Narkewar Tsibbu Cikin Bokanci

0
391

Wannan shi ake kira “gamin gambiza”, ma’anar wannan ita ce wata dabara ta yin gamin gambizar magungunan gargajiya na Bahaushe da ba Musulunci ne ya zo da su ba, da kuma nassoshi ko ayoyin Alƙur’ani. Misali a nan shi ne:

– Haɗa hayaƙin biya-rana da ƙasar ƙafar yarinya ko wata mace da ake so, Wanda da ma can Maguzawa ke yi kafin Musulunci, sannan a haɗa da waccan aya ta Alƙur’ani don mallakar zuciyarta.

A daidai wannan lokaci kuma, sai aka samu wasu baƙin littattafai suka fara shigowa daga Maroko da Masar da Tunis da Libya waɗanda ke karanbanin leƙe-leƙen abin da Ubangiji Maɗaukaki da Manzonsa (Sallallahu Alaihi Wa Sallam) ba su ce a leƙa ba (gaibu). Waɗannan ilmai sun haɗa da:

– Ilmin Aufaƙu da siddabaru da Hisabi da
– Tanjimi da falaƙi da mutantani da Rafani

A waɗansu lokuta za ka ga ƙwararru a wannan fage na tsibbu, ba masana ne na Alƙur’ani ba. Kodayake su kansu ma makarantan suna alfahari a ce sun shahara a cikinsa.

Ƙarni na ashirin wani ƙarni ne mai ƙunshe da sauye-sauye masu yawa da suka shafi rayuwa da cigaba. Wannan ya ƙara buɗe ƙofofin cin kasuwar tsibbu.

Daga cikin asiran da suka shahara a wannan lokaci akwai:

– Siddabaru
– Hisabi
– Ramli
– Ilmin taurari da falaƙi

Siddabaru ko rufa ido dai ya ƙunshi wasu ‘yan dabaru, waɗanda na bayan fage bai san da su ba sai an bayyana masa. Amma da an bayyana su, ya gan su, ya san dabaru ne kawai. Watau daga kalmar dabara ko dabaru. Daga cikin abubuwan da ke wakana a wannan ɓangaren na siddabaru akwai:

1. Saka ƙwai cikin kwalba
2. Saka allura a hanci
3. Dabon kuɗi
4. Haɗiye tsaba a baki ta fito ta ido
5. Yanka wuƙa a jiki
6. Dafa nama a saman itaciya
7. Harbin kasko a ga jini

Domin ƙarin bayani kan waɗannan sai a duba (Bunza, 1970 da 1995).

A ɓangaren sihiri kuwa, abubuwa biyu ke gudana. Da farko akwai kimiyya, na biyu kuwa shi ne ƙarfin iskoki ta fuskar tsafi tantagaryar sa. Hanyoyin aiwatar da sihiri cikin tsibbu gamin gambiza ne, ko mu ce hatsin bara ne. Ma’ana akan haɗa da ayyukan Musulunci ko Alƙur’ani, a hautsina da na Maguzawa. ldan kimiyya ce, da yawa daga ciki asiran tsirrai ne da itace.

Shi kuwa ɓangaren hisabi ko (ramli) da tanjim (ilmin Taurari) bincike ne na abubuwan da suka faku wadanda suka gabata da waɗanda ake ciki da waɗanda za a fuskanta. Don samun haske game da alaƙar aljannu ko shaiɗanu da fagen tsibbu da kashe-kashensa da siffofin matsafa, sai ka ci gaba da karatu har ƙarshen wannan Babi.

Domin karanta cikakken bayani a kan Yadda Neman Laƙani Da Asiri Ya Shiga Tsangayu danna nan.

Domin karanta cikakken bayani akan Zirga-Zirga Tsakanin Bokaye Da Masu Duba Don Neman Duniya danna nan.

Wannan bayanin an ciro shi ne daga Littafin Tsarin Tsangayun Alƙur’ani A Arewacin Najeriya; Tarihin Su Da Zamantakewar Su Da Hanyoyin Raya Su; wanda Dr. Sunusi Iguda Ƙ/Nasarawa ya wallafa shi; domin karanta cikaken Littafin danna nan.

labarin da ya wuceHaramtaccen Laƙani Ko Asiri
Labarin na GabaAsalin Tsibbu A Tsangayun Alƙur’ani