Wari Ko Hamanin Baki {Mouth Odour}

0
27

Warin baki abu ne me wuyar faɗi ga aboki ko wani da ake jin nauyinsa,toh saide dole akwana atashi mutum zaisan yana dashi,kwai lokutan da dole akan ɗanji baki ya canza wanda canjin ka iya zama normal musamman in ana axumi ko anjima ba’a sa komi a baki ba,

Toh saide in warin ya zamto koda yaushe akai-akai da har yakai yana hana mutum sakewa toh mahimmin abu shine ai kokarin gano abinda ke haddasa hakan tukun amagancesa domin ta haka ne za’a iya raba kai da matsalar.

Wasu lokutan ba rashin brush bane ko rashin tsafta bane kurum kamar yadda mutane kan ɗauka,kwai abubuwa da dama akarkashin hakan wanda suka ƙunshi:

  • Daɗɗiyar cutar ulcer,in mutum ya jima dauke da ulcer batare da maganceta ba, hakan nasa warin baki ko numfashi wanda ke tasowa daga can cikin uwar hanji tunda gyambo ne dama
  • Shyasa akan kirata da gyambon ciki tunda ko gyambon dake waje yakanyi wari ballantana na can cikin ciki da iska bata ratsawa… sakamakon kwayar cutar dake haddasa ulcer ɗin heliko bakta failorus dakesa gyambon ya kume. 
  • Haka nan toshewar kafafofin salivary gland wato bututun sashin dake samar da miyau abaki sakamakon tsakuwa data toshesa ta “salivary stones” hakan yana sa warin baki sosai kuwa
  • Haka ma samuwar tsakuwoyin tonsils wato tonsils stones dake faruwa sanadiyyar abincin dakan makale abaki da hakoran mu bayan gama cin abinci,inda a hankali yakan haɗu da kwayoyin cutar bacteria a bakin ya haddasa wannan tsakuwar dake haddasa warin bakin mara daɗi wanda har numfashi haka za’a ji yana ɗoyi.
  • Haka ma matsalar shigar kwayoyin cuta ramuka ko kogunan ƙashin fuska (sinuses) dake ƙasan hanci su haddasa “sinusitis” wato rauni agun, kaji harta hanci ko tusonon mutum wari yake gami da ciwon kai ko ciwon fuska. 
  • Haka yanayin abincin da mutum ke ci akai akai irinsu albasa ko tafarnuwa batare da tsafyar baki me kyau ba. 
  • Ɗabi’ar shan ababen zaƙi kamar tea empty ko yaushe,chocolates,candy,coke da lemukan gwangwani dana roba,duk in baki ba’a tsaftace sa dakyau tare da amfani da “tongue scrapper” ana karce saman harshen a wankesa bayan anyi brush to ana iya wayar gari da warin baki akwana a tashi. 
  • Ko kuma idan mutum nada kogon haƙori sakamakon abincin dakan shiga ciki ya maƙale nan ma yana iya haddasa warin baki
  • Haka zalika rashin iya wanke baki koda ana yi kullum,shima brush din iyawa ne,don haka in ba a sa kuce ko ina da kyau ana iya wayar gari da matsalar.
  • Haka ma idan mutum na kwanciya bacci batare da wanke baki ba bayan yaci wani abu komi kankantarsa koda kuwa biscuits ne kada araina,wannan bama warin baki ba hatta miyawun bacci na daga abinda ke kawosa wato kwanciya batare da cikakken tsaftar baki ba.
Matakan Ɗauka
  • Idan tsakuwoyin stones ne dole sai an huda an ciresu,saidai wannan aikin likita ne domin ba ganinsu ake ba ido da ido shine yasan mazauninsu a bakin,warin bakinsu yafi hamami in sune kamar an bude irin tukunyar gas dinnan haka zakaji bakin mutum yayi
  • Idan rashin yin brush da kyau ne toh ya dace agyara a kuma ke samun abu ana sakace tsakanin hakora.
  • Idan hakori me kogo mutum garesa yaje a wanke acike kogon ko a cire hakorin in bazai ciku ba,shikenan an rabu
  • Haka zalika in wani abu mutum yake ci toh sai ya kaurace masa musamman lokacin  kwanciya bacci,karka ci komi awa 2 kafin yin bacci inba ruwa ba.
  • Wanke baki da ruwan sinadarin hydrogen peroxide irin wanda ake siyarwa don wankin ciwo,bayan an  tsiyaya an ɗan ƙara masa ruwa kaɗan an kashe zafinsa sai ai amfani dashi ya zamto ana kurkure baki dashi sau 2 ko 3 ayini,yakan taimaka wajen rage matsalar idan har dalilin kwayoyin cuta ne
  • Tauna kanumfari kamar ƙwaya 3 yana sa aji saukin abin musamman wanda hakan ke hanasu more jima’i,in wajen jima’i ne kuma ana son kiss da sauransu toh ai amfani da kanumfarin a tauna kafin afara artabun yana dauke warin baki nan take har kuyi artabun ku ku gama 
  • Ko kuma tafasa kanumfarin kwaya 7 ko sama haka da a wadace da ruwa daidai misali arika kurkure baki da ruwan ana zubarwa a hankali,ake yi safe da yamma zuwa wani dan lokaci,musamman ace ana ƙarawa da gishiri acikin ruwan kanumfarin zaifi aiki, ana iya ake kurkurawa sau uku ayini basai iya sau biyu ba,ya danganta da tsananin warin da ake ji. 
  • In ulcer ce ai maganinta itama,sannan ake brush kullum kafin a kwanta.
  • Haka in “sinusitis” ne da hatta mutum shi kansa yana jin inya buso iskar hancinsa ya shaka tana warin ga ciwon kai toh shima yaje ga likita abashi magani a asibiti a warkar da abin.
  • Ko amfani da apple cider vinegar wajen kurkure baki safe da yamma inba kanumfari duk yakan taimaka.
  • Hakama amfani man olive azuba arika kurkurawa tsawon minti 20 a baki kafin a zubar,hakan ajere akai-akai zai tallafa
  • Hakama amfani da baking soda wajen wanke baki safe da yamma ko duk bayan sanda aka gama cin abinci a madadin amfani da makilin
  • Sai canza brush akai akai kada yake wuce wata 3 ana amfani da brush guda.
  • Koyon halayyar zuwa arika wankin hakora a clinics na dentist duk bayan wata 6 kimanin sau 2 a shekara zai taimaka,har lafiyar idanu da kunne saita ƙaru,basai me ciwon hakori ba wannan,zuwa flossing abu ne da akeso ga kowa. 

Domin karanta Contraceptive Implants: Ana Kiranta Ashanar Fata Da Hausa Wannan Wata Hanya Ce Da Ake Dasa Wani Roba Ƙarami A Hanun Mace Danna nan 

labarin da ya wuceContraceptive Implants : Ana Kiranta Ashanar Fata Da Hausa Wannan Wata Hanya Ce Da Ake Dasa Wani Roba Ƙarami A Hanun Mace
Labarin na GabaAmfanin Shan Ruwa Da Safiya Kafin Aci Komai