Cin Mutuncin Mutane Da Sunan Hamayyar Siyasa.

0
435

Ga  duk mai sauraro kafafen yaɗa labarai, ko wanda wajen zama ke haɗa shi da ‘yan siyasa daga lokaci zuwa lokaci, zai ji suna faɗar wasu maganganu na cin mutunci ga duk wanda yake hamayya da abin da suke so, ko suke kai, kuma a duk lokacin da wani ya yi ƙoƙarin dakatar da su ko hana su, sai ka ji sun ce, “Ai hamayyar siyasa ce”. Wato kai ka yi zaton faɗar hakan wata aya suka jawo dake halatta musu yin hakan.

Alhali kuwa an karɓo hadisi daga abu Huraira, Allah ya yarda da shi ya ce: Manzon Allah (Sallallahu Alaihi Wasallam) ya ce: ” …. Duk musulmi game da ɗan’uwansa musulmi haramun ne cin mutuncinsa da cin dukiyarsa da kuma zubar da jininsa, kuma ya isa mutum sharri ya rinƙa wulaƙanta ɗan’uwansa musulmi.”
Muslim da Tirmizi ne suka rawaito shi.
Kuma an karɓo daga Abdullahi ɗan Amr ɗan Aas Allah ya yarda da su daga Annabi (Sallallahu Alaihi Wasallam) ya ce: “Musulmin ƙwarai shi ne wanda musulmai suka kuɓuta daga cutar harshensa da ta hannunsa. …”
Bukhari da Muslim ne suka rawaito shi.

Domin karanta cikakken bayani a kan Gulma (Tsegumi) Don Gurɓata Tsakanin Jama’a danna nan.

Wannan bayani an ciro shi ne daga littafin Hattara Dai ‘Yan Siyasar Musulmai wanda Abubakar Abbas ya wallafa shi domin karanta cikakken littafin Danna nan.

labarin da ya wuceYin Ƙarya Da Sunan Yarfen Siyasa.
Labarin na GabaGulma (Tsegumi) Don Gurɓata Tsakanin Jama’a