Hatsarin Amfani Da Mayukan Hasken Fata

0
50

Yin amfani da funbact A da wasu mutane keyi, musamman mata domin mayar da fatar jikinsu ta yi haske, abu ne mai matuƙar hatsari ga lafiyar fata da jikin mutum gaba-ɗaya. Ya kamata mu fahimci cewa Allah SWT ya tsara halittar fatar mutum ne daidai da yadda ta dace da shi, ta fuskar launinta, laushinta, ko kaushinta.

Hakan yana nufin matuƙar launi ko laushi ko kaushin fata bai haifarwa mutum alamun rashin lafiya ba, to, ya haƙura da ita a haka nan kada ya yi ƙoƙarin yin amfani da sabulai, ko mayuka, ko ƙwayoyin magani, ko allurarai domin canza su.

Kaɗan daga cikin hatsarin da mutum zai iya fuskanta idan ya ɗauki matakin yin amfani da funbact A ko kuma duk wani maganin haskaka fata su ne:

1. Lalacewar fata (skin damage): magungunan haskaka fata suna ƙunshe ne da sinadarai (chemicals) masu ƙarfin gaske, kamar hydroquinone, steroids, da mercury. Daɗewa ana yin amfani da magunguna masu ɗauke da waɗannan sinadaran zai iya lalata ƙarfin fata (skin’s structure) ta zamo siririya maras ƙarfi, ta yadda za ta riƙa saurin yagewa da zarar wani abu ya yakushe ta, komai ƙanƙantarsa. Irinsa ne idan dalili ya taso wanda za a yi wa mutum ɗinki a fatarsa, to, ɗinkin ba zai yiwu ba saboda gautsin fatar.

2. Dabbare-dabbaren launin fata (skin discoloration): daɗewa ana yin amfani da magungunan ƙara hasken fata yana sanya fatar ta yi dabbare-dabbare kamar jikin kura. Mutum ya zamo kamar mujiya, ba ya son shiga cikin jama’a domin jikinsa baya da kyawun gani.

3. Bijirewar fata ga abubuwa masu yawa waɗanda mutum yake mu’amala da su (allergic reactions): wannan ya ƙunshi canzawar launin fata ta yi ja-zur, ko ƙaiƙayi, ko kumburi, ko zafi, ko ƙuraje, ko samiha. Ka ga mutum ya koma safa-da-marwa a asibiti wajen neman magani. Sa’annan duk ya karar da ‘yan kwabbansa da ya kamata ya riƙa cin naman kaji da su wajen sayen magani.

4. Ƙaruwar tasirantuwa da zafin rana (increased sun sensitivity): duk fatar da ake yi mata amfani da magungunan ƙarin haske, to, tabbas za ta rasa juriyar shiga cikin zafin rana. Idan kuwa mutum ya zauna a cikin rana, zai ji kamar ana soya shi a cikin tafasasshen mai. Sa’annan hakan zai jefa shi cikin hatsarin kamuwa da cancer ta fata.

5. Kamuwa da gubar mercury (mercury poisoning contraction): kamar yadda na faɗa a sama, magungunan haskaka fata suna ƙunshe da sinadarin mercury, wanda shi kuwa garin ƙarfe ne mai hatsari. Don haka, daɗewa ana yin amfani da shi zai iya sanya kamuwa da gubar mercury. Ita kuwa gubar mercury tana haddasa cututtukan laka (neurological disorders) da ciwon ƙoda (kidney disease).

6. Rashin karfin gwuiwar mu’amala da mutane (low self esteem): duk mutumin da ya ɗauki kansa a matsayin mummuna saboda kawai yana da duhun launin fata, to, kullum zai riƙa raina kansa, ta hanyar jin cewa shi ba cikakken mutum ba ne. Idan namiji ne, sai ya kasa tunkarar ‘yan-mata da maganar aure. Idan mace ce, ta yi ta gudun samari ko manema aurenta.

7. Rashin daidaiton zubar ruwan sinadarai (hormonal imbalance): wasu daga cikin magungunan haskaka fata suna ƙunshe da sinadarai masu jirkita daidaiton sinadaran jiki, daga nan su haifar da rikicewar al’ada da sauran matsalolin lafiya.

Bisa la’akari da waɗannan abubuwan da na lissafa, ya kamata mu guji yin mu’amala da magungunan haskaka fata gaba-ɗaya.

Shi funbact A an yi shi ne domin magance cututtukan fata idan sun auku. Saboda haka bai dace a yi amfani da shi ba sai da umurnin likita. Muhimman sinadaran da suke cikinsa su ne:

a. Betamethasone wanda rukunin magungunan hana kumburi da ƙaiƙayi ne na corticosteroids. Akan yi amfani da shi wajen magance eczema, psoriasis, da sauransu.

b. Neomycin wanda rukunin magungunan antibiotics ne wanda ake amfani da su domin magance cututtukan bacteria.

Don karanta Allurar Da Ake Yi A Jijiya Da Allurar Da Ake Yi A Tsoka danna nan
Edita@rumasau-kallamu

labarin da ya wuceJin Harsuna Biyu Ko Fiye Da Biyu (BILINGUALISM AND MULTILINGUALISM)
Labarin na GabaHaɗuwar Harshe (LANGUAGE CONTACT)