Axillary yana nufin wani yanki ne a ƙarƙashin hammata wato kusa da nono, kuma akwai manyan jijiyoyin jini a wurin waɗanda suke haɗuwa da tsokokin wurin su zamo kaluluwa (lymph nodes). Ita kuwa kaluluwa wata jaka ce wacce take tattare ƙwayoyin cututtuka idan suka shiga jiki domin ta hana su watsuwa zuwa sauran sassan jikinki. Don haka kaluluwa ba cuta ba ce, tana taimakawa jiki ne wajen rage watsuwar ƙwayoyin cuta a cikinsa.
Don haka duk wacce aka mata awon mammogram scan ya nuna ‘axillary pain” ko “axillary inflammation”, to, yana nufin cewa akwai kumburin kaluluwa ne a wajen hammatarta, Ma’ana, ba yana nufin cewa ana ɗauke da ciwon cancer nono ba ne. Yana nufin cewa garkuwar jiki tana ƙoƙarin yaƙi da ƙwayoyin cututtukan da suka shiga jikinki ne (lymphadenopathy).
Jin ciwo a nono ba tare da kumburi ko zubar ruwan nono ba yana iya zamowa saboda zafin kaluluwar ne yake kai wa zuwa ga nono (referral pain). Za a iya magance kaluluwarki wacce take sanya jiki jin zafin nono da hannu ne ta hanyar yin amfani da magungunan antibiotics ko antiviral ko antifungal idan aka gano ainihin ƙwayoyin cutar da suke haddasa kaluluwar.
Sa’annan za ku iya gasa hammatar da nonuwan da ruwan dumi (warm compress) safe da yamma, ko kuma yin wanka da ruwan dumi. Bayan haka, a riƙa motsa hannuwan, samun isasshen hutu, shan maganin kashe raɗaɗi, tare da yawaita shan ruwa.
Don karanta Zinariyar Awa Ga Jariranmu danna nan
Edita; Rumasa’u M. Kallamu