantar marigayi Ɗan Almajiri ta yi fice tsakanin makarantun Alƙur’ani da yawan almajirai da tsare-tsare masu ban sha’awa. Wan nan ya sa ta yi rassa da ɓangarori daban-dabun. An kafa wan nan makaranta ne a shekarar 1945.

    Almajiran Malam Ɗan-almajiri sun haɗa da Malam Ɗan-Inna da ‘ya’yansa. Malam ya rasu ya bar ‘ya’ya 14; bakwai maza bakwai mata. Bayan rasuwar sa sai Malam Haruna Rashid ya jiɓinci gudanar da ita kuma ta cigaba da bunƙasa a hannunsa da hannun wasu almajiransa musamman a wasu jihohi cikin tarayyar Nijeriya. Kaɗan daga rassan makarantar marigayi Malam Ɗan almajiri su ne:-

    – Makarantar Alƙur’ani da Islamiyya, Kaduna
    – Makarantar Alƙur’ani da Islamiyya, Katsina
    – Makarantar Alƙur’ani da Islamiyya, Bauchi
    – Makarantar Alƙur’ani da Islamiyya, Lagos

    Domin karanta cikakken bayani akan Tarihin Sheikh Is’haƙ Rabi’u Khadimul Alƙur’ani danna nan.

    Domin karanta cikakken bayani akan Asalin Sunan Ƙabilar Ƙuraish danna nan.

    Wannan bayanin anciro shi ne daga Littafin Tsarin Tsangayun Alƙu’ani A Arewacin Najeriya Tarihin Su Da Zamantakewar Su Da Hanyoyin Raya Su; wanda Dr. Sunusi Iguda Ƙ/Nasarawa ya wallafa shi; domin karanta cikakken Littafin danna nan.

  • Tarihin Gwani Daudu (1920-2000)

    Tarihin Gwani Daudu (1920-2000)

    An haifi Alaramma Malam Abubakar Yunusa a shekarar 1920 a garin Tsakuwawa a ƙaramar Hukumar Miga da ke cikin Jihar Jigawa. Ana yi masa laƙabi da Gwani Daudu saboda sarautar kakanninsa ta Galadiman garinsu.

    Alaramma Malam Abubakar ya shahara da baiwar karatu na yankan shakku. Saboda irin kaifin ƙwaƙwalwar da Ubangiji Maɗaukaki Ya ba shi, an ce Gwani Daudu ba ya manta duk abin da ya yi ido biyu da shi tun daga ƙuruciyarsa. Zarton malami, ma’abocin karamci da son almajirai. Gwani Daudu ya yi fice cikin dattijawan alarammomi da wayewa a zamanance da kuma kutsuwa fannonin ilmi Fiƙhu da Tafsir da Lugga da Nahwu.

    Gwani ya fita neman karatu bayan ya zama matashi mai kimanin shekaru goma sha biyar kuma bai koma gida ba sai da ya samu Alƙur’ani kuma ya rubuta shi. Ya yi tafiye-tafiyen neman karatu cikin Birniwa da Kirikasamma da Gayan. Gwani Daudu ya kafa tsangayun AIƙur’ani a birane daban-daban kamar garuruwan Mai Tafari da Kirikasamma da Kuka Uku.

    Don haka ne ma a halin yanzu ake kiran wata kasaitacciyar makaranta a garin Damaturu da tsangayar Gwani Daudu.

    Bayan Gwani Daudu ya dawo birnin Kano kuwa ya zauna a wurare daban-daban da suka haɗa da Durumin Zungura da Kankarofi cikin ƙaramar Hukumar Birni. Daga bisani kuma ya koma Unguwar Gwale.

    Gwani Daudu ya shahara da kyakkyawar maƙwabtaka da saraki da sauran al’umma. Saboda haka ne ma Sarkin Kano Ado Bayero ya ba shi filin da ya faɗaɗa tsangayarsa da ke Unguwar Gwale.

    Malaman Gwani Daudu sun haɗa da:-

    • Malam Mai Ɗanbahar Mai Tafari
    • Malam Iliya Gayan
    • Gwani Ɗankwandarai

    Gwani Daudu ya rasu a ranar 22 Sha’aban 1421, dai-dai da 17 ga Nuwambu 2000. Ya rasu ya bar ‘ya’ya da almajirai masu yawa:-

    ‘Ya’ya:

    • Malam Muhammad Abubakar
    • Malam Ahmad Abubakar
    • Malam Susi Abubakar
    • Malam Tamimuddari
    • Malam Adisaru
    • Malam Arisu

    Manyan Almajiransa sun haɗa da:-

    • Malam Ali Basukkwace
    • Malam Umar Panshekara
    • Malam Ahmad Ɗantsadawa
    • Alh. Hamza Yusuf
    • Malam Garba Na’ibi
    • Malam Muhammad Ɗan Meram

    Domin karanta cikakken bayani a kan Tarihin Alaramma Malam Isa ƊanƘauranmata Bin Umar danna nan.

    Domin karanta cikakken bayani a kan Misalan Waƙafi Ababen Koyi A Tarihin Musulunci danna nan.

    Wannan bayanin an ciro shi ne daga Littafin Tsarin Tsangayun Alƙu’ani A Arewacin Najeriya; Tarihin Su Da Zamantakewar Su Da Hanyoyin Raya Su; wanda Dr. Sunusi Iguda Ƙ/Nasarawa ya wallafa shi; domin karanta cikakken Littafin danna nan.

     

  • Misalan Malaman Yarabawa A Ƙarni Na Goma Sha Tara

    Misalan Malaman Yarabawa A Ƙarni Na Goma Sha Tara

    Malaman ƙarni na goma Sha Tara a ƙasashen Yarabawa sun haɗa da:

    • Sheikh Saleh bin Abdulƙadir
    • Sheikh Muhammad al-Busiri
    • Sheikh Harun
    •  Sheikh Abubakar bin Al-Qasim
    • -Malam Ahmad Qifu
    • Malam Usman bin Abubakar

    Domin karanta cikakken bayani a kan Wasu Daga Fitattun Malamai A Ƙasar Sakkwato Da Kewayen Ta danna nan.

    Domin karanta cikakken bayani a kan Tarihin Farko Na Nijeriya (1500 BC- 500 AD) danna nan.

    Wannan bayanin an ciro shi ne daga Littafin Tsarin Tsangayun Alƙur’ani A Arewacin Najeriya; Tarihin Su Da Zamantakewar Su Da Hanyoyin Raya Su; wanda Dr. Sunusi Iguda Ƙ/Nasarawa ya wallafa shi; domin karanta cikakken Littafin danna nan.