Author: Rabiu Musa Adam

  • Yadda Kunya Take

    Yadda Kunya Take

    “Kunya tana kawo dukkan alheri” (Manzon Allah SAW)

    Kunya wata ɗabi’a ce da take hana mutum aikata rashin ɗa’a ga Allah ko ga mutane. Kunya ɗabi’a ce da Allah ya yi umarni da shi tun tale-tale ba a addinin musulunci kaɗai ba, duk addinai kunya abu ne da aka yi umarni da shi, kuma abu ne mai kyau.

    Wannan ya sa Manzon Allah SAW yace: “Yana daga cikin abinda mutane suka gada daga kalaman hikima na Annabawa magabata – shi ne – Idan ba ka jin kunya, toh ka aikata abinda ka ga dama” Allah Ta`ala ya ba mu labarin wasu `yanmata da Annabi Musa ya shayar da dabbobinsu lokacin da ya bar Masar ya nufi Madyana a cikin suratul ƙasas.

    Wannan ƙissar an kawo ta a littafin Linjila ta Annabi Isa (AS) a wannan ƙissar an nuna yadda waɗannan ‘yanmata ko ɗaya daga cikinsu take ta jin kunya lokacin da za ta ta kai Annabi Musa AS wurin mahaifinsu ta yadda tana tafiya amma tana jin kunya.

    A addinin musulunci wanda yake addinin ne da bai bar komai ba mai kyau sai da ya yi umarni da shi, sannan duk wani abu mummuna ya yi hani da shi, ya yi umarni da jin kunya. Manzon Allah SAW ya ce “ Kunya tana daga cikin imani”.

    Kunya a addini ta kasu kashi biyu:

    Kunyar Allah; wanda shi ne mutum ya rinƙa ganin girman Allah ta yadda ba zai aikata wani abinda ya saɓa wa umarnin Allah ko ya ƙi aikata abinda Allah ya umarce shi ba. Idan mutum yana jin kunyar Allah to, ba zai aikata abinda Allah ya hana shi ba ko ya ƙi aikata abinda Allah ya umarce shi ba, saboda ya san Allah yana ganinsa. Wannan zai sa ya rinƙa ganin girman Allah.

    Kunyar mutane; wannan tana ƙasa da wancan na farkon. Kunyar mutane tana hana mutum aikata abinda ya ga dama a cikin rayuwar yau da gobe a cikin mutane. Zai hana shi aikata abinda Allah ba ya so. Ba wai don mutum ya ƙi aikata wani abu dan tsoron Allah ba, sai dan kunyar mutane. A’a, Bahaushe ya ce: ana barin halal don kunya. Abinda ake nufi shi ne, wani abin ba saɓa wa Allah ba ne, amma a al’adance ba daidai ba ne, idan dai addini bai wajabta shi ba, toh mutum zai iya bari don kunyar mutane. Wannan shi ma abu ne mai kyau.

    Manzon Allah SAW da kansa an rawaito cewa yana da tsananin kunya kamar yadda budurwa take da kunya. An san yadda budurwa- a da- su ke da kunya. Shi yasa Manzon Allah SAW ya ce idan aka tambayi budurwa kan maganar aure, toh shirunta shi ne amsa. Wannan ya nuna irin kunyar da budurwa take da shi ba zai ba ta dama ta amsa kai tsaye ba.

    Haka aka rawaito ce wa Sayyidina Uthman RA yana da tsananin kunya. Manzon Allah SAW ya ce: har Mala’iku suna jin kunyar Sayyidina Uthman. Manzon Allah ya ce shin ba zan ji kunyar wanda mala’iku suke jin kunyar sa ba.

    Nana Aisha RA an rawaito tana cewa: Da aka binne Manzon Allah SAW a ɗakinta da Sayidina Abubakar, tana iya cire kayanta ko mayafinta idan ta shiga ɗakinta, saboda mijinta ne da mahaifinta, amma da ka binne Sayyidina Umar a ɗakin sai ta ce sai na daina cire kayana ko mayafina a ɗakin saboda ina jin kunyar Sayyidina Umar. Duk da ba a raye yake ba, yana kabarinsa, amma tana jin kunya cire mayafinta a inda aka binne shi.

    Ba a musulmi ba kaɗai, har cikin waɗanda ba musulmi ba ana samun masu kunya saboda ɗabia’a ce mai kyau. A tarihin babban malamin nan Sir Issac Newton, ana faɗin cewa mutum ne mai kunya sosai da kamun kai, har ta kai ba ya son magana sosai a gaban jama’a.

    A mata kuma akwai irin su Isabella Clara Eugenia (1566 – 1633) duk da cewa mai mulki ce sosai, amma mace ce mai kunya da kamewa sosai. Akwai Maria Sibylla Merian (1647 – 1717) wadda tana daga cikin mata kaɗan da suka shahara a ɓangaren kimiyya a wacan lokacin, amma ta zaɓi gudumawarta ya fito fili ba ita ba, saboda ta fifta kunya, kamun kai da mutunci.

    Ga su ire iren Sarauniya Alexandra(1844 – 1925), matar Sarki Edward VII, `yar sarakai ce daga ƙasar Denmak, kuma matar basarake amma ba ta jefar da kunya, mutunci da kamun kai ba. Da waɗannan ɗabi`u ake gane ta duk inda ta shiga a Ingila alokacin duk da ba ta yawan fita jama`a.

    An kawo waɗannan ne don a nuna kunya ba addinin musulunci ne kaɗai ya yi umarni da ita ba, har ma sauran addinai da al`ummu daban daban. Kuma abu ne da mutane suke ƙaunar mai wannan sifar, da kuma yaba masa.

    Kunya ba ƙauyanci ba ne, ba kuma rashin wayewa ko gaɓanci ba ne, a a, ɗabi`a ce mai kyau. Manzon Allah SAW ya ga wani mutum yana yi wa ɗan`uwansa faɗa kan cewa ya faye jin kunya. Sai Manzon Allah SAW ya ce masa: ƙyale shi, kunya ba abinda take kawowa sai alkhairi” wannan ya nuna mana kunya alheri ce, ba kauyanci ba ne ko rashin wayewa. Kuma rashin kunya ba wayewa ba ne kuma ba wayo ba ne ko birnanci.

    A wannan zamanin musamman na Social Media, matasa da yawa sun tsame kansu daga jin kunya, musamman mata, waɗanda su ya kamata su kasance kan gaba wurin nuna wannan ɗabi`a kyakkyawa. Abubuwa na baɗala, lalacewa da rashin albarka duk sun yawaita a tsakanin matasa, ba don komai ba sai rashin wannan ɗabi`a ta kunya.

    Manzon Allah SAW ya yi gaskiya da ya ce “Wanda ba ya jin kunya ya aikata abinda ya ga dama” saboda rashin kunya da matasa ba ji yanzu, ya sa suke ta tsula tsiyar su a Social Media. Mata suna nuna tsaraici a fili, ana maganganun batsa, da baɗala, kai har ta kai ka ga ana nuna fasiƙanci a fili.

    Waɗanda suke waɗannan ayyukan na ashsha ba sa jin kunyar kowa, shi yasa suke abin da suka ga dama. Ka ga budurwa da ake sa ran za a same ta mai tsananin kunya amma ta fito duniya tana nuna tsaraicinta a fili ko tana magaganun batsa. Ba abinda ya jawo haka sai rashin kunya.

    Ci gaban zamani da ilimin zamani ba su ne suke ba da gudunmawa wurin ƙaruwar rashin kunya ba kaɗai, ga misalai nan da yawa na mata da maza wanda sun kai wani matsayi na karatun zamani amma sun kame kansu, suna da kunya da mutunci. Sannan a hannu guda kuma wasu ko bihim ba su sani ba, amma fitsara da sheɗanci ya zama musu abin tutiya.

    Manzon Allah SAW ya ce kunya ba ta kawo komai sai alkhairi, duk mai kunya toh zai ga sakamakon kunyarsa, ita ɗabi`a mai kyau ba ta faɗuwa ƙasa banza kuma tana da amafani. Akwai tagomashi mai yawa a nan duniya da kuma lahira. Kunya ba za ta bar mutum ya saɓa wa Allah ba, kunya ba za ta bar mutum ya wulaƙanta ba, kunya tana jawo wa mutum ɗaukaka da daraja.

    Rashin kunya takan sa mutum ya saɓa wa Allah, rashin kunya takan sa mutum ya wulakanta, takan jawo ƙasƙanci, taɓewa, da na sani da nadama. Manzon Allah SAW ya ce: “kunya tana da ga cikin Imani” duk mai kunya yana da imani, mara kunya shi kuma akasin haka. Imani kuwa ba inda yake kai mutum sai ɗa’a, ɗa’a kuma aljanna take kai mutum kai tsaye. Allah ka sa mu dace. Amin.

    Danna nan don karanta Shaiɗanin Wannan Ƙarni: JEFFERY EPSTEIN

    Edita@rumasau-kallamu

  • Riya Da Tasirin Social Media

    Riya Da Tasirin Social Media

    RIYA A MUSULUNCI:

    Duk wata ibada da musulmi zai yi don neman lada a wurin Allah, sharaɗi ne ya zama an yi shi ne saboda Allah Shi Shi kaɗai, ba tare da an haɗa Shi da wani mahaluki cikin wannan ibadar ba. Dole ne musulmi ya nufi Allah da kowace irin ibada da niyyar Allah ne Ya ba da umarnin a yi kuma Shi zai bada lada. Ya tabbata a hadisin Mahmud Bin Labid RA cewa Allah SWT zai faɗa wa waɗanda suka aikata wani aiki ba don Allah shi kaɗai ba, Allah zai ce musu ku je wurin waɗanda kuka yi aikin domin su a duniya su duba ko su na da ladan aikinku.

    A hadisin Imam Ahmad, Manzon Allah SAW ya ce “ Babban abinda na fi ji muku tsoro, ƙaramar shirka. Sahabbai suka ce; mecece ƙaramar shirka? Manzon Allah SAW ya ce Riya” Riya ƙaramar shirka ce ta fuskar neman yardan Allah da kuma neman yabon mutane. Shi kuma Allah, in dai ibada ce, toh Shi kaɗai ƙwallin – ƙwal a ke yi dominSa ba a haɗa Shi da wani – ko waye shi. Ita wannan shirkar bata fitar da mutum daga musulunci, amma tana ruguje ladansa, ta sa ya rasa ladan gaba ɗaya, sai dai ma ya ƙare da zunubi.

    Saboda haɗarinta, Manzon Allah SAW ya ja hankalinmu game da ita a hadisin Abi Musal Ash`ari, ya ma gargaɗe mu da mu guje ta. A wani hadisi Manzon Allah SAW ya ce: Riya tana shiga aiki – ba tare da mutum ya sani ba, kamar yadda Tururuwa ta ke tafiya akan dutse a cikin duhun dare” Jin tafiyar Tururuwa a kan dutse a cikin duhun dare abu ne mai wahala, toh haka tantance Riya cikin aiki, ta hanyar shin da wani nufi ko niyya aka yi aikin.

    TASIRIN SOCIAL MEDIA:

    Wannan dandali ko saha ta zama ruwan dare mai gama duniya, kuma tasirinsa ya wuce duk yadda mutum ya ke tsammani. Cikin `yan sakanni, duk wani abinda ya faru zai iya karaɗe duniya batare da bata lokaci ba. Wanɗanda su ke manyan birane ko cikin surƙuƙin daji duk zasu gani ko su ji. Sannan tasirin sa yanzu ya kai yana iya canza komai.

    Tasirin social media, ya kai yana iya canza wani ra’ayi na manyan mutane ɗaiɗaiku, yana iya tasiri a kasuwanci a kasuwanci, siyasa kai har uwa uba yana canza ƙudurorin gwamnatocin ƙanana da manyan ƙasashe. Idan akwai abinda zai iya girgiza gwamnati cikin ‘yan sakanni a wannan zamanin babu kamar Social Media.

    Cikin `yan kwanakin nan shugaban ƙasar Amurka Trump ya yaɗa wani shaguɓe da barkwanci a ɗaya daga cikin dandalin social media inda ya nuna shi ne “Yesu” wanda zai ceto duniya. Kafin ka ce wani abu, duniya ta sako Trump a gaba nan da nan ya goge abinda ya wallafa.

    Misali na biyu; bayan hare haren da Isra`ila ta kai wasu garuruwa a ƙasar Labanon, ranar 16 zuwa 17 ga watan Afrilu, 2026 sai wani bidiyo ya yi ta yawo a Social Media inda aka gano wasu sojojin Isra`ila sun karya wani mutun-mutumin “Yesu” suna faffasa shi da guduma.

    Wannan abin ya janyo kakkausar sukar ƙasar Isra’ila, duk da an san yadda Israila take da taurin kai ga duk ƙudurorinta ko abin sojojinta suka aikata, amma sai ga shi hukumomi a Isra`ila suna ba da haƙuri game da abinda ya faru, har da hukunta sojojin da suka aikata abin da hukuncin dauri na kwana 30 a gida, da kuma samar da wani mutun-mutumin sabo da mayar da shi inda yake nan take cikin kwanaki da bai wuce biyar ba. Wannan abin ba wanda ya isa ya sa Isar`ila ta yi wannan abin duk duniya in ban da tasirin Social Media ba.

    MUTANE A YANZU DA SOCIAL MEDIA:

    Ɗan adam, Allah ya halicce shi da son burgewa, neman ɗaukaka da shuhura. A yanzu dandalin Social Media ya zama hanya mafi sauƙi wurin samun waɗannan abububwan, nan da nan mutum zai shahara ko`ina a sanshi a ganshi, sunansa ya yaɗu. Akwai mutanen da ban da tasirin social media ba, da har su mutu ba wanda zai san suntaba rayuwa, sai `yan kaɗan da suke kusa da su, sai kuma a labari da hira in ta kama.

    Misali, irin manyan shehunan malaman da aka taɓa yi a ƙasaittacen birnin Kano waɗanda muke jin labari da wasu ma da har yanzu bamu sansu ba – Allah yayi musu rahama, Ya sa suna aljannah- da yanzu ne da sun karaɗe sosial media ko`ina an sansu ana ganinsu kamar yadda a yanzu muke ganinsu Prof. Bashir Aliyu Umar, OON da sauransu. Muna jin labarin Barau ƙwallon- shege da aka taba yi shi ma a Kano. Da yanzu ne da duk duniya sai ta san labarinsa kamar yadda aka san su Umar Bush da sauransu.

    Shugannin ƙasashe, manyan jagororin kasuwanci da na manyan shugabannin wuraren hada hada a duniya, yanzu sun fi maida hankali wurin nuna manufofinsu ta waɗannan hanyoyi na social media. Daga cikin shugabanni, kan gaba wurin amfani da social media akwai shugaban Amurka Trump, manyan `yan kasuwa akwai su biloniyan nan Elon Musk da kamfanisa na Tesla.

    RIYA DA SOCIAL MEDIA

    Wannan tasiri da ake gani na wannan sahar da dandali, ya sa wasu mutane dan neman shuhura da neman ɗaukaka, yin amfani da waɗannan hanyoyi ta yadda ba su tsaya neman duniya kaɗai ba, sai suka zarce har da aikin ibada. Mutane kowa yana neman hanyar da zai yi shuhura, wasu sun rungumi tallace tallace da kasuwanci, wasu bada ilimin addini da tarbiyya, wasu sana`o`i da ilimin zamani, wasu ɓarna da fasadi.

    Waɗanda suka ɗauki yaɗa ayukan ibadan da suke yi a social media, dan neman ɗaukaka da shuhura, su sani, wannan ba dai dai ba ne. Abin ya zama ruwan dare, sai ka ga mutum zai taimaka wa wani ko wasu masu buƙata, amma sai ya ɗora a media, ko bayan ya yi ibadar sa, sai kuma ya zo media yana ba da labari.

    Kai mai imani da ka yi don Allah, ina ka ga tallatawa a social media? Allah mabuwayi ne, kuma baya taɓar da aikin bawa, idan bawa ya yi ne dan Shi, sai Allah ya bashi ladan aikin cikakke kuma ya sa mutane suyi ta yaba masa ba tare da ya tallata a social media ba.

    Hadisin Abi Huraira wanda Imamul Bukhari ya fitar da shi, Manzon Allah SAW ya ce: “ Mutane bakwai suna cikin inuwar Al`arshi ranar da babu wata inuwa sai ita (ranar ƙiyama)- daga cikin waɗannan mutane, akwai wanda yayi sadaka da hanun damansa amma hanun hagunsa ba sani ba” a wannan hadisin yana nuna mana tsantsar ikhlasi da boye aikin ibada dan Allah shi kaɗai.

    Mu sani, duk wanda ya yi aikin ibada, idan har ya yi ne don a gani, ko don a yaba masa, ba shi da ladan komai a wurin Allah. Allah zai faɗa wa waɗanda suke aikin ibada dan a gani a yaba ranar tashin ƙiyama, Ya ce musu: “Ku je wurin waɗanda kuka yi aiki dan su, ku duba ko suna da ladan da za su ba ku” wanda ya yi aikin ibada a nan duniya ya ɗora a social media don ya sami comment da likes, to waɗannan comments da likes ɗin su ne ladansa, ba shi da komai a wurin Allah.

    Allah SWT ya ce “ Sai mu gabatar da ayukan da suka aikata, sai kawai mu sheƙar da shi kamar ƙura”S25:23, wasu malamai sun fassara wannan ayar ta cikin suratul Furƙan da cewa; waɗanda suka yi aiki ne ba dan Allah ba, sun yi ne dan su sami yabo, shuhura da ɗaukaka (likes, commnets and share), ko dan a san sun yi ko suna yi, to Allah sai ya sheƙar da ladan su kamar ƙura. Duk wanda ya yi aikin ibada dan likes, kuma ya samu, toh an biyashi, haka wanda yayi dan comments, share, view ko followers.

    Daga ƙarshe, mu ji tsoron Allah mu kyautata niyar ayukanmu, mu sani, Allah ne ya yi umarni da dukkan aikin ibada, kuma Allah ne zai bada lada. Wanda ya yi imani da Allah akan haka, ya sani Shi Allah duk inda bawa yayi aikin ibada – cikin dare ko rana, a bayyane ko a ɓoye, a birni ko a ƙauye- Allah ya sani kuma zai bashi lada cikakke. Shi tsantsance aiki ga Allah, shine duk lokacin da bawa zai gabatar da aiki kar ya nufi kowa da wannan aikin a zuciyarsa in ba Allah Shi kaɗai ba.

    Allah yana fada a wani hadisil ƙudsi wanda Abi Huraira ya raiwato, Imam Muslim ya fitar da shi, Allah ya ce: “Ni mawadaci ne ga duk wani mai haɗa Ni da wani a cikin aiki, duk wanda ya yi aiki ya haɗa Ni da wani, toh Ni bana buƙatar wannan aikin” Ɗan’uwa musulmi, mai imani da Allah bazai so a ce Allah ya ce baya bukatar aikinsa ba, ranar da yake cikin tsananin bukatar ladan aikinsa.

    Allah ka datar da mu, ka kaɓi ayukan mu. Amin.

    Danna nan don karanta Ga Tsoro Ga Ban Tsoro

    Edita@rumasau-kallamu

  • Shaiɗanin Wannan Ƙarni: JEFFERY EPSTEIN

    Shaiɗanin Wannan Ƙarni: JEFFERY EPSTEIN

    “Lallai shi – shaiɗan – yana umartanku ne da munanan ayuka da kuma alfasha”

    Jeffery Seymour Epstein an haife shi a 1953 a Brooklyn da ke birnin New York. Iyayensa, wato Seymour Epstein da Pauline Epstein yahudawa ne, kuma ba wasu shaharraru ba ne. Mahaifinsa ƙaramin ma’aikaci ne mai kula da wuraren shaƙatawa na birnin NewYork, Mahaifiyarsa kuma aiki take – ba koyarwa ba- a wata makaranta.

    Epstein ba shi da ‘yanuwa a wurin iyayensa wato ƙanne ko yayye. Ya taso a birni, kuma ya yi sakandare sannan jami`a, inda ya fara karantar lissafi da physics amma bai gama jami`a ba, duk da haka a 1979 ya sami karantarwa a wata makaranatar `ya`yan masu hannu da shuni mai suna Dalton School a Manhattan.

    A wannan makaranata ce ya haɗu da manayan mutane, ɗaya daga ciki kuma wanda ya taimake shi, shi ne Alan Greenberg shugaban kamfanin Bear Sterns. Wannan mutum shi ya fara shigar da Epstein harkar kuɗaɗe. Damar da masu shaidar karatu ma ba kowa ba, amma Epstein ya same ta a Vagas.

    Da goyon bayan Alan ne aka ɗauki Epstein a kamfanin Bear Stern a matsayin ƙaramin ma’aikaci amma nan da nan sai ya zama yana hada-hada da manyan masu kuɗi. Bayan nan Epstein ya bar Bear Stern, amma ba a san dalilin barinsa ba, lokacin ya ƙware wurin yadda ake hada-hada da manyan kuɗaɗe kuma ya ƙulla alaƙa da manyan masu kuɗi.

    A shekarun 1980 ya fara kula da kuɗaɗen manyan mutane, mafi muhimmanci a cikinsu shi ne wani shahararren biloniya mai suna Leslie Wexner wanda ya kafa Victoria`s Secret (L Brands) a wannan lokacin ne Epstein ya mallaki maƙudan kuɗaɗe, kuma ya sami damar ƙulla alaƙa da manyan ‘yan siyasa, sarakuna da manyaan ‘yan kasuwa na Amurka da sauran ƙasashen duniya.

    Esptein ya yi amfani da ƙwaƙwalwarsa da ƙwarewarsa wurin sarrafa kuɗaɗe, shirya tarruka na gani na faɗa, amfani da jiragen sa, wurare da gidaje na alfarma kuma na sirri wurin jan hankalin manayan mutane. Ya yi amfani da damar sa na attajiri, ya sami shiga jikin manyan attajirai na duniya, manyan sarakuna, shugabanni da jagorori al`umma.

    Epstein ya yi amfani da damar sa ya jefa waɗanda ya ƙulla alaƙa da su cikin wani irin mummunan tarko. Da yawa daga cikin waɗannan mutanen sun aikata aika aika da ta`asa marasa kyau marasa daɗin ji, kamar lalata da ƙanana yara, safarar ƙanan yara, tilasta wa mata da yara karuwanci da sauran badaƙala.

    Ana zargin sa da yin mafani da waɗannan aika aika na waɗannan manyan mutane don cimma burinsa na ƙashin kansa da kuma ci gaba da ɓarnarsa ba tare da damƙe shi ba ko an gurfanar da shi a gaban kuliya manta sabo. Sannan yana amfani da masha`ar da suka aikata ne dan tilasta musu yin abinda ya ke so ko kuma abinda wasu suke so.

    An fara tuhumar Epstein da laifuffuka na lalata da ƙanana yara, da sauran laifuffuka a 2008 wanda a wannan lokacin ya amsa wasu daga cikin laifuffukan, hakan yasa ya yi zaman wucin gadi na wata goma sha uku (13) a gidan yari cikin gata, har da ba shi kwana shida ya fita daga gidan yari dan zuwa hada-hadarsa. Daga baya ma aka sake shi.

    Bayan nan ya koma ya ci gaba da sharholiyarsa da harkokinsa a duniya. An sake buɗe wannan tuhuma a 2018, a wannan lokacin bai amsa laifinsa ba. A watan bakwai Yuli na shekaran 2019 aka kama shi aka tsare, bisa zarginsa da lalata da safarar ƙananan yara, haɗa kai da masu aikata manyan laifuffuka. An sami gawar Epstein a ɗakinsa na gidan yari ranar 10 ga watan tara 2019. Rahoto daga hukumomi ya tabbatar da ce wa Epstein ne ya kashe kansa.

    Wannan babban shaiɗani ne da an daɗe ba a sami kamar sa ba. Sannan ɓarnar sa ta yawaita, ta yi ambaliya, saboda an sami kundi kundi na ayyukan lalata da fasiƙancin sa da sauran manyan attajirai, sarakuna da shugabanni kimanin miliyan da wani abu.

    DALILAN DA KE JAWO AIKATA AYYUKAN ƁARNA

    Ayyukan fasiƙanci da lalata da sauran laifuffuka na keta alfarmar Allah sun zama ruwan dare a cikin alummar musulmi da ma waɗanda ba su ba. Daga cikin dalilan da yake sa ɓarna irin waɗannan ke yawaita, akwai ci gaban da aka samu a yanzu a duniya ta yadda komai yake yaɗuwa cikin sauƙi kuma ake samu cikin sauƙi ta hanyar kafofin sadarwa na zamani.

    ƘARANCIN TSORON ALLAH: tsoron Allah ya ƙaranta a zuciyoyin mutane, shi yasa ba sa ganin aikata laifi wani abu ne mai girma. Duk wanda tsoron Allah ya ƙaranta a zuciyarsa, to abu ne mai sauƙi a wajensa ya keta alframa Allah ba tare da ya ji komai ba. Allah Ta`ala ya ce: “Duk wanda ya girmama alamomin Allah, to lallai wannan yana daga cikin taƙawar zuciya” Tsoron Allah yana hana aikata ɓarna da laifi.

    ƘARANCIN ILIMIN ADDINI: Rashin sanin abinda Allah ya umarci mutum, da abinda Allah ya hane shi suna sa mutum ya faɗa cikin aikata ɓarna dumu dumu ba tare da ya san girman abinda yake aikatawa ba. Manzon Allah SAW ya ce: “…… wani bawa da Allah ya ba shi dukiya, amma bai ba shi ilimi ba, saboda haka yana ta ɗawainiya a cikin dukiyar, bai san Allah yana da haƙƙi a cikin dukiyar ba, ba ya jin tsoron Allah, ba ya sada zumuncinsa da wannan dukiya, ya ɗimauce, toh wannan yana cikin mummunar makoma” rashin sanin shari`ah yana sa bawa ya yi ta afkawa cikin laifi.

    YAUDARA TA SHEƊAN: Sheɗan babban abokin gaban ɗan Adam ne, Allah da kansa ya nusar da ɗan adam game da shi, Allah ya ja kunnen bawa game da haɗari, da makircin sheɗan. Allah ya ce: “kada ku bi tafarkin sheɗan, lallai shi babban abokin gabanku ne. Ba abinda yake umartanku da shi sai ɓarna da alfasha” a wani wurin Allah ya ce: “ Yana muku alƙawarin ƙarya, yana muku shigo shigo ba zurfi, ba abinda yake yi sai yaudara” saboda haka duk lokacin da sheɗan ya sami dama aka ɗan Adam ba abinda zai zuga shi sai saɓa wa Allah da tabka manya laifuffuka.

    ƘARANCIN KUNYA: kunya ɓangare ne na imani, wanda ba shi da kunya, toh ya rasa wani ɓangre na imani. Sannan wanda yake da ƙarancin kunya zai iya aikita duk abinda ya so. Manzon Allah SAW ya ce: “Duk wanda ba ya jin kunya toh ya aikata duk abinda ya so” musamman a yanzu za mu ga kunya ta ƙaranta a wurin matasa, musamman a kafofin sada zumunci, sai ɓarna kala kala ake yaɗawa saboda ƙarancin kunya.

    Waɗannan kaɗan ne daga dalilan da suke janyo keta alfarmar Allah, akwai wasu da yawa kamar rashin umarni da kyakkaywa da hani da mummuna, zama da abokan banza, rayuwar sharholiya, rashin tarbiyya ta gari, shagala da duniya da sauaransu.

    AƘIBAR AIKATA ƁARNA:

    Akwai aƙiba, wato sakayyar aikata ɓarna. Da yawa daga cikin mutane ba su san cewa aikata laifi da yawaita ɓarna su na da uƙuba ba. Daga ciki, aikata ɓarna da laifi yana jawo fushin Allah, da ƙarancin albarka a rayuwar mutane. Yawaitar masifu kala kala daban daban, kuma akai-akai, sannan rugujewar al`umma da rushewar gida da iyali, lalacewar matasa, taɓarɓarewar tarbiyya, da kuma uwa uba maƙikyanmu za su samu galaba a kan mu, su yi ta gasa mana aya a hannu ba kuma abinda za mu iya yi.

    HANYOYIN RAGE AIKATA ƁARNA:

    Akwai abubuwa da suke taimakawa wurin rage aikata ɓarna da laifuffuka ko kuma taƙaikta su, daga ciki akwai jin tsoron Allah kamar yadda ya dace, neman ilimin adddini, tarbiya ta gari, jin kunya da kamewa, umarni da kyakkaywa da hani ga mummuna, fifita lahira, girmama alamomin ubangiji da ganin alfarmarsa.

    RUFEWA DA SHAWARWARI

    A faɗin duniya ire-iren Epstein suna nan da dama, amma na shi ne yanzu ya fito fili, kuma manyan mutane da dama sun faɗa komar irin waɗannan mutanen, kuma sun rasa yadda za su fita. A yanzu haka akwai kundi na takardu, hotuna da bidiyo na wannan lalatar da ta ƙunshi mutane da dama wadda ta kai kimanin shafuka miliyan uku da dubu ɗari biyar wanda aka sake a yanzu.

    Babban abin lura a lamarin Epstein, shi ne yadda waɗanda suke rajin kare haƙƙin mata da yara, suke laɓewa suke tabka manyan laifukan lalata da ƙananan yara da safararsu kamar kayan gwanjo. Suna ta kururuwa game da auren wuri, amma sun ɓige da lalatar wuri a matsayin sharholiya. Wannan ya nuna cewa babu addinin da ya san `yancin mace da kare mata `yancinta kamar addini musulunci.

    Abu na biyu, manyan mutane da suka haɗa da attajirai, sarakuna, manyan malamai da mashahuran mutane su guji kutsawa cikin aikata abinda Allah ya hana don kawai suna da damar aikata laifi ba tare da wani ya sani ba. Su sani Allah ya ba su wannan mastsayi ne don taimakon al`umma ba don aikaita ɓarna ba. Allah ta’ala ya ce “ Waɗanda idan muka ba su mulki, shugabanci, jagoranci a bayan ƙasa, sai su tsai-da sallah, su ba da zakka, sannan su yi umarni da kaykkayawa, sannan su yi hani da mummuna”

    Sannan su guji ƙulla alaƙa da mutanen da ba su da gaskiya ko ba su da tarbiyya da mutunci, saboda faɗawa cikin komar mugayen mutane da za su rinƙa yi wa mutum barazana da masha’ar da ya aikata don biyan buƙatun kansu, ko dan irin wannan lokaci da ake ciki na bankaɗe bankaɗe da tonon silili.

    Da yawa daga cikin mutane sun faɗa irin wannan koma ta sheɗanu kuma sun rasa yadda za su yi su fita. Wasu sai dai su ƙara faɗawa cikin wata ɓarnar ta kisan kai dan su tsira. Kamar yadda ake zargin cewa wasu ne da suke cikin komar Epstein suka aika aka kashe shi don kawo ƙarshensa su samu su numfasa, saboda muddin yana raye, toh suna tafin hanunsa, sai yadda ya yi da su.

    Allah, muna roƙonka da ka kare mu daga keta alfarmarka, ka kare mu daga faɗawa komar sheɗanu. Allah ka shiryar da mu, ka sa mu cika da imani. Amin.

    Danna nan don karanta Ga Tsoro Ga Ban Tsoro

    Edita@rumasau-kallamu

  • Ga Tsoro Ga Ban Tsoro

    Ga Tsoro Ga Ban Tsoro

    “Ubangiji (Allah) ya halicci mutane, Samuel Colt ya dai-daita su”

    – Sammuel Colt (1836)

    12/08/2024

    SHIMFIƊA

    Samuel Colt ya faɗi wancan maganar ce bayan ya ƙirƙiri ƙaramar bindigar hannu (Revolver), don ya nuna mahimmancin abin da ya ƙirƙira. Sannan dan ya nuna rashin fifikon wani a kan wani idan kowa ya mallaki bindiga.

    Allah SWT ya ce: “Kada ku kashe kawunan ku, Allah mai rahama ne a gareku” (Q4:29). Allah Ta`ala ya ce: “Wanda ya kashe Mumini da gangan, sakamakonsa jahannama zai tabbata a cikinta…” (Q4:93). A Hadisi Manzon Allah SAW ya ce:” Baya tare da mu wanda ya ɗau makami a kan mu”

    Waɗannan ayoyi da hadisi da wasu masu tarin yawa suna hani ne game da kisan kai. A ayar farko Allah sai da ya nuna shi kansa mai rahama ne ga bayinsa, wato rashin tausayi ne da imani a zuciya ya ke sanya wani ya kashe mutum ɗan uwansa.

    A aya ta biyu kuma Allah ya nuna sakamakon wanda ya yi kisan kai ba da wani dalili na shari`ah ba. Manzon Allah ya faɗi cewa ba ya tare da Shi (Manzon Allah SAW) sannan ba ya tare musulmi gaba ɗaya wanda ya ɗau makami don zubar da jinin musulmi.

    MAKAMI A HANNUN FARAR HULA

    Hasashe ya tabbatar da cewa a duniya akwai ƙananan makamai kimanin milliyan ɗari Takwas da Saba`in da Biyar (875M) yawancin su a hannun fararen hula da gama-garin mutane.

    Kimanin miliyan ɗari (100) daga cikin waɗannan makaman suna Afirka, har da ƙasar mu Najeriya. Sannan kashi Arba`in (40%) na daga cikin mace mace a duniya sanadiyyar amfani da waɗannan makaman ne.

    Yaɗuwar ƙananan makamai musamman bindiga, wata matsala ce da duniya take fama da shi a yanzu. Bincike ya tabbatar da cewa abubuwan da suke ke janyo yaɗuwar ƙananan makamai sun haɗa da yaƙe yaƙe -rashin zaman lapiya a ƙasashe daban daban, da ayukan ta`addanci.

    Na biyu taɓarɓarewar dokokin ƙasashe da rashin ƙarfin gwamnatoci. Na uku ƙaruwar kamfanonin ƙirƙiran makamai a duniya. Waɗannan dalilai suna janyo ƙaruwar laifuffukan da suka haɗa da kashe-kashe, fashi da makami, kashe kai, ƙaruwar ayyukan ta`addanci da sauransu.

    Wannan matsalar ta shafi duniya gaba ɗaya, kullum ayyukan ɓarna da ke afkuwa cikin ƙasashe daban daban suna tabbatar da haka. Manyan ƙasashe irin su Amurka, kullum suna fama da irin waɗannan matsaloloin na amfani da ƙananan makamai wanda sanadiyyar su kullum ake rasa rayuka masu yawa.

    Duk da Amurka tana da dokar mallakar makami. Amma wannan matsalar ta addabi Amurka. Babban misali a nan shi ne yadda wani matashi mai suna Thomas Mathew Crooks ya kai wa ɗan takaran shugabancin ƙasar Amurka Donald Trump hari da bindiga, hakan ya yi sanadiyyar tsinke masa saman fatan kunnensa na ɓangaren dama.

    Wannan harin ya faru ne ranar 13 ga watan Yuli, 2024 a birnin Pennsylvania yayin da Donald Trump ya ke tsaka da yaƙin neman zaɓensa a zaɓen da ya gabata. Najeriya ɗaya ce daga cikin ƙasashen duniya da kuma Afirka da ke matuƙar fama da wannan matsala ta yaɗuwar ƙananan makamai a hannun gama-garin mutane da fararen hula, musamman a waɗannan shekarun.

    Ƙaruwar yaɗuwar makamai a hanun gama-garin mutane a Najeriya za a iya danganta shi daga lokacin da aka fara fasa bututun mai da kuma masu sace fararen fata suna garkuwa da su, musamman a kudancin ƙasar nan a baya.

    Zuwa rigingimun addini a Arewa ta tsakiya a farkon shekarun 90s, rigingimun Tibi da Jukun, sannan rigimar Boko haram/ISWAP da `yan ta`adda masu garkuwa da mutane a Arewa maso gabas na ƙasar nan, waɗannan rigingimu sun ta da zaune tsaye da kawo rashin kwanciyar hankali, sun janyo rasa rayuka masu yawa tun daga shekarun 2008 har zuwa yau.

    Gwamnatoci, ba za a ce ba sa taɓuka komai ba, amma a gaskiya, ayyukan `yan bindiga daɗi da masu tarzoma sun yi tsanani fiye da ƙima. Mutane har gani suke kamar sun fi ƙarfin hukumomi saboda wasu dalilai.

    Samuel Colt da ya ce Allah ya halicci mutane, shi kuma ya daidaita su. So yake ya fito da wani abu mai mahimmanci a fili. Duk wanda yake aikata aikin ta`adanci dan kawai yana riƙe da makami, toh ba fa ya fi wanda ya ke yi wa ta`addancin ƙarfi ba ne, kawai dan yana riƙe ne da makami.

    Duk lokacin da wanda ake yi wa ta`addanci shi ma ya riƙe makami, to sai dai kowa yi ta kansa, a lokacin kowa daidai yake da kowa, ba wanda zai yi wa wani ta`addanci, sai dai a yi kare-jini-biri-jini. Don haka kowa sai ya sa kowa cikin zullumi da tsoro.

    Masu riƙe da makamai sun sani, idan kowa zai sami makami toh su kansu ba za su ji daɗin rayuwar su ba kamar yadda suke yinta a yanzu, saboda yadda suke farautar sauran mutane, haka suma za a rinƙa farautar su.

    A irin wannan yanayi, sai rayuwa ta zama tamkar rayuwar dabbobi a daji wanda Allah ya ba shi sa’a shi ke nan, ba wanda ya ke da tabbacin rayuwarsa. Kowa kullum cikin zullumi da rashin kwanciyar hankali. Rayuwa ta zama ba komai ba, mara daɗi, gajeriya mai cike da tsoro.

    RUFEWA

    Allah SWT ya sanya rahama a cikin zuciyoyin halittarsa musamman ɗan adam, shi yasa za a ga Uwa yadda take tarairayar `ya`yanta. Wannan rahamar ce ta ke sanya mutum ba ya iya kashe ɗan uwansa haka kawai idan wannan rahamar tana cikin zuciyarsa. Shi ne abinda Allah ya ke nuni da ayar a aka ambata a farko.

    Shi kansa Allah da ya halicce mu, bai zama mai ɗaukan ranmu haka kawai ba, sai ajalin da rubuta mana ya yi. Duk wanda ya kashe wani, ya sani ba zai tabbata a duniya ba shi ma wata rana sai ya mutu, ya bar duniyar.

    A hadisin Manzon Allah SAW a fili ya faɗi cewa duk wanda ya ɗau makami ya yi kisan kai, to ba ya tare da Mu (wato ba ya tare da Manzon Allah SAW da kuma sauran muminai). Shin idan mutum ya mutu amma ba ya tare da Manzon Allah SAW, ina ne makomar sa?

    A aya ta biyu Allah ya ja kunnen mu da nuna mana sakamakon wanda ya aikata aika aikan kisan kai, makomar sa wutar jahannama kuma zai tabbata a cikin ta har abada. Shin wannan abin da Allah ya faɗa shin akwai wanda ya ke ganin ba haka ba ne? Ko kawai tatsuniya ce da labarin ƙanzon kurege?

    Duk musulmin da ya yi imanin akwai ƙiyama, akwai hisabi sannan akwai sakamako, to ya tabbata abinda Allah ya faɗi gaskiya ne to ba zai yarda ya kusanci wannan mummunan aikin ba, ba zai yarda ya ɗau ran wani mutum ba.

    Dukkan musulmi da yake rayuwa a wannan duniyar, na farko dai ya san zai mutu, toh buƙatar sa in ya mutu ya sami rayuwa mai daɗi da take cike da ni`ima wadda tafi ta nan duniyar. Rayuwar lahira ta aljannah ba a samun ta da saba wa Allah, musamman da mummunan aika aika na kashe ran ɗan Adam.

    Allah muna roƙonka ka shiryar da mu, Ka ganar da mu hanya mai kyau, Ka tabbatar da mu a kan ta, sannan Ka ba mu rayuwa mai kyau a nan duniya da rayuwa mafi kyau a lahira. Amin.

    Karanta Ayyukan Ta’addancin Matasa A Kano: Aure, Yawan Haihuwa Da Tarbiyya A Wata Mahanga

    Edita@rumasau-kallamu

  • Malamai, Malanta Da Hanyoyin Sada Zumunta II

    Malamai, Malanta Da Hanyoyin Sada Zumunta II

    September 12, 2024

    ƁANGARE NA II: HANYOYIN SADA ZUMUNTA

    Musamman a wannan ƙasar Najeriya hanyoyin sada zumunta sun fara ɓulla ne daga shekara ta dubu biyu (2000) lokacin da aka fara amfani da wayar hannu mai amfani da layin waya.

    Da farko wayoyin da ake amfani da su, wayoyi ne da ba sa ɗauke da manhajar hanyoyin sada zumunta, da yawan mutane a lokacin ba hanyoyin sada zumunta ne a gaban su ba, kawai abinda su ka fi yi shi ne buga waya da amsa kira.

    Za a iya ce wa mafiya wayancin waɗannan hanyoyi ba a samar da su ba, balle ma a saka su a matsayin manhaja a wayar hannu. Misali, manhajar sada zumunta na 2go wasu ɗalibai na jami`ar Witwatersrand Johannesburge, suka ƙirƙire shi a 2007.

    Brian Acton da Jan Koum su ne suka ƙirƙiri manhajar Whatsapp a shekara ta 2009, Facebook kuma Nick Clegg, Sheryl Sandberg, Sean Parker, Mark Zuckerberg suka ƙirƙira a 2004 a Massachuset ƙasar Amurka. Twitter kuma a shekarar 2006 aka ƙirƙire shi, amma sai 2012 aka ƙaddamar da shi wanda Jack Dorsey, Noah Glass, Biz Stone da Evan Williams su ka ƙirƙira.

    Twitter (2006), Tiktok( 2016), Telegram (2012). Kafinsu akwai wasu hanyoyin na wasiƙu da sada zumunci kamar su hotmail, yahoomail (1997) da gmail (2004) da sauransu amma ba a samun su a manhajar wayar hannu. Waɗancan su ne aka fi sani a nan, amma akwai dubbansu suna nan ana ta amfani da su yau a faɗin duniya.

    A nan kasar, musamman a yankin mu na Arewa, da yawa daga cikin masu amfani da waɗannan manhajoji na sada zumunta ba su san waɗannan manhajoji ba sai kusan shekarar 2010 yau shekara goma sha –biyar ke nan. Sannan da yawa da ga cikin mutane ba su san babban dalilin samar da waɗannan manhajojin ba, balle su yi amfani da su ta hanyar da ta dace.

    Matasa na cikin `yan gaba dai gaba dai wurin amfani da waɗannan manhajojin. Ƙaramin misalin da zan bayar shi ne a cikin mutane miliyan hamsin (50M) da suka yi amfani da 2go a nahiyar Afrika miliyan 13 suna Najeriya kuma sama da kashi casa`in (90%) matasa ne.

    Wannan hasashe haka yake har yau a ko ina, matasa su ne kan gaba wurin amfani da waɗannan hanyoyi musamman a ƙasashe masu tasowa. Wannan ya na faruwa ne sakamakon rashin aikin yi da zaman banza da matasa suke fama da shi a ƙasashe masu tasowa wanda ci bayan tattalin arziki ke sabbaba shi.

    A yau ana ganin samari marasa aikin yi suna yin duk abinda za su yi dan su sami kuɗin da za su sayi data dan su sami damar amfani da waɗannan manhajoji na sada zumunta. Misali, Facebook idan mutum ba shi da data, idan kuma ba lite yake amfani da shi ba, toh a akwai abinda ake cewa “free mode” kwai za ka ga rubutu, amma hotuna ko bidiyo ba za su bayyana ba, sannan ba zai baka damar bin hanyar da za ka sami labari ba ko wani bayani ba wato “link”.

    Sau da yawa wannan yana hana mutane fahimtar asalin abinda aka yaɗa ko aka wallafa, sannan ya kan sa mutum ya yi sharhi na goyon baya ko akasin haka, ko ma ya yaɗa abinda ba shi ne ba.

    Abu mai mahimanci na gaba shi ne, mutane suna shiga abin da ba su da ilimi a kai. Wannan shi ne dalilin yin wannan rubutun. Sau da yawa babban malami zai yi bayani na ilimi mai zurfi a kan wani abu mai mahimmanci da ya shafi addini, a yaɗa shi ta hanyoyin sada zumunta, kwatsam sai ka ga wani matashi, ko wani ɗan tasha bai san dama ko hagu ba a kan abinda ya shafi ilimin addini, kawai sai ya ce wannan babban malamin nan “ƙarya” ya keyi, ko zai ci gyaran malamin.

    Ba don komai ba, kawai wannan hanya ta ba shi dama ya ga ko ya ji abinda wannan babban malamin ya faɗa. Wani babban abin takaicin shi ne shi, wannan matashi ko ɗan tashan ba zai iya kawo wata hujja na ilimi ba, sai soki-burutsu, jahilci da hayaniya.

    Misali ɗaya daga cikin misalai masu yawa shi ne mas`alar mutum ya ce ya saki matarsa da wasa ko da kuwa a shirin wasan kwaikwayo ne. Manyan malamai kamar Dr. Bashir Aliyu Umar, oon da Prof. Umar Sani Fagge sun yi fatawa a kan ce wa duk wanda ya aikata haka matarsa ta saku.

    Suka kafa hujja da hadisin Manzon Allah SAW ingantacce. Amma aka samu wasu waɗanda ba su wani abu na ilimin addini, kai wasu ma `yan tasha ne, suka rinƙa surutai na jahilci da rashin ladabi ga malamai da malanta da ƙoƙarin ƙaryata hadisin Manzon Allah SAW da molon ka.

    Ba abinda ya ba su wannan damar sai waɗannan hanyoyi na sada zumunta wanda suke ganin ilimi kamar abin banza da arhan malanta. Idan aka duba a baya za mu ga mas`aloli na addini, malamai da tsarekunsu su suke tattauna cikin girmamawa ta hanyar rubuce – rubucen ilimi.

    Amma yanzu saboda waɗannan hanyoyin na zamani sai a ci mutuncin malami, a zage shi, a faɗi munanan maganganu game da shi, ba tare da an kawo wata hujja ko wata magana ta ilimi ba saboda ba abin da za a iya faɗa da rashin ilimi.

    Sannan abu na biyu, wannan ya ba da dama kowa ya ga cewa zai iya zama malami saboda yawan yaɗuwar ilimin kayauta kuma cikin sauƙi. Kowa zai iya zama malami dare ɗaya. Wanda kuma ba haka ba ne, kuma ba ma zai yiwu ba.

    Abu na uku, waɗannan hanyoyin sun bai wa wasu `yan dagajin mutane damar yin sojan gona, su mai da kansu malamai, su tsoma baki a cikin abinda ya shafi ilimi, da ma faɗin duk abinda suka ga dama. Jahilai kuma suna nan birjik followers, masu sharing da masu like.

    Daga ƙarshe, waɗannan hanyoyin sun ba da gudumawa wurin yaɗuwar ilimi da wayar wa mutane kai game da addini, sannan a gefe ɗaya kuma sun ba da damar raina malamai da ilimi, rashin ganin girman ilimi da mahimmancinsa. Malamai sun zama ba komai ba, sannan malanta ta zama arha.

    Duk wanda baya ganin wanɗanda suke riƙe da tushen addininsa, (ilimi) da girma ta yaya zai ga girman addininsa? Gimama malamai yana daga cikin abinda zai sa mutum ya san daraja da girman addininsa.

    Whatsapp: 08039290267

    Karanta Malamai, Malanta Da Hanyoyin Sada Zumunta A Yau (1)

    Edita@rumasau-kallamu

  • Malamai, Malanta Da Hanyoyin Sada Zumunta A Yau (1)

    Malamai, Malanta Da Hanyoyin Sada Zumunta A Yau (1)

    Malam Imam Ahmad da sauran malaman sunan sun rawaito daga Abi Darda` (RA) ya ce: Manzon Allah SAW ya ce: “Lallai Malamai magada Annabawa ne, Su Annabawa ba su bar dinari ko dirhami ba, sai dai sun bar ilimi. Wanda ya yi riƙo da shi lallai ya yi riƙo da rabo babba”

    A cikin wannan rubutun duk inda aka faɗi malami ko malamai ana nufin malamin addinin musulunci wanda aka yarda da iliminsa da kuma tsoron Allahan sa. Irin waɗannan malaman su ne magada Annabawa, saboda suna yaɗa shiriya ga mutane (Wanda aiki ne annabawa). Ko kuma don su (malamai) suna ɗauke da wani abu (ilimi) wanda yake daga wurin Allah wanda aka samu ta hanyar Annabawa. Duk ɓangare biyun sun cancanci girmamawa.

    Malanta wata hanya ce da ta ƙunshi kyautata niyya, tsoron Allah, gwagwarmaya, haƙuri, jajircewa, ladabi da girmama wanda ake neman ilimi wurinsa, dan neman sanin abinda ya shafi addini, wanda ya ke ɗaukan lokaci mai tsawo. Duk mai neman ilimi yana ba da lokacinsa ne gaba ɗaya, ya lizimci malami, ya jajirce, tare da yi wa malami ladabi, da haƙuri ga duk abinda zai iya bijirowa ta ɓangaren malamin ko ta ɓangaren karatun ko yau da gobe.

    Duk wanda ya bi wannan hanyar, bayan wani lokaci ana sa ran ya sami wani abu na ilimi, har ma ya amsa sunan malami. Sanin kowa ne shi ilimi ba a daina nemansa kuma ba a iya ƙure samunsa. Sai dai mutum ya yi iya yinsa kawai. Sannan ba kawai don mutum ya sami ilimi shi ke nan ba, sai an cigaba da bincike, karatu da nazarce nazarce.

    A ƙarni na Sha-shida (16) a Arewacin ƙasar nan, Jami`ar Gobarau da kuma `yandoto ta Katsina sun zamo wurare da suka tara masana a kowani fanni na ilimi wanda manyan malamai daga duk faɗin nahiyar Afrika da ma wasu wuraren suke zuwa dan neman ilimi da ilimantarwa.

    Bayan jihadin Babban Malami, Shehu Usmanu Ɗan Fodiyo, cikin jama`ar Shehun malamin, manyan malamai irin su ƙaninsa, Abdullahi Ibn Muhammad Ibn Fodiyo (Abdullahin Gwandu), Malam Mustapha (Ɗan Tafa), Waziri Ɗan Laima da kuma irinsu ɗan Shehu Usman bin Fodiyo wato Muhammad Bello da ƙanwarsa Nana Asma`u da ɗanta Abdulkadir Ɗan Tafa da sauran manyan malamai sun yi ta ba da gudunmawa wurin karantar da mutane, rubuce rubucen littatafi da ƙasidu na ilimin addini, lugga da sauransu.

    Duk lokacin da aka sami tarin malamai a wuri, ko a lokaci ɗaya, sau da yawa akan sami wata mas`ala ta addini wadda za a iya samun saɓani a tsakanin malamai. Wannan yana faruwa ne sakamakon yawan bincike a kan mas`aloli na addidni daban daban da malamai su ke yi. Sabani ba wani abu ba ne da zai sa a ta-da jijiyar wuya ko a ɗau makami, tun da su masu ilimi ne, toh a ilmance ake komai ta hanyar rubuce rubucen ƙasidu, littattafai da wasiku da fitar da fatawa.

    MISALAI GUDA UKU KAƊAI DAGA MAGABATA.

    Misali na farko shi ne: Lokacin da Turawan mulkin mallaka suka shigo yankin Arewa, Sarakunan mu na musulunci sun ƙi miƙa wuya, kamar yadda turawan suka nema. Da yawa sun zaɓi su yaƙi waɗannan turawan.

    Sarkin Muslumi Attahiru I da sanyin safiyar ranar 15 Maris 1903 bayan an gwabza tsakanin jama`arsa da turawa na kimanin sa`o`i biyu, sai ya fahimci yaƙi da turawan nan babu nasara, saboda a ƙalla an kashe mutane kusan 100 cikin mutanen sa, a ɓangaren turawa ko mutum guda ba a kashe ba, saboda bindigogi na zamani da suke amfani da su a wancan lokacin.

    Ganin haka, ya yanke shawarar yin hijira zuwa gabas, bayan ya yi shawara da wasu daga cikin muƙarrabansa. A ranar 27 Yuli, 1903 aka yi yaƙin ƙarshe a wani gari da ake kira Burmi ranar Juma`a Sarkin Musulmi Attahiru I da kusan mutane 600 suka yi shahada a cikin masallacin juma`a. Wannan jajircewa da Sarkin musulmi da yayi, ɗaya daga cikin sojojin taurawan Ingila William Wallace ya tabbatar da haka.

    Ba tarihin Sarkin Musulmi Attahiru I zan bayar ba, amma ana cikin wannan taƙaddama bayan fitar Sarkin musumi daga birnin Sakkwato ranar 21 Maris, 1903 aka zaɓi Muhammad Ibn Ali Ibn Bello (Attahiru II) a matsayin sarkin Musulmi. A wannan lokacin Wazirin Sokoto Muhammadu Buhari ya nemi fatawa a wurin Alkalin Gwandu Ahmad Bin Sa`id kan maslaha ga musulmi; A miƙa wuya wa turawa, ko a ci gaba da yaƙarsu ko a yi hijira? Wanda wasu suna ganin ba bu wata maslaha da ta wuce a miƙa wuya wa turawa kawai.

    Wannan fatawa ta a miƙa wuya ta samu karɓuwa sosai musamman dalilin takardar da Wazirin Sokoto Muhammadu Buhari ya yi “Risalatil Wazir Ila Ahlil Ilmi Wat Tadabbur” ta yadda suka yi amfani da ilimin usul wurin bayanin hukuncin abinda ya kamata shugabannin musulmi su yi na miƙa wuya da yarda da turawan mulkin mallaka. Akwai waɗanda suka saɓa musu a ra`ayi suma da hujjojinsu, amma cikin rubuce rubuce na ilimi kowa ya fito da hujjarsa, ba hayaniya ko zage –zage da cin mutunci.

    Misali na biyu: Shi ne Lokacin da aka sami taƙaddama kan saka karatun Qur`ani a gidan rediyo a 1955 zuwa 1960 wanda Sheikh Ibrahim Nyass ya ba da fatawar ya halatta a sa karatun Qur`ani a gidan rediyo, shi kuma Sarkin Zazzau Malam Jafaru Ɗan Isyaku ya ba da fatawa sɓanin haka.

    Dukkansu (Sheikh Ibrahim Nyass da Sarkin Zazzau Malam Jafaru Dan Isyaku) kowa ya yi amfani da ilimi mai zurfi na Usulul Fiqh da hujjoji masu ƙarfi wurin bayanin hukuncin wannan mas`ala. Sheikh Ibrahim Nyass ya ba da fatawarsa ne sakamakon tambaya da wasu daga cikin malaman Kano suka yi masa. Sarkin Zazzau Malam Jafaru Ɗan Isyaku ya ba da nasa fatawar ne sakamakon tambayar da Sarkin Kano Malam Muhammadu Sanusi I ya tura masa duk da cewa shi ma Sarkin Kano Malam Muhammadu Sasusi I babban malami ne.

    Abin sha`awa a nan shi ne Shiekh Ibrahim Nyass har wani littafi ya yi wanda aka buga shi a shekaran 1956 a ƙasar Masar mai suna “Alhujja albaligha fi kawn Idha`at alQur`an fir radiyo Sa`igha”. Wannan mas`alar ita ma haka aka ƙarƙareta ta hanyar ilimi ba hayaniya da harigido.

    Misali na uku, a ƙarni na 19, an sami taƙaddama a kan Sadalu da Qabalu a sallah, wannan taƙaddama ta samo asali ne saboda bayyana da yaɗuwar tajdidin ɗarikar Tijjaniya da Sheikh Ibrahim Nyass ya kawo wanda kafin zuwan wannan tajdidi, ɗarikar Ƙadiriyya ita ce aka fi sani kuma ta fi daɗewa a ƙasar Hausa tun bayan jihadi.

    Malaman ɗarikar Kadiriyya sun tafi a kan sadalu cikin sallah. Sheikh Ibrahim Nyass da wasu malamai a Kano suka zo suka warware wancan fahimta ta sadalu da hujjoji. Wannan ya sa `yan Kadiriyya suke ganin `yan Tijjaniya sun zo da wani sabon abu har aka riƙa kiran `yan Tijjaniya masu bin wannan fatawar da “`Yan Ƙabalu”

    Shehunan malamai irin su Malam Muhammadu Salga (r. 1938), Malam Tijjani Usman Zagon Barebari (r.1970), Malam Shehu Maihula (r1988) da sauransu sun yi rubuce rubuce dan tabbatar da ingancin yin ƙabalu a sallah. A ɗayan ɓangaren na Qadiriyya wanda Malam Nasiru Kabara ya ke jagoranta sun yi na su rubuce rubuce kan ingancin yin sadalu a sallah.

    A nan ma wani abin sha`awa, shi ne duk rubuce rubuce na ilimi aka rinƙa yi, har yau waɗannan rubuce-rubuce suna nan. An sami irin wannan taƙaddama ta faru a sokoto har Malam Abubakar Atiku Gwandu (r. 1913) ya rubuta wani littafi mai Irshad al-ikhwan ila bayan hukm as-salat bis-sadlu wa al-kablu.

    A kwai misalai masu yawa kan taƙaddama ko saɓani da ake samu tsakanin malamai tun tuni, amma abin zai birge ka idan ka kalli hanyar da ake bi wurin bayyana ra`ayi da hujjoji da fito da komai fili, hanya ce ta rubuce rubuce na ilimi, ba soki burutsu da hauragiya da shirme ba. Kuma malamai su suke kayansu ba kowani kare da doki ba. Hargowa da hayaniya da shiga fagen ilimi daga ko wani kare da doki ya samu asali ne dalilin yaɗuwar hanyoyin sada zumunta.

    Wanda shi ne za mu tattauna a rubutu na gaba.

    Rabiu Musa Adam

    Whatsapp: 08039290267

    September 12, 2025

    Karanta Ayyukan Ta’addancin Matasa A Kano: Aure, Yawan Haihuwa Da Tarbiyya A Wata Mahanga

    Edita@rumasau-kallamu

  • Ayyukan Ta’addancin Matasa A Kano: Aure, Yawan Haihuwa Da Tarbiyya A Wata Mahanga

    Ayyukan Ta’addancin Matasa A Kano: Aure, Yawan Haihuwa Da Tarbiyya A Wata Mahanga

    Ku yi auren soyayya, sannan ku auri masu haihuwa, zan yi alfahari da yawanku ranar tashin kiyama”

    – Manzon Allah (SAW)

    SHIMFIƊA

    Tun da Allah ya tsara zamantakewar al`ummomi, ya ƙaddara samun masu bijirewa tsarin zamantakewa. An sami masu bijirewa Annabawa wajen bin dokokin Allah, ana kuma samun masu bijirewa tsarin rayuwar jama’a kamar ɓarayi da sauran masu aikata laifuka daban daban.

    Babban dalili a nan shi ne abinda Allah ya ba mu labari na ‘ya’yan Annabi Adam (Habila da Qabila). Wannan abin da Allah ya ƙaddara ba hujja ba ne game da ayyukan ɓarna a cikin al’umma, dan Allah da kansa ya zargi wanda ya yi kisan kai cikin ‘ya’yan annabi Adam da kuma irin uƙubar da aka tanadar masa.

    Thomas Hobes a cikin nazariyyarsa ta kasa- jama’a da ke rayuwa a wuri ɗaya- ya na ganin dole a samar da shugabanci mai ƙarfin iko ta yadda duk wani mutum –ɗan ƙasa- zai miƙa wuya kuma ya ba da duk wani haƙƙi nasa ga shugabancin da zai kare shi daga dukkan ta’addancin wani ɓata-gari.

    Hobes ya nuna cewa idan aka bar mutane kara zube, ba tare da wani shugabanci ba, toh kowa zai yaƙi kowa ta yadda rayuwa za ta zama, mummuna, gurɓataciyya, taƙaitacciya mai cike da tsoro da tashin hankali. Sai ya ce, don a kare mutane daga wannan yanayi dole ne sai an samar da shugabanci mai ƙarfin iko don tabbatar da doka da oda da kuma samar da zaman lafiya da kwanciyar hankalin jama’a.

    Duk da wannan nazariyya ta Hobes ta samu ƙalubale da ga wasu manazarta, amma dai tana da madogara mai ƙarfi. Idan muka dubi yanayin zamantakewar al’umma a yanzu, duk lokacin da aka ce ba idon hukuma a guri, toh sai ka ga ɓarna ta samu gindin zama, maɓarnata sun samu dama, jama’a kuma su shiga halin ɗar-ɗar, zullumi da tsoro.

    Karamin misali, a watan Oktoba, 2020 lokacin da aka yi zanga-zangar end sars, a jihar Legas akwai lokacin da aka janye jami`an tsaro na ɗan wani lokaci a wasu wurare don kare rayukansu, jama’a da yawa sun shiga halin zullumi saboda ƙaruwar ayyukan ta’addanci a waɗannan unguwanni, har sai da ta kai jama’a sun fara kira ga gwamnati da a taimaka a dawo da jami’an tsaro musamman `yansanda.

    Wannnan yana tabbatar da ce wa duk lokacin da aka rasa tasirin hukuma, toh lallai jama’a za su shiga cikin halin tsoro da barazar ayyukan ‘yan ta’adda da ɓata-gari. Wannan ba wai a irin ƙasashen mu na Afrika ba ne kaɗai, har da ƙasashen da suka ci gaba sosai. An ga irin abinda ya faru a Los Angeles na ƙasar Amurka a cikin wannan watan har sai da ta kai an sa dokar ta ɓaci a birnin, aka kuma tura sojoji masu yawa don kwantar da zanga-zanga da ta rikiɗe ta koma tarzoma.

    AURE, YAWAN HAIHUWA DA TARBIYYA

    Bazan faɗaɗa magana a wannan ɓangaren ba, amma zan yi tsokaci. A kwanakin nan, ayukan ɓata gari da ta’addanci na matasa ya yawaita a birnin Kano, musamman abinda ya shafi faɗan daba, kisan kai da ƙwacen waya. Mutane a shafukan sada zumunta musamman facebook- wanda shi na fi bibiya- suna ta rubuce-rubuce game da lamarin. Amma abinda na ga mutane sun raja’a a kansa shi ne yawaitar aure da haihuwa tsakanin al-unmmar mu da kuma rashin baiwa ‘ya’ya tarbiyya. Zan ɗauki kowanne cikin abubuwa ukun in yi magana a kai a taƙaice.

    Yawaitar aure, ni a fahimtata ba ita ce matsalar ba kai tsaye, domin yawaita auren shi ma yana da nasa matsalar wadda ta ke da alaƙa da ƙaruwar bata-garin matasa. `Yan mata sun yawaita, zaurawa ma haka, idan ba a yawaita aure ba, lallai zinace -zinace zai yawaita, ta hakan kuma za a yi ta haifar ‘ya’yan da ba su da iyayen da za su ɗauki nauyin su ko su ba su tarbiyya- an koma gidan jiya.

    Na biyu yawaitar haihuwa, shi ma ba laifi ba ne, saboda ai mun san gidaje a Kano waɗanda ‘ya’ya kawai sun kai talatin, arba’in ko ma sama da haka. Wasu ma dalilin ‘ya’yan suka sami ɗaukaka. Amma na tabbata idan da za a tambayi matasan nan masu aitaka ɓarna su nawa ne a gidan su, zai yi wahala a ce mafiya yawansu su kai ashirin, talatin ko arba’in, wasu ma su biyar ne ko uku ko ma shi kadai ne.

    Ba na goyon bayan haihuwa ba tsari, musamman a wannan yanayin da ake ciki na matsi, mutum ya san abinda ya kamata na yadda zai kula da haƙƙin da Allah ya ɗora masa, sannan ya sani Allah zai tambaye shi game da ‘ya’yansa. Idan bai kula da haƙƙin da Allah ya ɗora masa ba, ya san abinda zai biyo baya a gaban Allah.

    Tarbiyya, wacce ita ce muhimmi, kuma babban abin. Ko da ɗa ɗaya ne Allah ya baiwa mutum, idan bai tsaya da gaske ya ba shi tarbiyya ba, toh sai ya gagare shi kuma sai ya zamar wa jama`a fitina. Amma duk yawan ‘ya’yan mutum, da taimakon Allah idan ya tsaya da gaske ya ba su tarbiyya, toh sai ka ga sun zama masu mafani a cikin al`umma waɗanda ake alfahari da su.

    Tarbiyar nan fa, ba wai samar da abinci ne ko abin sha da tufafi ba kaɗai, ya haɗa har da ɗabi’u da halayyar uba da uwa su kansu, da kula da abokansa da waɗanda ya ke mu’amala da su, inda yake zuwa da sauransu. Babu yadda za a yi uba ya zama maƙaryaci, mai nuna rashin gaskiya mai zalintar iyalinsa kuma ya sa ran ɗansa ba zai zama haka ba.

    A yanzu iyaye sun ɗauka tarbiyya aikin su ne su kaɗai, ba ruwan kowa da ‘ya’yansu, kada wani ya yi katsalandan cikin aikinsu, ko yaya kusancin sa ya ke da su. Toh iyaye su sani, tarbiyyar ‘ya’ya ba aikin mutum ɗaya ba ne, aikin mutane ne da yawa, aikin iyaye ne su biyun, aikin malamai ne (malam makarantun ‘ya’ya), aikin maƙota ne, aikin ‘yan’uwa ne da abokan arziƙi.

    Duk lokacin da iyaye su ka kasa gane haka, toh su sani suna aikin banza ne kawai, suna yin abinda suke yi ne sauran mutanen kuma su na warwarewa. Saboda haka sai iyaye sun yarda cewa tarbiyar ‘ya’ya na kowa da kowa ne, kowa yana da gudumawar da zai bayar daga cikin waɗanda aka faɗa a baya.

    Wannan shi ne yanzu abin da ya ke cutar iyaye saboda son ‘ya’ya kuma shi yake kawowa taɓarɓarewar tarbiyyar ‘ya’ya don ba wanda zai taya ka abinda ba za ka iya yi kai kaɗai ba. Tarbiyya ba za ta samu ba idan masu taimakawa wajen tarbiyya suka zura wa iyaye ido game da ‘ya’ya ko da kuwa sun ga abinda zai cutar da ‘ya’yan ko zai cutar da iyaye.

    ZAMANTAKEWA DA TARBIYYA

    Yanayin zamantakewar mu a yanzu ya canza daga zamantakewa na Bahaushe da aka sani zu wa zamantakewa na ‘yan bariki. Rayuwa ta ba ruwa na da kai, ba ruwan ka da ni, ba ruwanka da gidana da ‘ya’yana ba ruwana da gidanka da ‘ya’yanka. Ya’yanka ‘ya’yanka ne, nawa nawa ne. Duk abinda na ga ‘ya’yanka suna yi ba abinda ya shafe ni ba ne, haka kai ma.

    Wannan ba zamantakewa ne ta al`adar Bahaushe ba. Addinin musulunci da tarbiyya duk ba su yi koyi da haka ba. Idan ana so a gyara tarbiyar ‘ya’ya dole sai an canza wannan zamantakewar ta bariki. A dawo duk abinda ya shafi ɗaya ya shafi kowa. Sannan a canza zaman munafunci zuwa zaman amana da mutunci, zaman amana shi ne a faɗa wa kowa gaskiya komai ɗacinta ta hanyar da ta dace, idan ta kama a tilasta masa game da wata maslaha na zamantakewa dole ne a yi masa haka don gyara.

    Babban abin yi kafin a sami wannan gyara na zamantakewa sai al`umma ta dawo da ga rakiyar gabatar da abin duniya a kan mutunci da dattaku. Ya zama masu dattaku da mutunci su ne iyaye, su ne jagorori su ne masu faɗa a ji a cikin unguwanni, girmama na gaba a cikin al`umma. Da dai sauran abin da ya kamata.

    Samun manyan mutane masu mutunci da dattaku a cikin al`umma ya na nuna cewa al’umma tana da na gaba waɗ anda za su iya hanawa a hanu ko su sa a yi ayi. Idan da waɗannan a cikin al`umma tarbiyya za ta gyaru daga sama har ƙasa. Duk al’umar da ta zama ba babba, ba dattijo mai faɗa a ji a cikin ta, toh ta kamar hanyar halaka, taɓewa da lalacewa.

    Waɗannan matasa sun zama haka ne saboda tun suna ƙanana ba wanda yake faɗa musu su ji har suka zama abinda suka zama yanzu ba wanda ya isa ya faɗa musu su ji. Tasirin mai faɗa a ji (dattawa) a cikin al`umma ya fi na jami’an tsaro, saboda dattawa za su iya daƙile faruwa duk wani abu kafin ya faru ta hanyar tsawatarwa tun daga layi zuwa unguwanni. Al’ummar mu yanzu muna fama da rashin manya dattawa a cikin mu, ba wai babu su ba ne, akwai su, sai dai mu ne ba ma girmama su, ba ma ganin kimarsu da darajarsu.

    RUFEWA DA SHAWARWARI

    Ayyukan daba da ƙwacen wayoyi ya fara zama ruwan dare a Kano, abin kullum yana ƙara tsamari, mutane kullum suna cikin zullumi da tsoro a lokutan da suke cikin harkokin su na yau da kullum. Sau da yawa ɓata-gari suna kashe mutane masu mutunci da kamala (masu aikin yi da iyali) wannan ba ƙaramin abin ta-da hankali ba ne, sannan yana ƙara yawan ɓata-gari da zaman banza a fakaice.

    Shawo kan mastalar faɗan daba da ƙwacen wayoyi a Kano ko ma kawo ƙarshen sa, dole ne sai gwamnatin jiha da jami’an tsaro sun tashi tsaye sosai don daƙile waɗannan ayyukan kafin abin ya kai wani yanayi, duk da akwai ‘yan matsaloli, amma za a iya shawo kansu.

    Abu na gaba, dole a samar da kwamitocin dattijai a unguwanni don tsawatarwa iyaye da ‘ya’ya kan duk abinda suka gani ba dai dai ba da ma ɗaukan mataki idan hakan ya kama. Masu hannu da shuni a unguwanni su samar da gidauniya na tallafa wa marasa galihu da sana’a ko karatu.

    A sami kyakkaywan haɗin kai daga mutanen unguwa, duk da ana samun waɗanda ba sa ba da haɗin kai, dole a taka musu birki don kar su yi zagon ƙasa ga tafiyar. Idan ta kama a ɗau mataki a kansu ma ba laifi ba ne don cimma abin da ake buƙata.

    Kiran waɗannan matasan da zama da su, jan hankalinsu, yi musu nasiha da nuna musu illar ayyukan su nan duniya da lahira. Jan su a jiki da nuna muhimmancin su a cikin al’umma, kwaɗaitar da su irin dammamakin da ke gaban su da irin abin da za su iya zama nan gaba.

    June, 15th 2025

    Don karanta Wasu Daga Dalilan Shaye-shayen Ƙwayoyi danna nan

    Edita@rumasau-kallamu

     

     

     

     

     

     

     

     

     

  • Matasa

    Matasa

    Allah SWT ya ce:
    “Lallai su matasa ne, sun yi imani da ubangijinsu sai muka kara musu shiriya”

    MATASHIYA: WANENE “MATASHI”
    Majalisar ɗinkin duniya dangane da abinda ya shafi shekaru, ta faɗi waye matashi. “Matashi shi ne wanda bai yi ƙasa da shekara goma sha biyar ba kuma bai wuce shekara ashirin da huɗu ba”. Idan muka dubi yanayi, cimaka da yankuna na duniya, za mu ga banbanci tsakanin masu waɗannan shekaru a zubi, yanayin girman jiki, wayewa, ilimi har ma da tunani.

    Haka ma abin da ya shafi dokokin ƙasa zuwa wata ƙasar, za mu iya samun bambance banbance na masu waɗannan shekaru. Misali wasu ƙasashe daga shekara 18 shi ne matashi yake samun damar yin zaɓe ko izinin zaman kansa. A ƙasashe kamar Koriya ta Kudu, sai matashi ya kai shehara goma sha tara ko ma ashirin.

    Tarayyar Afrika a nata ɓangaren, ta bayyana matashi shi ne wanda ya ke tsakanin shekara goma sha biyar zuwa talatin da biyar. Daga shekara goma sha biyar ɗabi’a, tunani da wasu halayyar mai wannan shekaru sukan canza.

    Mai waɗannan shekaru yana taka wasu matakai masu mahimmanci a rayuwa, wanda ake buƙatar a kula sosai, sannan shi kansa matashi ya kula da su, ya yi ƙoƙarin yin amfani da su dan cin moriyar su nan gaba. Wasarairai da su da yin abin da ba shi ya dace ba a wannan lokacin ya na sanya mutum babbar nadama bayan shekarun sun wuce.

    MATSAYIN MATASHI A WANNAN LOKACI A NAJERIYA

    Najeriya ta na da tsare tsare masu kyau game da matasa amma a rubuce kawai. Kamar sauran ƙashashen duniya masu tasowa musamman na Afrika da Asiya. Gwamnatoci ba su fiye damuwa da abin da ya shafi matasa ba, ko dai saboda rashin sannanin mahimmancin su, gudumawarsu a gina al’umma da ci gaban ƙasa, ko kuma dan wani dalili na ƙashin kansu na siyasar su ta cikin gida.

    Matashi a wannan ƙasa kusan shi ya ke tanadar wa kansa da kansa duk wani abu na gina rayuwarsa. Hukumomi ba sa ba da mahimmanci sosai dangane da abinda ya shafi wannan ɓangaren. Misali, abinda ya fi komai mahimmanci a rayuwar matashi babu kamar ilimi. Makarantun mu na sakandire kowa ya san hali da yanayin da suke ciki, babu wani kyakkyawan tsari da zai ƙarfafa gwiwar ɗalibi don zamowa wani abu nan gaba. Makarantun sakandire sun zama madakata ga da yawa daga cikin matasa musamman ‘ya’yan talakawa waɗanda ba sa iya karatu a makarantun kuɗi.

    Matasa sun gama sakandire amma sun faɗi jarabawar gamawa, babu wani tanadi da hukumomi suke da shi na yadda za a yi da waɗannan matasan, daga nan sai su kiɗime, su rasa yadda za su ci gaba da rayuwa ga kuma buri. Wannan ya ke janyo wasu su fara shaye shaye don rage raɗaɗin zaman banza da yawon banza, wasu kuma su faɗa ayyukan ɓarna na yau da kullum. Kaɗan ne ake samu su nemar wa kansu sana’a don dogaro da kai.

    A halin yanzu, ina makarantun mu na vocational da technical, suna nan, amma an yi watsi da su. A Arewa tun 1909 aka buɗe makarantar koyar da sana’a a Nasarawa inda ake koyar da saƙa, aikin kapenta da sauransu. A 1946 an sami bunƙasar wuraren koyar da sana’o’i inda aka buɗe wurare har goma sha huɗu a Arewa.

    Na kawo wannan ne don kawai in nuna yadda makarantun koyar da sana’a suke da mahimmanci a da da yanzu. Za a iya amafani da waɗannan makarantu wurin saitawa da inganta rayuwar matasa a wannan ƙasa, don ba su damar komawa waɗannan makarantu in ba su sami damar yin nasara a jarabawar gama sakandire ba don su koyi san’a don dogaro da kai da kuma ɗauke musu kewar zama da yawon banza.

    IRIN TANADE-TANADEN DA YA KAMATA A YI WA MATASHI:

    Hukumomi a Najeriya suna da tanade-tanade masu yawa da inganci game da matasa a wannan ƙasa, amma ba a ba su mahimmanci wurin aiwatarwa, saboda wasu dalilai na shugabanni. Wani lokaci ana kallon aiwatar da waɗannan tanade-tanade da ba abin da za a iya ganin alfaninsu ne a yanzu yanzu ba. Su kuma ‘yan siayasa abin da suke so, shi ne sha yanzu magani yanzu, a gani a ƙasa don yaɗa manufofinsu da ɗorewar siyasar su.

    Akwai tanade-tanaden da hukumomi suke da su na ilimantar da matasa, koya musu sana’o’i da abinda ya shafi wasanni. Abin da ya shafi ilimi da koyar da sana’o’i kullum hukumomi da ‘yan siyasa suna yin abinda za su iya, amma dai bai taka kara ya karya ba.
    Abin da ya shafi wasanni shi ne har yanzu kamar an bar mu a baya musamman a nan Arewa.

    A yanzu duk da addini da al’adar mu suna da tasiri mai yawa a rayuwar mu ta yau da kullum, amma dai a yanzu duniya ta ci gaban da ya kamata a ce mun tsunduma cikin abinda ya shafi wassani da motsa jiki wanda yanzu ya zama sana’a mai tagomashi a duniya. Banda ƙwallon ƙafa, akwai wasanni kamar ƙwallon kwando, ƙwallon hannu, ƙwallon raga, table tenis, badminton, guje guje, tsalle –tsalle, kokawa, iyo da sauran wasanni da ake gudanar da su ƙarƙashin kulawar hukumar wasanni ta duniya wato (Olympics).

    A shekarun nan matasa ‘yan ƙalilan da sunayensu suka fito fili daga Arewa waɗanda suke buga ƙwallon ƙafa a duniya, an ga yadda suka samu ɗaukaka. Amma sauran ɓangarorin wasanni an yi buris da su, da ƙyar za ka sami ‘yan Arewa a sauran wasanni da na ambata a sama.

    Idan hukumomi da ‘yan siyasa za su bai wa sauran ɓangarori na wasanni kulawa ta yadda za a samar da wuraren horar da matasa waɗannan wasanni, kamar yadda a Kano ɗaya daga cikin gwamnatocin da suka wuce aka gina makarantar horarwa kan wasanni. Faɗaɗa tunani wurin samar da ƙwararrun masu horar da wasanni iri–iri, a riƙa nemo matasa masu baiwar waɗannan wasanni ana ba su horo na musamman, sannan hukumomi su taimaka musu wurin shiga gasar wasanni na cikin gida da kuma na ƙasa da ƙasa.

    Wannan wani tanadi ne mai kyau da zai rage wa matasa zaman banza, sannan za a samar musu da wani abin yi wanda ba lallai sai sun yi karatu mai zurfi ba, zai ba su dama su riƙe kansu da ‘yan uwansu ta hanyar abin da suke samu na kudade. Ƙari a kan haka shi ne, sauran matasa za su yi sha’awar waɗannan wasanni dan abinda suka ga ‘yanuwansu suka zama. Idan ba a manta ba akwai wata matashiya Tobi Amusan da ta lashe gasar tseren mita 100 a shekaran 2022.

    Wannan abinda ya shafi wasanni an kawo shi ne a babin misali kawai, amma akwai damammaki da yawa da hukumomi suke wasarairai da su wanda zai ba wa matasa dama mai yawa a rayuwarsu don zama wani abu nan gaba ba tare da dogaro da gwamnati ba.

    ABIN DA MATASHI YA KAMATA YA YI WA KANSA

    A ƙashashen da suka ci gaba, hukumomi su suke yi wa matasa tanadi tun farko don a ɗora matashi a kan hanya, a ba shi ilimi mai kyau, a ba shi dama na koyon sana’a da sauransu. Amma a ƙasashen mu masu tasowa kamar yadda na faɗa, abin ba haka yake ba. Toh shin matashi don bai samu waɗannan tande-tanaden ba sai ya zauna ya kashe kansa da kansa yana ji yana gani? Shekarun samartaka wasu shekaru ne da yake bai wa wanda yake wannan mataki damammaki waɗanda ba su da iyaka.

    Matashi yana da ƙarfin jiki, lokaci da ƙarancin tsoro, wanda ba a wannan shekarun yake ba yana da ƙarancin waɗannan abubuwa. A wannan shekarun matashi ji yake kamar ya ɗau duniya a ka saboda ƙarfin da yake ji jikinsa, ba wasu nauyi na yau da kullum a kansa da zai cinye masa lokaci, kamar hidimar iyali. Sannan matashi yana da ƙaracin tsoron yin duk abinda ya ke so, zai iya yin tafiye-tafiye masu nisan gaske, zai iya shiga ko yin duk wani abu mai haɗari ba tare da yin dogon tunani ba.

    Waɗannan su suke bai wa matashi damar zama wani abu a rayuwarsa. Idan mutum ya girma ƙarfinsa ya fara ƙarewa wasu abubuwan ba zai iya yin su ba, lokacin sa kuma na aikinsa ne ko sana’arsa da kuma iyalansa, sannnan tsoron abinda zai iya kai wa ya komo. Misali tsoron mai zai faru ko wani hali iyalansa da ‘yanuwansa za su shiga idan ba ya nan duk waɗannan suna daƙile wanda ba matashi ba.

    Ɗaya daga cikin manyan abubuwa da Najeriya ta ke da shi wanda ƙasashe da yawa babu, shi ne, duk ɗan Najeriya zai iya zama komai a ƙasar nan, abin nufi a nan, shi ne duk abin da kake so ka zama a Najeriya za ka iya zamowa, misali zama babban ɗan siyyasa, attajiri, babban jami’in gwamnati da sauransu.

    Kullum muna gani waɗanda ba ‘ya’yan kowa ba, kuma su kansu ba kowa ba, suna zama manyan mutuane a ƙasar nan, ba za ka taɓa samun haka ba a wasu ƙashashe. A waɗannan ƙasashen idan ka taso a gidan takalawa, a haka za ka girma ka gama rayuwarka a wannan layin. Babu tsallake zuwa wani layin, wato abinda ake cewa “social mobility”.

    Saboda haka, wannan dama ce mai kyau ga duk wani matashi da ya taso a Najeriya da ya yi ƙoƙarin samun ilimi ko da ba mai zurfi ba ne, ya sami sana’a ya riƙe, musamman idan a gidan su akwai sana’a, kada ya raina ta duk ƙanƙantar ta. Yanzu zamani ya canza za a iya zamanantar da duk wata sana’a, a tallata, kambama ta. Kada matashi ya kallafa wa kansa sai ya sami aikin gwamnati a yanzu, kada kuma ya yaudaru da abinda wasu suke samu ta hanya mara kyau a gwamnati.

    Matashi ya rage wa kansa dogon buri. Duk arziƙin da Allah ya ƙaddara wa mutum sai ya same shi a duniya. Shi arziƙin ɗan Adam ana rubuta masa shi tun yana cikin mahaifiyarsa. Kamar yadda ya tabbata a hadisin Manzon Allah SAW da ga Abdullahi ibn Mas`ud, Bukhari da Muslim suka fitar da shi. Sannan babu wanda zai mutu har sai arzikinsa ya same shi, babu wanda ya isa ya tare masa shi.

    Kawai a daure a nema ta hanyar halas, kada matashi ya yi gaggawar neman arzikinsa ta hanyar haramun. Manzon Allah SAW ya ke cewa, “Mala’ika Jibril ya faɗa min cewa babu wata rai da za ta mutu face ta sami arziƙin gaba ɗaya sannan kuma sai ta kai ajalinta. Ku ji tsaoron Allah ku kyautata nema. Kada ɗayan ku ya yi gaggawar neman arziƙinsa ta hauyar haram.

    Kawai matasa ku tashi ku nema, Allah zai bayar. “Waɗanda suka yi gwagwarmaya za mu shiryar da su kan tafarkin mu, lallai Allah ya na tare da masu kyautatawa”

    January 17th, 2025.

    Danna nan don karanta Biyayya Ga Mahaifa

    Edita:@rumasau-kallamu

  • Biyayya Ga Mahaifa (Iyaye)

    Biyayya Ga Mahaifa (Iyaye)

    “Sannan mun yi wasiya ga mutum da ya kyutata wa mahaifansa, mahaifiyarsa ta yi goyon cikinsa cikin wahala sannan ta haife shi cikin wahala…” (Q 46:15)

    Wata rana cikin watan satumba na shekarar 2024 na je jihar Legas ɗan halartar wani horon aiki. Bayan na isa ne, na hau motar haya dan ƙarasawa inda zan halarci horon, da yake da safe ne, a kan hanyar mu sai na hango wani yaro ɗan makaranta da bai wuce shekara goma (10) ba da mahaifiyarsa a gefen titi suna jiran abin hawa, mahaifiyar tana ta gyara wa yaron takalminsa da safarsa, sannan tana ta ƙoƙarin shafa masa wani abu kamar man shafawa, a zato na yaron ne ya shafa man shafawan amma bai yi yadda ya kamata ba, mahaifiyar take gyara masa.

    Duk wannan abin da mahaifiyar ta ke yi, yaron yana tsaye kamar ba da shi ta ke ba. Wannan abinda ya faru ya sani tunani sosai game da lamarin iyaye da ‘ya’ya.
    Allah maɗaukakin sarki saboda girmama sha’anin iyaye bai taƙaita lamarinsu ga masu Imani ko musulmi kaɗai ba, za mu iya fahimtar haka ne a ayar da take cikin Suratul Ahkaf, aya ta 15 in da Allah ya yi kira ga “mutum” kowa da kowa ke nan, ba wai wasu gungun mutane na musamman ba.

    Kalmar da Allah ya yi amfani da ita na “mutum” ya ƙunshi musulmi, mumini, fasiƙi, munafiki, kafiri da duk wani jinsi na mutum, sannan ya umurce shi da ya yi wa iyayensa biyayya. Biyayyar iyaye ana buƙatar ta ne daga duk wani mutum. Mahaifiyar da na gani da ɗanta, daga yanayin shigarta babu alamar musulma ce, amma ku dubi yadda ta ke yi wa ɗan ta. Shi ya sa Allah a aya ta 23 ckin Suratu Isra’i, ya yi kira ga mutum da ya bauta masa, ya kuma jingina hakan da yi wa iyaye biyayya.

    Kira zuwa ga bautar Allah kira ne ga kowa da kowa, toh haka ma kira zuwa yi wa iyaye biyayya ta shafi kowa da kowa. Iyaye suna yin duk abinda za su iya ne wurin su ga sun kyautata rayuwar ‘ya’yan su a nan gaba, suna ƙarar da ƙarfinsu, abinda suke da shi, su na haƙura da jin daɗinsu, su ma sa kansu a wahala don kyautata rayuwar ‘ya’yansu, idan ta kai su rasa rayuwarsu ma iyaye a shirye suke su rasa rayuwar su don ‘ya’yansu. Babu wanda zai iya yin wannan in ba iyaye ba. Duk waɗannan abubuwa ba su taƙaita ga wani mai addini ba, duk an haɗu a kan wannan babban lamarin.

    A aya ta takwas cikin suratul ankabuut Allah ta’ala cewa ya yi “ mun yi wasiya ga mutum da ya kyautata wa iyayensa, da za su yi maka umarni da ka yi shirka da Ni kan abinda ba ka da ilimi, toh kada ka yi musu biyayya (kan wannan umarnin na yin shirka)” A wannan ayar ma Allah kai tsaye ya kira mutum bai ware wani ba, sanan ya ba da wasiyar yi wa iyayye biyayya da kyautatwa.

    Ya kuma nuna ko da kuwa iyayen nan kafirai ne, ba a bai wa mutum dama ya saɓa musu ba. Idan iyaye waɗanda ba musulmi ba, suka umurci mutum da ya yi shirka da Allah, toh sai ya ƙi musu biyayya kan wannan umurnin na yin shirka da Allah, amma haƙƙin biyayya yana nan a wuyan sa dole.

    Wannan ayar tana ƙara nuna mana ce wa iyaye ko suna saɓa wa Allah, to wajibi ne a yi musu biyayya a dukkan ɓangarori na rayuwarsu. Inda kawai ba za a yi musu biyayya ba shi ne inda su ka yi umarni da a saɓa wa Allah. A abin da ya shafi biyayya wanda yake kan kowane mutum, Allah ne a gaba, sannan iyaye ba tare da babancin imani ko rashin sa ba.
    Iyaye wasu mutane ne na musamman da Allah ya zaɓa kuma ya fifita, ba wai dan haihuwar mutum da suka yi ba kaɗai, har ma da irin gudumawar da suka bayar a cikin rayuwarsa.

    Shi yasa a hadisin Manzon Allah SAW wanda Amr bin Shu’aib daga Babansa daga Kakansa ya ce wani mutum ya zo wurin Manzon Allah SAW ya ce: Mahaifina yana da buƙata da dukiyata, sai Manzon Allah SAW ya ce: “kai da dukiyarka duk na mahaifinka ne” Wannan ya ƙara tabbatar mana da matsayin iyaye a wurin mutum, ba wai ma shi kansa kaɗai ba har ma abinda ya mallaka na iyayensa ne, suna da damar yin abinda sukaga dama a ciki.

    Amma yanzu sai ka ga mutum yana yi wa iyayensa rowa kawai don Allah ya yi masa arziƙi. Shi bai san arziƙin nan da Allah ya ba shi da shi kansa duk na iyayen sa ne ba. Idan kuma ya ƙi musu abinda suke so a cikin dukiyarsa ba tare da yin almubazarranci ba, toh ya sani yana da laifi mai girma a wurin Allah.

    Waɗanda ba musulmi ba, idan ba su yi wa iyayensu biyayya ba, toh bayan laifin shirka da Allah akwai kuma na ƙin bin umarnin Allah dangane da ƙin yi wa iyayesu biyayya. Shi kuma musulmi da ya saɓa wa iayayyensa, ko da yana da wasu ayukan laheri sai an kama shi da laifin ƙin wa iyayensa biyayya.

    Allah ya hore wa kowane mutum bin iyayensa da kyautata musu, wannan yasa za a ga wanda ba musulmi ba, yana kyautata wa iyayensa, a kuma sami musulmi mai ƙin biyayya ga iyayensa. Babu abinda ya kai wannan takaici. Kamata ya yi a ce wanda ya fi kowa bin umarnin Allah, shi ne wanda ya fi yi wa iyayensa biyayya da kuma kyautata musu.
    Haka kuma, Allah ya tsara idan mutum ya kyautata wa iyayensa, toh shi ma sai ‘ya’yansa su kyauatata masa.

    Rabiu Musa Adam
    Deceember 25th, 2024.

    Danna nan don karanta Ni’imar da Allah Ya Yi Wa Mutane Ba Tare Da Sun Fahimta Ba

    Edita:@rumasau-kallamu

     

  • TARIHIN ZANGA ZANGA A NAJERIYA: MAFITA KO MAHALLAKA

    TARIHIN ZANGA ZANGA A NAJERIYA: MAFITA KO MAHALLAKA

    Tarihi ana rubuta shi ne ba don ka yarda ko kar ka yarda ba, ana rubuta tarihi ne don ka ɗau darasi daga abin da ya faru.

    SHIMFIƊA:

    Kalmar zanga zanga a harshen Hausa tana da ma’anoni da dama a turance, amma kalmomin da suka fi dacewa da ita, ita ce Kalmar “protest” da kuma kalmar “Demonstration”. Kalmar “demonstration” ta fi dacewa da zanga zanga saboda a ma’anar “demonstration” shi ne Jama’a su nuna ra’ayinsu bisa tsari da doka don gwamnati ta canza wani ƙudiri.

    Zai iya zama ta hanyar lumana ko ta hanyar tarzoma da rigima, wanda ya ƙunshi tattaki, tarurruka da sauran hanyoyin nuna wata buƙata ko nuna damuwa”. Kalmar “Protest” ita kuma a dunƙule tana nufin zanga zangar lumana; wato nuna rashin amincewa ko rashin yarda ta hanyar yin tarurruka, tattaki da lacca- lacca, amma cikin lumana wanda ya ƙunshi rike alluna da waƙe-waƙe dan jawo hankalin gwamnati kan wani abu mai mahimmnaci.

    Daga waɗannan ma`anoni guda biyu da suka gabata, za a iya fahimtar kalmar zanga zanga, ta iya zama ta lumana ko akasin haka. Shi yasa duk lokacin da aka ambaci kalmar sai an ɗora ta da wata kalmar don nuna abinda ake nufi ya fito fili.
    Tun ranar 29 ga watan 5 na shekarar 2023 da aka ranstar da shugaban ƙasa Mai girma Ahmed Bola Tinubu ya shelanta cire tallafin mai wanda ya janyo tashin farashin man fetir wanda hakan ya sabbaba tashin sauran kayayyakin masarufi.

    Farashin mai ya ci gaba da hauhawa daga naira 300 zuwa naira 720 (a gidajen ƙananan ‘yan kasuwar mai, a yanzu 820 zuwa 850). Daga nan farashin sauran kayan masarufi suka rinƙa hauhawa da tashin gwaron zabi, sakamakon hakan mutane sun faɗa halin ƙa-ƙa-ni -ka-yi da ƙarin wahalar rayuwa da tsanani na yau da kullum. Wannan halin da ake ciki kullum ƙaruwa yake yi babu alamar sauƙi ko sassauci.

    Rayuwar talaka ta na ƙara shiga tsanani. A hannu guda kuma talakan wannan ƙasa yana ganin yadda shugabanni suke sharholiya da dukiyar ƙasa, da kuma taskance ta ga kansu da iyalansu. Alhali abinda ya kamata shi ne talaka ya sami sauƙin rayuwa saboda irin arziƙin da Allah ya yi wa ƙasarsa.

    Ba shugaba Tinubu ne ya sabbaba wannan halin da ake ciki ba, ɗorawa ya yi daga inda aka tsaya. Tun daga dawowa mulkin dimokraɗiyya ake ƙara farashin man fetur, wanda yana ɗaya daga cikin abinda talakan wannan ƙasa ya dogara da shi dan gudnanar da akasarin rayuwarsa. Janar Abdussalam ya miƙa mulki ga shugaba Obasanjo farashin man fetir yana Naira 20 kacal a shekarar 1999. Amma bayan shekaru 25 yanzu farashin sa ya kai Naira 720 zuwa 800+ (NNPCL N620)

    TARIHIN ZANGA ZANGA

    A tsari irin na dimokraɗiyar ƙasashen yamma da muka ɗauko muka yafa, an amince mutane su nuna fushinsu, ko rashin amincewar su, ko nuna wata buƙata ta su ta hanyar fitowa kan tituna da wuraren tarurrukan jama`a don yin haka. To amma tun da arowa muka yi muka yafa, ba lallai ba ne mutanen mu su yi abinda ya dace ko kuma hukumomin mu su yi abinda ake buƙata. Saboda haka ne zamu duba yadda aka gudanar da wasu zanga zanga a wannnan ƙasar tamu don ganin ina muka dosa game da abinda ya shafi zanga zangar da ake ta kira da a fito.

    ZANGA ZANGAR MATAN ABA 1929

    Wannan shi ne zanga zangar farko a tarihin wannan ƙasar. A ranar 6 ga watan 12 na shekarar 1929, mata sama da dubu goma (10,000) daga ƙabilu shida na kudu maso gabashin wannan ƙasar ne suka fito zanga zanga dan nuna fushinsu game da abubuwa uku.

    Na farko yadda sarakunan da turawa suka naɗa suka taƙaita wa mata a dama da su a gwamnati, wanda a al’adar wannan yanki tun tale-tale mata suna da ta cewa a gudanarwa da alamuran jama`a na yau da kullum. Na biyu ƙin amincewa da ƙarin haraji wanda wani mai riƙon ƙwarya na D.O na lardin Bende, mai suna Mr. Cook ya ɗauko hanyar ƙidaya mata da dabbobi da sake duba yadda ake biyan haraji.

    Sai mata suka zaci ƙara musu haraji za a yi duk da wanda aka ƙara wa mazajensu a shekaran 1928. Sai na uku, yadda farashin kayan gona ya yi warwas saboda babbar masassarar tattalin arziƙi da duniya ta faɗa ciki a wannan lokacin. Waɗannan dalilai ne suka sa mata suka fito don nuna rashin amincewarsu game da waɗannan matakai, wadda ta fara da zanga zangar lumana daga wani gari mai suna Olokoa a garin Bende wadda ta yaɗu zuwa akasarin yankin kudu maso gasbashin wannan ƙasa.

    A ƙarshe, wannan mummunar zanga zangar ta haifar da sace sace, da ƙona kayan gwamnati a wurare kamar Owerri da Kalaba. Mata sama da hamsin da biyar ne suka rasa rayukansu, wasu sama da hamsin suka jikkata. Sannan an sami ‘yar nasara na amince wa mata su shiga a dama da su a gudanar da gwamnati.

    ZANGA ZANGAR MATAN ABEKUTA 1946

    Sakamakon ƙarin haraji da aka ƙaƙabawa wa mata, ƙungiyar mata ta Abekuta (AWU) wanda ƙungiyace ta ma’aikata da `yan kasuwa mata ƙarƙashin jagorancin Funmilayo Ramsone-kuti, a lokacin tana shugaban wata ƙaramar makaranta, da kuma sirikarta Grace Eniola Soyinka. Wannan ƙungiya ta gabatar da ƙorafe-ƙorafenta ga Turawa da kuma Sarkin Abekuta game da nauyin harajin da ka ɗora wa mata da kuma yadda ake gudanar da tsarin shugabanci na Sole Native Authority, duk da korafe korafen, ba abinda ya canza.

    A ranar 5 ga watan Oktoba 1946 mata suka taru a fadar Sarkin Abekuta Ladipo Ademola dan nuna damuwarsu da rashin amincewa da waɗancan matakai. Gwamnati ta mayar da martani mai zafi ta hanyar kame, tare da ɗaukan matan da suka taru har da barkonon tsohuwa.

    An ci gaba da sa-in-sa har zuwa ranar 10 ga watan Sha biyu, in da aka samu matsaya da ‘yar ƙwarya-ƙwaryar nasara, kamar sakin matan da aka kame aka kulle, sannan Sarkin Abekuta ya sauka na ɗan wani lokaci cikin wani yanayi da aka yi na yaudara, saboda turawa suna ƙaunarsa. Sannan aka bai wa mata dama a dama da su a cikin harkar gwamnati. Shima harajin da aka dakatar zuwa wani lokaci aka dawo da shi ta wata hanyar.

    ZANGA-ZANGAR ƊALIBAN JAMI’O’I 1978

    A lokacin mulkin Janar Gawan cikin shekarar 1978 Majalisar ƙoli ta mulkin soji na wannan lokacin ne ta ƙara kudin gurin kwanan dalibai zuwa Naira 90 da kuma kuɗin tikitin cin abinci, aka ƙara kwabo hamsin N50k daga N1.50k zuwa N2.00k. kamar yadda shugaban hukumar kula da Jami`o`i ta ƙasa na lokacin wato Parpesa Jibril Aminu da kuma Ministan Ilimi kanal Ahmadu Ali suka faɗa.

    Wannan ƙarin ya janyo ɗalibai ƙarƙashin ƙungiyarsu ta NUNS a wancan lokacin, wanda Segun Okeowo ya jagoranci zama da sauran ɗalibai a Ilori, Maiduguri da Kalaba. Ƙarshe dai dalibai sun yanke su kaurace wa ɗakunan karatu daga ranar 17 ga watan Afrilu, 1978. Amma da ɗaliban suka fahimci gwamnati ta yi biris da buƙatunsu, sai shugaban ya shelanta da jagorantar zanga zanga a jami`ar Lagas wanda hakan ya janyo kashe ɗalibi ɗaya. A jami`ar Ahmadu Bello da ke Zaria kuwa, ɗalibai takwas ne sojoji suka kashe.

    Bayan sati guda an gudanar da zanga zangar gama gari na ɗalibai wadda aka fi sani da “Ali Must Go” zanga zangar ta janyo ɓarna mai yawa da ta haɗa da sace-sace, lalata kayan gwanmati da sauransu, Gwamnatin tarayya ta ba da umarnin rufe dukkan jami`o`in ƙasar, sannan aka rusa ƙungiyar ɗalibai ta NUNS. Ƙarshe dai gwamnati ba ta janye ƙarin da ta yi ba, sannan an sallami wasu malaman jami`o`i da kuma ɗalibai har da shugaban ƙungiyar ɗaliban Segun Okeowo wanda ɗalibi ne a jami`ar Lagos duk da a ƙarshe ya yi karatunsa a Jami`ar Awolowo. Amma dai babu dai wata ƙwaƙƙwarar nasara da aka cimma a wannan zanga zangar.

    ZANGA ZANGAR RASHIN AMINCEWA DA SHIRIN TSUKE BAKIN ALJIHU 1986

    Ɗaliban Jami`o’i, ma`ikata, da waɗanda ma ba ma`aikata ba har da zauna gari banza ne suka kwarara kan titunan ƙasar nan ranar 24 ga watan biyar na shekarar 1986 bayan da Bankin Duniya mai ba da lamuni ya ƙaƙaba wa Najeriya shirin tsuke bakin aljihu (SAP) wanda ya ƙunshi karya darajar naira, ƙara farashin man fetur, ƙara kudin karatu a jami`o`i. Waɗannan abubuwa sun janyo tsadar kayan masarufi.

    Kafin a fita wannan zanga zangar ƙungiyar ɗaliban ƙasar nan sun yi tarrurruka da miƙa wa gwamnati ƙorafe-ƙorafe guda 10 da suke so gwamnati ta aiwatar da su, a ciki har da soke shirin nan na tsuke bakin aljihun gwamnati, amma gwamnati ta yi kunnen uwar shegu.

    Wannan ya sanya ɗaliban jami’ar Jos da ta Benin suka fita zanga zangar lumana, daga nan zanga zangar ta koma ɓarna, sace-sace da ƙona kadarorin gwamnati. Sakamakon wannan zanga-zangar mutane 2 sun rasa rayukansu a Jami`ar Benin, sannan wasu da yawa sun mutu a manyan birane irin su Lagos. An kame shugaban ƙungiyar ɗaliban jami`o`i Ghani Fawenhimi da shugaban ƙungiyar ɗalibai ta kasa wato Lukman Salihu Mohammed, sannan aka rufe Jami`o`i goma sha uku. Kamar zanga-zangar da ta gabata Gwamnati bata janye wannan shiri na tsuke bakin aljihu ba.

    Shugaban ƙasa na wannan lokacin wato Janar Babangida cewa ya yi babu wani shiri da zai maye gurbinsa. Haka dai aka ƙare ba wani abin a zo a gani bayan zanga zangar.

    ZANGA ZANGAR RASHIN AMINCEWA DA SOKE ZAƁEN 1993

    Musamman a kudu maso yammacin Najeriya an gudanar da mummunar zanga-zanga bayan rushe da soke zaben da aka gudanar a ranar 12 ga watan shida, na shekarar 1993 wanda ya gudana tsakanin Cif Abiola na Jami`iyyar SDP da Alhaji Bashir Tofa na Jam`iyyar NRC. Duk da ba a kai ga sanar da wanda ya lashe zaɓen ba a hukumance, amma dai an tattara ƙuri`un da ya nuna Cif Abiola na jam`iyayr SDP yana kan gaba da ƙuri`u 8,341,309 wato kashi 58.38 a cikin ɗari, abinda ya ba shi damar zarce Bashir Tofa da ya sami ƙuri`a 5, 952,087 wato kaso 41.64 cikin dari.

    Ranar 24 ga watan shida, Shugaban ƙasa na wannan lokacin ya sanar da soke zaɓen gaba daya, wanda hakan ya janyo mummunar zanga zanga da ya janyo mutuwar mutane sama da ɗari. `Yan ƙabilar Ibo da suke Legas sun yi ta gudun hijira dan barin ɓangren yarbawa.

    An rurrufe gidajen jaridu da rediyo, sannan aka kame `yan jaridu. Gwamnati soji ta wannan lokacin ta hana duk wata kotu karɓan karar duk wani abinda ya shafi soke zaɓen. Duk da wannan zanga-zangar da kuma abinda ya faru, ba abinda ya canza. Ƙarshe ma dai aka damƙe Abiola bayan ya ayyana kansa a matsayin shugaban ƙasa, har Allah ya karɓi kayansa.

    ZANGA ZANGAR RASHIN AMINCEWA DA CIRE TALLAFIN MAI 2012 (OCCUPAY NIGERIA)

    A ranar 1 ga watan Janairun shekara 2012 ne shugaban ƙasa na wannan lokacin Jonathan ya shelanta cire tallafin mai da ƙarin farashin da ya kai kashi 120% bisa ɗari akan tsohon farashin na man fetir. Wannan ya janyo ranar 2 ga wannan wata na Janairu aka fito zanga-zanga a biranen Legas, Kano, Abuja, Minna, Gusau da kuma ofishin jakadancin Najeriya da ke birnin Landan, an gudanar da irinta a birnin New York da dai sauran manyan biranen ƙasashen duniya.

    Musamman a garin Minna ta jihar Neja, matasa sun fito tituna suna ƙone-ƙonen kadarorin gwamnati, motocin jama`a har ma kadarorin wasu manyan mutane a jihar. Wannan zanga-zangar kamar sauran na baya an yi ta`adi mai yawa na kayan al`umma, kadarorin gwamnati, an kuma yi hasarar rayuka goma sha shida (16) daga sassa daban-daban na ƙasar nan.

    Ita ma wannan zanga-zangar ba ta haifi wani ɗa mai ido ba, saboda duk buƙatun da aka fito nema ba wanda gwamnati ta aiwatar da shi, ƙarshe dai haka abin ya wuce ba tare da an cimma wani abin a zo a gani ba. Ministan kuɗi na lokacin Mrs. Ngozi Okonjo-Iweala cewa ta yi idan gwamnati ta janye tallafin mai za ta ajiye aiki.

    ZANGA ZANGAR NUNA ƘYAMAR (SARS) ZARATAN (`YANSANDA) NA MUSAMMAN DON DAƘILE FASHI DA MAKAMI DA SAURAN MUGGAN AYYUKAN LAIFI 2021

    Wasu daga cikin jama`a musamman mutanen kudu sun yi ta ƙorafe-ƙorafe kan yadda jami`yan `yansada na musamman wanda aka samar da ita tun shekara 1992 don daƙile fashi da makami da sauran muggan ayyukan `yan ta`adda da masu sace mutane.

    Ana zargin waɗannan zaratan `yansanda da wuce gona da iri da cin zarafin ɗan adam fiye da kima wurin gudanar da ayukansu. Waɗannan zarge-zarge da ƙorafe-ƙorafe sun yi yawa tun daga 2017 har zuwa 2021 musamman ta kafar sadarwa ta tweeter wanda yake ɗauke da alamar #EndSARS.

    Wannan kururuwar ya samu karɓuwar mutane sama da miliyan ashirin da takwas a wannan kafa ta sadarwa. Wanda ya janyo zanga-zangar goyon baya a ƙasashen waje da dama don kawo ƙarshen ayyukan waɗannan `yansanda.

    A cikin watan October, 2021 ne aka gudanar da munanan zanga-zanga a jihohi da dama na kudancin wannan ƙasa dan nuna ƙyamar ayyukan waɗannan zaratan `yansandan na musamman. Wasu daga cikin ire iren zargin da ake yi wa waɗannan jami`ai ya yi ta yawo a kafafen sadarwa kamar wanda aka gano wasu jami`an wannan sashe sun harbe wani matashi har lahira sannan suka yi awon gaba da motarsa ƙirar Lexus SUV.

    A ranar 8 ga watan Goma 2021 zanga-zanga ta ɓarke a sassa daban daban na kudancin wannan ƙasar. ‘Yansanda sun yi ƙoƙarin tarwatsa wannan zanga-zanga amma abin bai yiwu ba. Ranar 20 ga watan Goma an zargi jami`an soji da kisan masu zanga zanga a Lekki na jihar Legas.

    A ranar 11 ga watan 11, 2020 Gwamnati ta sanar da rushe wannan sashe na zaratan jami`an `yansanda. Wannan shi ne babbar nasarar da aka samu biyo bayan wannan zanga-zanga. Amma a gefe guda kuma zanga-zangar da ta janyo hasarar rayuka sama da hamsin (55+) na fararen hula, `Yansanda goma sha daya (11) da kuma jami`an soji bakwai (7).

    RUFEWA

    Idan muka dubi waɗannan jerin zanga-zangar da aka gudanar a wannan ƙasa tun tale-tale da kuma nasarorin da aka samu, za mu iya cewa daga abinda ya wuce na tarihin zanga-zanga, babu wata ƙwaƙƙwarar nasara da zamu iya cewa an samu sai ma dai hasara ta rayuwa da dukiyoyi da zanga zangar ke haifarwa. A taƙaice, kwalliya dai bata biyan kuɗin sabulu.

    Daga abinda ya gabata, wannan zanga-zangar da ake ta kururuwa da kiran mutane su fito, shin tana da wani bambanci da wadda aka yi a baya? Da ga dukkan alamu babu wani bambanci saboda da dalilai masu yawa. Na farko dai shi ne, su waye waɗanda za su shirya wannan zanga-zangar ta yanzu? Misali a baya mun ga ƙungiyar mata da ƙungiyar ɗalibai ne suke kiran zanga-zangar, amma daga ƙarshe sai abin ya fi ƙarfinsu, ɓata-gari suka shiga suka yi aika-aika.

    Toh wannan su waye suka shirya ta, kuma su waye jagororinta? Wannan tambaya ce da duk waɗanda suke kira da a fito zanga-zangar ba takamaimen wanda zai bada amsar ta. Rashin wannnan amsar shi zai nuna inda zanga-zangar ta dosa. Wato kowa sarkin kansa ne a zanga-zangar.

    Abu na biyu, shin akwai tabbbacin ɓata-gari baza su yi amfani da wannan dama ba dan tada hargitsi da tarzoma? Wannan ma abu ne da babu wanda yake da tabbacin rashin faruwar hakan, musamman a irin wannan yanayi da muke ciki na ƙwarya-ƙwaryar tsaro a wannan yanki namu na Arewa da ma kasa baki ɗaya. Saboda haka akwai matsaloli da ba wanda zai iya tantance su kai tsaye, wanda hakan ya ke nuna rashin yinta zai fi yinta alheri.

    A maganar gaskiya, mutanen wannan kasa suna cikin babbar matsala, wahala, takura da matsin rayuwa. Mutane ba sa iya samun abinci, ba sa iya gudanar da rayuwar su kamar yadda ya kamata. Alhali shugabannin siyasa su na cikin daula da walwala, wasu ma har da almubazzaranci. Toh wace hanya za a bi dan nusar da shugabanni halin da talaka ya ke ciki a wannan kasar?

    Dole ne shugabannin addini da na al`umma su riƙe mastayinsu na `yan tsakiya tsakanin Shugannin siyasa da kuma al`umma. Talakawa ba su da damar ganin shugabanni kai tsaye, su faɗa musu halin da suke ciki a sauraresu, amma shugabannin addini da na al`umma musamman sarakuna su ne suke da wata dama ta musamman, ita ce suna da alaƙa da talakawa kai tsaye kuma suna da alaƙa da shugabanni kai tsaye, sun san halin da talakawa suke ciki sannan sun san yadda za su kai kukan talaka a sauresu kuma a ɗau mataki.

    Saboda haka, ya kamata su san wannan sannan kuma su yi abin da ya kamata kafin lokaci ya ƙure musu. Talakwa su zama ba sa ganin girmansu da darajar su, balle su saurari maganarsu.

    Edita:@rumasau-kallamu