Yadda Ake Yi Wa Maigida A Lokacin Fushi

0
21

Mu mata haƙiƙa muna da yawan yin laifi. Abin da ake so shi ne, mu dinga taƙaita fushi. Kada mu yarda mu dinga zaman gaba da mazajenmu.

A duk lokacin da muka yi wa maigida kuskure, to mu yarda mun yi laifin, kada mu tsaya muna musu, kuma mu ba da haƙuri. Domin yin hakan riba ce babba. Saboda wannan Hadisin.

Annabi Alaihissalam yana cewa: “Shin kuna son in ba ku labarin matanku su wane ƴan Aljannah?

sahabbai suka ce: “Eh”. Ya ce, “ƴan Aljannah daga cikin matayenku su ne masu haihuwa, kuma masu jin tausayin mazajensu, wadda duk lokacin da mijinta ya yi fushi, sai ta ce, “Wallahi ba zan yi barci ba har sai ka ce ka yafe min”.

Domin karanta Waya Kamata In Bayyana Wa Sirrina Idan Na Fara Al’ada Danna nan 

Bukhari

Mafi yawancinmu ba ma iya juriya da haƙuri. Tilas idan an ɓata wa mace rai ta damu. To amma a duk lokacin da maigida ya yi fushi, kamata ya yi ke kuma ki haɗiye naki fushin, don ki samu shiga cikin waɗanda Allah yake so. Don Allah yana cewa: “Waɗanda suke ciyarwa a cikin sauƙi da tsanani, kuma suke masu haɗiyar fushi, kuma da masu yafe wa mutane laifi. Kuma Allah yana son masu kyautatawa”.

(Ali’imran: 134)

Idan yana faɗa, sai ki yi shiru har ya gama faɗansa, ko da kuwa bai fahimci yadda abin yake ba. Ba za ki yi masa bayani ba. Sai dai in abin ya wuce (ya huce), to sai ki yi masa bayanin ga yadda abin yake. To sai ya fahimta, kuma ya karɓi uzurinki.

Domin karanta Yadda ‘Yan Mata Ya Kamata Su Kula Da Jikinsu Daga Lokacin Balaga Danna nan

Idan kuma maigida ya yi miki laifi ne, kuma kina so ya gane hakan, ba tare da kin ɓata rai ba. To sai ki nemi hanya mai kyau. A misali, idan kina kiran sa da suna na soyayya wanda yake jin daɗinsa. Kamar Habibi ko My dear. To sai ki canja don ya gane. Ki dinga kiransa Malam ko Maigida, to da ya ji kin canja zai damu, ya kuma nemi jin me ya faru ne.

Annabi (S.A.W) ya cewa Nana A’isha, “Ina ganewa idan kina fushi”. Sai ta tambaye shi. “Yaya kake ganewa?” Sai ya ce, “Idan ba kya fushi in za ki yi rantsuwa kina cewa WA RABBI MUHAMMADIN. Amma in kina fushi za ki rantse, sai ki ce “WA RABBI IBRAHIM”.

Bukhari

Domin Dauko Cikekken Littafin Danna nan 

labarin da ya wuceAbubuwan Da Suke Ƙara Soyayya Ga Maigida
Labarin na GabaAbubuwan Dake Rage Ƙaunar Miji Gurin Matarsa