Abubuwan Da Suke Hana Mace Bin Miji

0
534

A Musulunce, akwai abubuwan da suke hana aiwatar da umarnin miji a duk lokacin da umarninsa ya ci karo dasu. Ga bayanin abubuwan kamar haka:

1. Umarni da saɓon Allah: Haramun ne mace tayi wa mijinta biyayya a duk lokacin da ya umarce ta da aikin saɓo, saboda hadisin da aka karɓo daga sahabin Annabi, Aliyu (R.A) yace, Manzon Allah (tsira da amincin Allah su tabbata agare shi) yace: “Babu biyayya ga wani mutum a cikin aikin saɓo. Haƙiƙa kaɗai ana yin biyayya ne a cikin abin da yake sananne a shari’a “.
Bukhari, Muslim da Abu Dawud da wasun su ne suka rawaito shi.

2. Umarni da abin da yafi ƙarfin ikon wanda aka umarta. Musulunci bai yarda mace ta aiwatar abin da mijinta yasa ta matuƙar dai abin da yasa ta yin yafi ƙarfin ikonta. Dalili kuwa hadisin da aka karɓo daga Umar ɗan Khaddab (R.A) cewa: ” (mu musulmai an hana mu ɗorawa kanmu abinda bazamu iya ba”. Bukhari ne ya rawaito shi.

3. Afkuwar ƙaƙƙarfan uzuri: kamar mantuwa ko rashin lafiya. A musuluce, mantuwa da rashin lafiya ƙaƙƙarfan uzuri ne daka iya hana mace aiwatar da umarnin mijinta, kuma ya zama batayi laifi ba, amma fa duk lokacin da mace taƙi bin umarnin mijinta, alhali umarnin nasa bai ci karo da ɗaya daga cikin waɗannan abubuwa ba, to babu ko shakka ta tabbata mai saɓo kuma ta cuci kanta .

Domin sanin cikakken bayani akan Haƙƙoƙin Miji Na Dole Akan Matarsa danna nan.

Wannan Bayani An ciro shi ne daga littafin Nagartacciyar Rayuwar Aure wanda Abubakar Abbas ya wallafa shi domin karanta cikakken littafin danna nan.

labarin da ya wuceKyautata Tarbiyyar ‘Ya’ya
Labarin na GabaDokokin Suturar Musulma