Kishi Iri Nawa ne

0
615

Kishi Iri biyu ne:

1. Kishin Allah ga bayinsa.
2. Kishin bayi a tsakaninsu.

Yaya Kishin Allah Yake?

Kishin Allah shi ne, fushin da Allah yake yi da muminin bawan da ya saɓa masa, da kuma ƙyamar da yake yi wa mummunan aikin bawa ya aikata.

Mene ne Bambanci Tsakanin Kishin Allah da na Bayinsa?

Kishin Allah ya bambanta da kishin bayinsa da abubuwa masu zuwa kamar haka:
1. Kishin Allah ya fifici na bayi.
2. Kaɗai Allah yana yin kishinsa ne idan aka yi abin da ya haramta.
An karɓo daga Abdulahi ɗan Mas’ud (Radiyallahu Anhu) daga Annabi tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi ya ce: “Babu wanda ya fi Allah kishi” . Bukhari ne ya rawito shi.
Kuma an karɓo daga Abu Huraira (Radiyallahu Anhu) daga Annabi tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi ya ce.” Allah yana kishi, kuma yana yin sa ne idan mumini ya aikata abin da ya haramta”. Bukhari ne ya rawito shi.

Domin karanta cikakken bayani a kan Mene ne Kishi danna nan.

Wannan bayani an ciro shi ne daga littafin Duhun Kai Gaba Da Kishiya wanda Abubakar Abbas ya wallafa shi domin karanta cikakken littafi danna nan.

labarin da ya wuceHaƙƙin Zaman Gidan Miji
Labarin na GabaKashi Nawa Kishin Bayi ya Kasu?