Karatun Manzon Allah (Sallallahu alaihi wassallam).

0
420

Allah Maɗaukaki ya ce da Manzonsa (Sallallahualaihi wassallam): “Ƙa kyautata karatun Alkur’ani matukar kyautatawa”.

Suratul Muzammil, aya ta 4.

Sai Manzon Allah tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi ya kasance yana yayyanka karatunsa, aya-aya, yana cewa: (Alhamdulillahi rabbil alamin)
Sannan ya tsaya, sannan yace: (Arrahamanurrahim)
Sannan ya tsaya, kuma yana jan muryarsa da karatu ja sosai. Sannan kuma karatunsa, tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi, karatu ne da za a iya fassara shi harafi bayan harafi

Suratul Fatiha, aya ta (1-2).

Domin karanta cikakken bayani a kan Kukan Manzon Allah (sallallahu alaihi wassallam) danna nan.

Wannan bayani an ciro shi ne daga littafin Manzon Allah Annabi Muhammad (Sallallahu alaihi wassallam) Kamar Ga Ka Ga Shi wanda Abubakar Abbas ya wallafa shi domin karanta cikakken littafin danna nan.

labarin da ya wuceZancen Manzo (Sallahu Alaihi Wasallam).
Labarin na GabaDariyar Manzon Allah (Sallallahu alaihi wassallam).