Matsayin Azumin Ashura A Wurin Ahlul Baiti (Radiyallahu Anhuma)

0
44

Daga hadisan da suka gabata, za mu fahimci cewa ranar Ashura sananniya ce tun kafin bayyanar Manzon Allah (Sallallahu Alaihi Wa Sallam) kuma azumin ranar shi ma an daɗe ana yin sa tun zamanin yahudu da nasara har zuwa lokacin larabawan jahiliyya.

To amma akwai waɗansu masu da’awar Son Ahlul Bait (Radiyallahu Anhuma), da bin tafarkinsu su ba sa yin wannan azumin; suna ko ganin ƙirƙirarsa aka yi kawai wai don nuna farin ciki da goyon baya; kan kashe Sayyidina Husaini (Radiyallahu Anhu) da aka yi a ranar ashura shekara ta 61 hijiriyya.

Wannan yana nufin tun ɗaruruwan shekaru kafin a haifi Husainin aka fara murnar za a kashe shi; ɗan uwa ka yi tunani, a hankalce haka za ta yiwu?

To amma mu duba mu gani shin su Ahlul baiti (Radiyallahu Anhuma); ya ya suka ɗauki ranar ashura da kuma azumin ranar? Ga amsa daga bakinsu:

Sayyidina Ali (Radiyallahu Anhu): An karɓo daga Al-As-wad IbnYazid ya ce; “Ban ganin wanda ya fi Sayyidina da Ali da Abu Musa yawan umartar mutane da yin azumin ashura ba.

An karɓo daga Abu Abdullahi daga babansa (Alaihis Salam) ya ce haƙiƙa Ali (Alaihis Salam) ya ce; “Ku yi azumin ashura da tasu’a saboda yana kankare zunubin shekara guda 2.

Daga Abul Hasan (Alaihis Salam) ya ce: “Manzon Allah (Sallallahu Alaihi Wa Sallam) ya yi azumi ranar Ashura”3)
JA’AFARU SADIK (Radiyallahu Anhu)

An karɓo daga Assadik (Radiyallahu Anhu) ya ce wanda zai iya azumtar watan Muharram gaba ɗayansa ya yi; zai tsare mai yin sa daga dukkan saɓo”.

Daga Abu Ja’afar (Alaihis Salam) ya ce: “Jirgin ruwan Annabi Nuhu (Alaihis Salam) ya tsaya a jikin dutsen jude ranar Ashura, sai ya umarci gaba ɗayan mutane da aljanu da suke taře da shi da su yi azumi a ranar.

Wannan kaɗan ne daga maganganun Ahlul Baiti (Radiyallahu Anhuma) kan falalar azumin ashura, saboda wani babban malamin shi’a mai suna Radiyuddin Abul Ƙasim Aliyu bin Musa Ibn Ja’afar Ibn Tawus ya ce: Hadisai da yawa sun zo kan bayanin zaburarwar kan azumin ranar Ashura”.

Mai karatu ka ga yadda maganganun Ahlul Baiti (Alaihis Salam) suka dace da maganganun kakansu (Sallallahu Alaihi Wasallam) da na sauran musulmi kan azumin Ashura da falalarsa da tarihinsa tun zamanin Annabi Nuhu (Alaihis Salam).

Sai dai kuma su Kulaini da Ɗusi da ire-irensu sun yi fatali da waɗannan maganganu na gaskiya da hadisai ta yadda suka Rago waɗansu maganganun suka jingina su ga Ahlul Baiti saɓanin waɗanda suka gabata.

A irin waɗanan maganganu sai suka ce wai Abu Ja’afar da Abu Abdullahi sun hana yin azumin ashura; kuma yin sa bidi’a ne, kuma wai iyalan Ziyadu ne da banu Umayya suka ƙirƙiro domin murnar kashe Husaini; kuma duk wanda ya yi to zunubinsu ɗaya da waɗanda suka kashe Husaini, da sauran maganganu.

To abin tambaya a nan shi ne, shin su ma Imaman da ma Annabi Nuhu da Ahlul Kitabi har ma da shugaban halitta (Sallallahu Alaihi Wa Sallam) banu Umayya ne? Kuma wannan wacce irin tufka ce da warwara daga Imamai? Anya suna baki biyu? Ko kuwa dai akwai wata a ƙasa?

Kuma su Ɗusi da Sadik da Hurrul Amili, da Nuri Attabrasj da Ibn Tawus da suka rawaito falalar azumin; suna yaɗa sunnar banu Umayya ke nan? Ɗan uwa ka yi tunani.

Daga ƙarshe ya kamata a sani cewa ruwayoyin da suke tabbatar da falalar ranar ashura da yin azumi a ranar ingantattu ne a wurin malaman Shi’a; amma waɗanda suke hani da sukar azumin raunana ne! Kamar yadda shaihunsu Alhaj Assayyid Muhammad Rida Alhusaini Alha’iri ya faɗa a littafinsa mai suna; “Najatul Umma fi lkamatil aza’i ala! Husaini wal a’ imma shafuka na 145, da 147, bugun binin Ƙum na Iran shekara 1413.

Gaskiyar Magana

Daga abubuwan da suka gabata za mu fahimci cewa gaskiyar magana game da ranar ashura da azuminta ita ce; Ranar Ashura rana ce mai daraja da ake yin azumi a cikinta tun kafin bayyanar Manzon Allah (Sallallahu Alaihi Wa Sallam).

Dukkanin musulmai tun daga annabawa har Ahlul Baiti sun yarda da haka. Duk abinda ya saɓawa abin da ya gabata ƙarya ne.

Ya Allah ka ganar da mu gaskiya ka ba mu ikon bin ta.

Domin karanta cikakken bayani a kan Abubuwan Da Ba Su Inganta Ba Game Da Ashura danna nan.

Wannan bayanin an ciro shi ne daga Littafin Gaskiyar Magana A Kan Ashura wanda Shehu Mansur Dala ya wallafa shi; domin karanta cikakken Littafin danna nan.

Edita@rumasau-kallamu

labarin da ya wuceMalaman Mabera A Sakkwato
Labarin na GabaLalurar Rashin Jin Ƙamshi, Ko Wari (LOSS OF SMELL)