Abin Lura Idan ‘Ɗan Ka Ko ‘Yar Ka Sun Kai Shekarun Farko Na Tashen Balaga

0
649

Idan ‘ɗan ka ko ‘yar ka sun kai shekarun farko na tashen balaga, to ka lura da waɗannan:

1. Duk lokacin da yaro ko yarinya suka kai matakin tashen balaga wato “early adolescence”, musamman daga shekara 11, 12 zuwa 13… 18… To wannan shi ne lokaci mafi hatsari ga yara da iyayensu.

2. A lokacin ne yaro yake samun zama na gari ko na banza, me amfanar da al’umma ko me cutar da su.

3. Yaro ya fi tasirantuwa da abokan sa ko kawayen ta fiye da malaman sa ko mahaifan sa.

4. Yaro yana jin shima daidai yake da kowa a duniya, kuma zai iya yin komai kamar yadda kowa yake yi, haka ita ma yarinyar.

5. A lokacin ne yaro yake neman ‘yanci daga ikon mahaifan sa a kan sa. Yana son ɗakin sa daban, wajen kwanciyar sa daban, abinci, kayan sakawa da aski sai wanda ran sa yake so.

6. A lokacin ne yake jin karfin sa ya kawo, kuma zai iya ja da kowa.

7. A lokacin yaro komai yana yin sa ne gaga-gaga, ba kan gado babu nutsuwa, kuma ba wanda ya isa ya hana shi (a tinaninsa), idan kuma iyaye ba su bi hanyar da ta dace ba, to za su sha wahala da shi/ita.

Mafita:

1. Iyaye su ja yaron su a jiki, kuma su yi amfani da hikima wajen yi masa gyara da tarbiyyar sa.

2. Kar su nuna masa ƙarfi ko iko, domin zai iya bauɗare musu, a ƙarshe ya haifar musu da hawan jini.

3. A kula sosai da su waye abokan sa, ko ƙawayen ta. A haɗa shi da na gari, a raba shi da na banza.

4. A samar masa da aikin yi, wajen nuna masa yadda zai dogara da kan sa (koda kuwa dan masu kuɗi ne shi).

5. A tsara masa ayyukan da zai ke yi a kullun tun daga safe zuwa rana, i.e. makaranta, barci, cin abinci, ziyara, hutu, da sauran su.

6. Iyaye su zama abokan ‘yayan su wajen bincikar matsalolin ‘yayan, da magance musu ita.

7. Kada a hana yaro wani abu, face sai an maye masa gurbin sa da wani, idan ba haka ba, to zai yi wanda aka hana shi muni.

8. Kar ayi amfani da karfi, da duka, da tsattsauran hukunci wajen ladabtar da shi; har sai idan abu ya ta’azzara, sai a je da shi guidance and counseling domin neman shawarwari.

9. A rinka tunatar da su ayoyin Alƙur’ani da Hadisan Manzo S.A.W da sukai magana akan biyayyar iyaye.

10. Sannan a rinƙa haɗawa da Addu’ar nema musu shiriya da nagarta a wajen ALLAH (SWT)
Wallaahu A’alam.

ALLAH Ka shiryar da mu da su a kan hanyar Ka Madaidaiciya……

Domin karanta cikakken bayani akan Haƙƙoƙin Ƙananan Yara A Musulunci danna nan.

Domin karanta cikakken bayani akan Yadda Ake Addu’ar Nema Wa Yara Samun Karatu Da Raba Su Da Abokanan Banza danna nan.

labarin da ya wuceMatsayin Koke-koke Da Kururuwa
Labarin na GabaMafifitan Ayyukan Mai Azumi