Hukunce-Hukuncen Jinin Cuta

0
475

Shin ko kun san mene ne hukuncin jinin cuta?

Jinin cuta ba ya hana wani abu daga abubuwan da jinin haila da na biƙi suke hanawa; kuma haƙiƙa mai jinin cutar hukuncin ta ɗaya da mace mai tsarki, tana salla, kuma tana azumi; kuma tana ittikafi a cikin masallaci, kuma ana iya saduwa da ita.

Fadima ‘yar Abi Hubaish, Allah ya yarda da ita ta ce:

“Ya Manzon Allah, ni ina jini ba na tsarkaka, shin zan bar salla ne?

Sai Manzon Allah ya ce: “A’a, … idan hailar ta zo, to ki bar salla, idan kuma ta kau, to ki wanke jinin ki yi salla”.

Sai dai mai jinin cuta tana yin alwala lokacin shigar kowace sallah.

Wannan bayanin an ciro shi ne daga Littafin Fassarar Littafin Fikhul Muyassar Na Biyu wanda Rukayya Dalha ta wallafa shi; Domin karanta cikakken littaffin danna nan.

Domin karanta cikakken bayani a kan Abubuwan Da Suke Hana Mace Bin Miji danna nan.

labarin da ya wuceAbin da ya Halatta Game da Mai Jinin Haila da na Biƙi Tare da Mazajensu
Labarin na GabaYadda Ake Amfani Da Status Saver Na Whatsapp