Raka’a Biyu Kafin Magariba

0
676

Ana so ga wanda ya ga dama ya sallaci raka’a biyu kafin sallar Magariba saboda Hadisin Abdullah Ibn Mugaffal (R.A) haƙika Manzon Allah (Sallallahu alaihi wasallam) Ya ce: ku yi salla kafin magriba ku yi sallah kafin magariba, a na uku sai ya ce in kun ga dama, domin kada a ɗauke ta sunnan ratiba”. (Bukhari 1129, Abu Dawud 1281).
Kuma Anas Ibn Malik (R.A) Ya ce: “Idan mai kiran Sallah ya yi kira sai shabbai su yi ta gaggawar yin satara da dirkokin masallaci, suna sallatar raka’a biyu kafin sallar magariba” (Mulim 625, Muslim 838).

Domin karanta cikakken bayani akan Nafiloli Waɗanda Ba Ratibai Ba danna nan.

Wannan bayani anciro shine daga littafin Ingantattun Nafiloli Da Falalarsu wanda Usman Abubakar Muhammad (Shehu Mansur Dala) ya wallafa shi domin karanta cikakken littafin danna nan.

labarin da ya wuceFalalar Raka’ Atil Fajr.
Labarin na GabaNafiloli Waɗanda Ba Ratibai Ba.