Kashi Nawa Kishin Bayi ya Kasu?

0
525

Kishin bayi ya kasu kasha biyu:

1. Halattaccen Kishi.
2. Haramtaccen Kishi.

Mene Ne  Halattaccen Kishi?

Halattaccen kishi shi ne, matsakaicin kishi wanda Allah yake so, kuma wanda yake afkuwa saboda faruwar wani abin zargi ko tuhuma ko kuma bayyanar zalunci a fili ƙarara. An karɓo daga Jabir ɗan Atik (Radiyallahu Anhu) ya ce, Annabi tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi ya ce: “… kishin da Allah yake so shi ne kishi kan wani abin Zargi” Abu Dawud ne ya rawaito shi.

Misalin Halattaccen kishi:

A lokacin Manzon Allah tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi, wani sahabinsa sabon aure ya nemi izininsa don zuwa gida wajen iyalinsa, sai Manzon Allah tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi ya ce da shi: “Ɗauki makaminka ka tafi da shi, don ina jiye maka tsoron cin karo da Yahudawa bani Ƙuraiza”. Sai wannan sahabi ya ɗauki makaminsa ya tafi da shi, ko da ya isa ƙofar gidansa, sai ya tarar da matarsa tsaye a ƙofar gida, nan take sai kishi ya kama shi, inda ya nufi matarsa da mashinsa zai caka mata. Sai ta ce masa kar ka jefe ni da mashi, shiga gidan ka ga abin da ya fito da ni. Sai ya shiga, da shigarsa sai ya ga wani shirgegen maciji nannade a kan shimfiɗa. sai ya yi kan macijin ya jefe shi da mashin, sannan ya kafe mashin a tsakar gidan ya fito. Can sai macijin ya motsa ya yiwo kansa, inda a sakamakon hakan ba a san wanda ya riga mutuwa ba a tsakaninsu”. Muslim ne ya rawaito shi. Hadisi Mai lamba (2236).

Wane Amfani Halattaccen Kishi Yake da Shi?

Halattaccen kishi yana da amfani kamar haka:
1. Sa mai yin sa samu ƙaunar Allah.
2. Sakawa a ga kwarjinin wanda yake yin sa.
3. Sawa a cimma tsawaituwar wanda aka yi shi domin sa.
4. Tsamo wanda aka yi kishin domin sa daga halaka.
5. Sanin masoyinka.

Wane Kishi ne Haramtacce?

Haramtaccen kishi shi ne wanda Allah baya son sa, wanda yake afkuwa ba tare da faruwar wani abin zargi ba, ko kuma wanda aka wuce iyaka wajen yin sa, ko da kuwa ya faru ne a ta dalilin wani abin zargi.

Misalin Haramtaccen Kishi:

An karɓo daga Abdullahi ɗan Abbas (Radiyallahu Anhu) cewa, wani mutum ya zo wajensa, sai ya ce da shi. “Na nemi auren ta, sai ta so shi, sai kishin son ta ya motsa mini, sai na kashe ta, shin ko zai yiwu a karɓi tubana?” Sai Abdulalhi ɗan Abbas ya ce da shi, “Ko mahaifiyarka na da rai?” Sai ya ce, “A’a”. sai ya ce masa, “To ka tuba ga Allah mai gima da buwaya, kuma ka ci gaba da kusantar sa gwargwadon iko”. Aɗa’u ɗan Yasar ya ce :” Sai ya ce “Ni ban san wani aiki da ya fi kusantarwa zuwa ga Allah mai girma ba Buwaya ba irin bin mahaifiya”. Bukhari ne ya rawaito shi a cikin littafinsa Al’adabul Mufrad.

Domin karanta cikakken bayani akan Mene Ne Maganin Ƙazamin Kishi (Haramtacce) danna nan.

Wannan bayani anciro shine daga littafin Duhun Kai Gaba Da Kishiya wanda Abubakar Abbas Ya wallafa shi domin karanta cikakken littafi danna nan.

labarin da ya wuceKishi Iri Nawa ne
Labarin na GabaMene ne Maganin Ƙazamin Kishi ( Haramtacce)