Yadda Kunya Take

0
16

“Kunya tana kawo dukkan alheri” (Manzon Allah SAW)

Kunya wata ɗabi’a ce da take hana mutum aikata rashin ɗa’a ga Allah ko ga mutane. Kunya ɗabi’a ce da Allah ya yi umarni da shi tun tale-tale ba a addinin musulunci kaɗai ba, duk addinai kunya abu ne da aka yi umarni da shi, kuma abu ne mai kyau.

Wannan ya sa Manzon Allah SAW yace: “Yana daga cikin abinda mutane suka gada daga kalaman hikima na Annabawa magabata – shi ne – Idan ba ka jin kunya, toh ka aikata abinda ka ga dama” Allah Ta`ala ya ba mu labarin wasu `yanmata da Annabi Musa ya shayar da dabbobinsu lokacin da ya bar Masar ya nufi Madyana a cikin suratul ƙasas.

Wannan ƙissar an kawo ta a littafin Linjila ta Annabi Isa (AS) a wannan ƙissar an nuna yadda waɗannan ‘yanmata ko ɗaya daga cikinsu take ta jin kunya lokacin da za ta ta kai Annabi Musa AS wurin mahaifinsu ta yadda tana tafiya amma tana jin kunya.

A addinin musulunci wanda yake addinin ne da bai bar komai ba mai kyau sai da ya yi umarni da shi, sannan duk wani abu mummuna ya yi hani da shi, ya yi umarni da jin kunya. Manzon Allah SAW ya ce “ Kunya tana daga cikin imani”.

Kunya a addini ta kasu kashi biyu:

Kunyar Allah; wanda shi ne mutum ya rinƙa ganin girman Allah ta yadda ba zai aikata wani abinda ya saɓa wa umarnin Allah ko ya ƙi aikata abinda Allah ya umarce shi ba. Idan mutum yana jin kunyar Allah to, ba zai aikata abinda Allah ya hana shi ba ko ya ƙi aikata abinda Allah ya umarce shi ba, saboda ya san Allah yana ganinsa. Wannan zai sa ya rinƙa ganin girman Allah.

Kunyar mutane; wannan tana ƙasa da wancan na farkon. Kunyar mutane tana hana mutum aikata abinda ya ga dama a cikin rayuwar yau da gobe a cikin mutane. Zai hana shi aikata abinda Allah ba ya so. Ba wai don mutum ya ƙi aikata wani abu dan tsoron Allah ba, sai dan kunyar mutane. A’a, Bahaushe ya ce: ana barin halal don kunya. Abinda ake nufi shi ne, wani abin ba saɓa wa Allah ba ne, amma a al’adance ba daidai ba ne, idan dai addini bai wajabta shi ba, toh mutum zai iya bari don kunyar mutane. Wannan shi ma abu ne mai kyau.

Manzon Allah SAW da kansa an rawaito cewa yana da tsananin kunya kamar yadda budurwa take da kunya. An san yadda budurwa- a da- su ke da kunya. Shi yasa Manzon Allah SAW ya ce idan aka tambayi budurwa kan maganar aure, toh shirunta shi ne amsa. Wannan ya nuna irin kunyar da budurwa take da shi ba zai ba ta dama ta amsa kai tsaye ba.

Haka aka rawaito ce wa Sayyidina Uthman RA yana da tsananin kunya. Manzon Allah SAW ya ce: har Mala’iku suna jin kunyar Sayyidina Uthman. Manzon Allah ya ce shin ba zan ji kunyar wanda mala’iku suke jin kunyar sa ba.

Nana Aisha RA an rawaito tana cewa: Da aka binne Manzon Allah SAW a ɗakinta da Sayidina Abubakar, tana iya cire kayanta ko mayafinta idan ta shiga ɗakinta, saboda mijinta ne da mahaifinta, amma da ka binne Sayyidina Umar a ɗakin sai ta ce sai na daina cire kayana ko mayafina a ɗakin saboda ina jin kunyar Sayyidina Umar. Duk da ba a raye yake ba, yana kabarinsa, amma tana jin kunya cire mayafinta a inda aka binne shi.

Ba a musulmi ba kaɗai, har cikin waɗanda ba musulmi ba ana samun masu kunya saboda ɗabia’a ce mai kyau. A tarihin babban malamin nan Sir Issac Newton, ana faɗin cewa mutum ne mai kunya sosai da kamun kai, har ta kai ba ya son magana sosai a gaban jama’a.

A mata kuma akwai irin su Isabella Clara Eugenia (1566 – 1633) duk da cewa mai mulki ce sosai, amma mace ce mai kunya da kamewa sosai. Akwai Maria Sibylla Merian (1647 – 1717) wadda tana daga cikin mata kaɗan da suka shahara a ɓangaren kimiyya a wacan lokacin, amma ta zaɓi gudumawarta ya fito fili ba ita ba, saboda ta fifta kunya, kamun kai da mutunci.

Ga su ire iren Sarauniya Alexandra(1844 – 1925), matar Sarki Edward VII, `yar sarakai ce daga ƙasar Denmak, kuma matar basarake amma ba ta jefar da kunya, mutunci da kamun kai ba. Da waɗannan ɗabi`u ake gane ta duk inda ta shiga a Ingila alokacin duk da ba ta yawan fita jama`a.

An kawo waɗannan ne don a nuna kunya ba addinin musulunci ne kaɗai ya yi umarni da ita ba, har ma sauran addinai da al`ummu daban daban. Kuma abu ne da mutane suke ƙaunar mai wannan sifar, da kuma yaba masa.

Kunya ba ƙauyanci ba ne, ba kuma rashin wayewa ko gaɓanci ba ne, a a, ɗabi`a ce mai kyau. Manzon Allah SAW ya ga wani mutum yana yi wa ɗan`uwansa faɗa kan cewa ya faye jin kunya. Sai Manzon Allah SAW ya ce masa: ƙyale shi, kunya ba abinda take kawowa sai alkhairi” wannan ya nuna mana kunya alheri ce, ba kauyanci ba ne ko rashin wayewa. Kuma rashin kunya ba wayewa ba ne kuma ba wayo ba ne ko birnanci.

A wannan zamanin musamman na Social Media, matasa da yawa sun tsame kansu daga jin kunya, musamman mata, waɗanda su ya kamata su kasance kan gaba wurin nuna wannan ɗabi`a kyakkyawa. Abubuwa na baɗala, lalacewa da rashin albarka duk sun yawaita a tsakanin matasa, ba don komai ba sai rashin wannan ɗabi`a ta kunya.

Manzon Allah SAW ya yi gaskiya da ya ce “Wanda ba ya jin kunya ya aikata abinda ya ga dama” saboda rashin kunya da matasa ba ji yanzu, ya sa suke ta tsula tsiyar su a Social Media. Mata suna nuna tsaraici a fili, ana maganganun batsa, da baɗala, kai har ta kai ka ga ana nuna fasiƙanci a fili.

Waɗanda suke waɗannan ayyukan na ashsha ba sa jin kunyar kowa, shi yasa suke abin da suka ga dama. Ka ga budurwa da ake sa ran za a same ta mai tsananin kunya amma ta fito duniya tana nuna tsaraicinta a fili ko tana magaganun batsa. Ba abinda ya jawo haka sai rashin kunya.

Ci gaban zamani da ilimin zamani ba su ne suke ba da gudunmawa wurin ƙaruwar rashin kunya ba kaɗai, ga misalai nan da yawa na mata da maza wanda sun kai wani matsayi na karatun zamani amma sun kame kansu, suna da kunya da mutunci. Sannan a hannu guda kuma wasu ko bihim ba su sani ba, amma fitsara da sheɗanci ya zama musu abin tutiya.

Manzon Allah SAW ya ce kunya ba ta kawo komai sai alkhairi, duk mai kunya toh zai ga sakamakon kunyarsa, ita ɗabi`a mai kyau ba ta faɗuwa ƙasa banza kuma tana da amafani. Akwai tagomashi mai yawa a nan duniya da kuma lahira. Kunya ba za ta bar mutum ya saɓa wa Allah ba, kunya ba za ta bar mutum ya wulaƙanta ba, kunya tana jawo wa mutum ɗaukaka da daraja.

Rashin kunya takan sa mutum ya saɓa wa Allah, rashin kunya takan sa mutum ya wulakanta, takan jawo ƙasƙanci, taɓewa, da na sani da nadama. Manzon Allah SAW ya ce: “kunya tana da ga cikin Imani” duk mai kunya yana da imani, mara kunya shi kuma akasin haka. Imani kuwa ba inda yake kai mutum sai ɗa’a, ɗa’a kuma aljanna take kai mutum kai tsaye. Allah ka sa mu dace. Amin.

Danna nan don karanta Shaiɗanin Wannan Ƙarni: JEFFERY EPSTEIN

Edita@rumasau-kallamu

labarin da ya wuceTatsuniyar Dogarawa Uku
Labarin na GabaTatsuniyar Tsohuwa Da ‘Yan Mata Uku
Rabiu Musa Adam
Sunana Rabiu Musa Adam, ni malami ne a sashen koyar da manya na cibiyar Al-Furqan, Kano.