Kyautata Tarbiyyar ‘Ya’ya

0
521

‘Ya’ya wata babbar ni’ima ce da baiwa da Allah yake yin ta ga wanda yaso cikin bayinsa.
Yaba wa Allah da gode masa game da wannan ni’ima shi ne: uwa da uba; miji da mata, su tsayu a kan tarbiyantar da ‘ya’ yansu da ilmantar da su hakkokin Allah da na bayinsa don su iya isarwa da kowane mai hakki hakkinsa.

Allah (S.W.T) ya labarta mana yadda Annabi Ibrahim da Annabi Ya’akub (A.S) suka yi kokarin sauke wannan nauyi da ya rataya a wuyansu inda ya ce:
Ma’ana:“kuma ba wanda zai ƙi addinin Annabi Ibrahim sai wanda bai san ciwon kansa ba. Hakika mun zaɓe shi a duniya kuma shi a lahira yana cikin salihai (130). (ku tuna) lokacin da Ubangijinsa yace da shi ka mika wuya (ka musulunta) ya ce “na mika wuya ga Ubangijin talikai (131). Sai kuma (Annabi) Ibrahim ya yi wa ‘ya’yansa wasiyya da ita (wannan hanyar), kuma Ya’akub ma (ya yi wasiyya), ya ce: “ku ‘ya’yana! Hakika Ubangiji ya zaɓa muku addini, saboda haka kada ku kuskura ku mutu sai kuna musulmai (132)”.
Ita ma kakar Annabi Isa (A.S) matar Imran ta tsayu da yi wa ‘yarta Maryam addu’ar Allah ya tsare ta kuma ya tsare zuriyarta daga sharrin shaidan. Allah Madaukaki ya ce:
Ma’ana: “…haƙiƙa na raɗa mata suna Maryam, kuma (ya Ubangijina) ina rokonka ka tsare ta da zuriyarta daga shaidan jefaffe (36). Sai Ubangiji ya karbe ta kyakkyawar karba, kuma ya haɓaka, kuma ya sanya rainonta ga Zakariyya…”.
Don haka, rainon ‘ya’ya a kan tarbiyyar ƙwarai da ta ƙunshi dukkan wani abu kyakkyawa a musulunce, tare da nesanta su daga dukkan wani mummunan abu a musulunce; haƙƙi ne ya rataya a kan miji da mata, uwa da uba gaba ɗayansu, lallai ne su yi da jikinsu, da maganarsu, da kuma dukiyarsu har a kai ga cim ma biyan buƙata.
An karɓo daga Abdullahi ɗan Umar Allah ya yarda da su, daga Annabi (tsira da amincin Allah su tabba agare shi) ya ce: “Dukkanku makiyaya ne kuma kowannenku abin tambaya ne a kan abin da aka ba shi kiwo… mai gida makiyayi ne a kan mutanen gidansa, mace ma makiyayiya ce akan gidan mijinta da ‘ya’yansa, dukkanku makiyaya ne kuma dukkanku ababan tambaya ne a kan abin da aka ba ku kiwo”. Bukhari da muslim ne suke rawaito shi.

Domin karanta cikakken bayani akan Haƙƙin Wanda Mutuwa Ta Raba Shi Da Abokin Zamansa Daga Cikin Ma’aurata danna nan.

Wannan bayani an ciro shi ne daga cikin littafin Nagartacciyar Rayuwar Aure wanda Abubakar Abbas ya wallafa shi domin karanta cikakken littafin danna nan.

labarin da ya wuceRaya Daren Lailatul Ƙadari
Labarin na GabaAbubuwan Da Suke Hana Mace Bin Miji