Kaffarar Azumin Ramadan

0
395

Game da kaffara kuwa; ya gabata cikin hadisin Abu Hurairah (Radiyallahu Anhu); inda wani mutum ya sadu da iyalinsa da tsakar rana a watan azumin Ramadan; kuma aka ce akwai ramuwar kaffara a kan sa, wato ‘yanta wuyaye, idan bai samu dama ba; to azumin watanni biyu a jere; idan kuma ba zai iya ba; to ya ciyar da miskinai sittin.

An ce, kaffarar jima’i a kan zaɓi ake yi ba a tartibi (jere) ba; sai dai waɗanda suka rawaito tartibin sun fi yawa. Saboda haka ruwayarsu ta fi rinjaye saboda sun fi yawa, kuma suna da ƙarin masaniya (ilimi) sama da ragowar; inda suka yi ittifaƙi kan cewa azumin wanda ya yi jima’i ya warware; wanda hakan ba ta samu ba cikin ragowar ruwayar, kuma wanda ya sani hujja ne a kan wanda bai sani ba; kuma daga cikin abin da ke rinjayar da tartwikiibin cewa ya fi taka tsantsan kuma riƙo da shi ya isar; idan mun ce zaɓi ne ko ba zaƙi ba, saɓanin idan muka riƙi ragowar hadisan.

Haka kuma wanda kaffara ta hau kansa, kuma ya kasa ‘yanta wuyaye ko yin azumi ko ciyarwa; to za ta sauƙa daga kansa, saboda ba a kallafa abu sai har idan za a iya. Allah Maɗaukakin Sarki ya ce:

“Allah ba ya kallafawa rai abu face wanda za ta iya”. (Baqara: 286).

Kuma ga dalilin aikin Ma’aiki (Sallallahu Alaihi Wasalam); wato inda Ya ɗauke kaffara kan mutumin nan yayin da ya gaya masa wahalar da yake ciki, har ma ya ba shi dabino akan ya je ya ciyar da iyalansa.

Sannan kaffara ba ta hawa kan macen da mijinta ya neme ta; saboda Manzon Allah (Sallallahu Alaihi Wasalam) an ba shi labarin abin da ya faru tsakanin wannan mutumi da matarsa, amma bai wajabta mata kaffara ba, sai guda ɗaya (wato ramuwar azumin). Allahu a’alam.

Domin karanta cikakken bayani akan Ramuwar Azumin Ramadan danna nan.

Domin karanta cikakken bayani akan Raya Daren Lailatul ƙadari danna nan.

Wannan bayanin anciro shine daga Littafin Guziri Ga Mai Azumin Ramadana (Bisa Koyarwar Alƙur’ani Da Sunnah); wanda Ibrahim Baba (Ibrahim Garba Nayaya (Baban Fauzan) ya wallafa shi; Don karanta cikakken Littafin danna nan.

labarin da ya wuceYadda Al’ada (Jinin Haila) Yake
Labarin na GabaFalalar Yin Umara A Watan Ramadan