Mafifitan Ayyukan Mai Azumi

0
308

Ayyukan Mai Azumi – Akwai ayyuka mafifita da ya kamata mai azumi ya kusance su; daga ciki akwai:

1. Karatun Alƙur’ani Mai Girma, wato mai azumi ya lazimci karatun Alƙur’ani da kuma fahimtar saƙon da yake cikinsa, amma idan ba za a iya karatun ba, to babu laifi a lazimci majalasin karatun, wato wajen da ake karantawa tare da fassara Alƙur’ani.

Nana A’isha, Abu Huraira da Ibn Abbas (Radiyallahu Anhuma), sun faɗa cikin hadisin Manzon Allah (Sallallahu Alaihi Wasalam) cewa, “Mala’ika Jibrilu ya kasance yana karanta wa Annabi (Sallallahu Alaihi Wasalam) Alƙur’ani a kowane dare na watan Ramadana, sau ɗaya a kowacce shekara, sai ya karanta masa sau biyu a shekarar da zai yi wafati”. (Sahihul Bukhari 4997 – 4998, Sahihu Muslim 2450).

Wannan hadisi ya nuna cewa karatun Alƙur’ani shi ne mafificin aikin ibada ga mai yin azumi a watan Ramadana, don haka, sai a himmatu da karatunsa.

2. Kyauta, ana son mai azumi ya yawaita kyauta ta hanyar ciyar da jama’a da kuma sakin hannu gare su, da taimakon gajiyayyu da makusanta. An karɓo hadisi daga Abdullahi Ibn Abbas (Radiyallahu Anhu) cewa, Annabi (Sallallahu Alaihi Wasalam) ya fi kowa kyauta, kuma ya fi yawaita kyautarSa a cikin watan Ramadan, musamman a lokacin da yake ganawa da Mala’ika Jibrilu. (Bukhari 4997).

Haka nan Ibn Abbas (Radiyallahu Anhu) ya ce, “Alherin Manzon Allah (Sallallahu Alaihi Wasalam) ya fi sakakkiyar iska”. (Bukhari 1902).

3. Sallar Nafila, ana so mai azumi ya yawaita nafila, musamman Ƙiyamul Laili (wato sallar dare); saboda kwaɗaitarwar da Manzon Allah (Sallallahu Alaihi Wasalam) ya yi cikin hadisin Abu Huraira (Radiyallahu Anhu) cewa, “Duk wanda ya tsaya yin sallar Ƙiyamul Laili, yana mai imani da neman lada, za a gafarta masa zunubansa da suka gabata”. (Bukhari 2009).

Haka nan cikin hadisin Abu Dharrin Alghiffariy (Radiyallahu Anhu) ya ce; Manzon Allah (Sallallahu Alaihi Wasalam) ya ce, “Wanda ya yi sallar asham tare da liman, har ya idar, za a rubuta masa ladan ƙiyamul laili”. (Sunan Tirmizi 646, Ibnu Majah 1327).

4. Yawaita zikiri, ana son mai azumi ya yawaita yin zikiri da salatin Fiyayyen Halitta (Sallallahu Alaihi Wasalam); domin akwai gwaggwaɓan lada ga yin zikiri da salatin Annabi (Sallallahu Alaihi Wasalam).

5. Ciyar da mai azumi abin buɗa-baki, yana daga cikin mafificiyar ibada ciyar da masu azumi abin buɗa-baki. Hadisi ya tabbata daga Annabi (Sallallahu Alaihi Wasalam) cewa; “Duk wanda ya ciyar da mai azumi abin da zai yi buɗa-baki, yana da kwatankwacin ladan mai azumin, ba tare da an rage ladan wanda ya ciyar ba”. (Sunan Tirmizi 647, Ibnu Majah 1746).

A nan, muna jan hankalin masu hali a kan su taimaka wa mabuƙata, musamman makusantansu. Domin za ka iske mutumin da yake da hali a unguwa; amma kaso mafi yawa suna rasa abin da za su yi buɗa-baki, a wani lokacin kuma, masu ƙoƙarin yin sadakar ma, za ka iske suna yi ne cikin rashin kyautatawa, face kaɗan. Yana da kyau masu hali da shugabanni su gane, taimakawa a irin wannan lokaci; cikin iklasi da neman yardar Allah, wallahi rabautuwarsu ce. Amma ina tausayi da rahama, kai ka ci mai kyau, amma maƙwabtanka suna fama da yunwa!

Yana da kyau ku ciyar daga mafi kyawun dukiyarku; kuma cikin abu mai kyau; tare da sakin zuciya da jin dadi da walwala.

6. Umarah, yin Umarah cikin watan Ramadana na daga cikin mafifitan ayyuka; don haka, mutumin da yake da iko sai ya ɗauki azama. Manzon Allah (Sallallahu Alaihi Wasalam) ya ce, “Yin Umarah a cikin watan Ramadan daidai yake da aikin Hajji”. A wata ruwayar kuma Ya ce, “Wanda ya yi Umarah a watan Ramadan; tamkar ya yi aikin Hajji ne tare da Ni”. (Sahihul Bukhari 863).

A nan ma, muna ƙara jan hankali, musamman ga waɗanda sun yi Umara; amma suna ta ƙara maimaitawa, alhali maƙwabtansu na fama da yunwa, da baƙin talauci. Ku sani, duk da wannan falala ta Umara ta nafila; duk da wannan lada, ciyarwa ita ta fi sama da Umarar da za ka tafi, alhali ga maƙwabtanka; ko danginka na fama da yunwa, da wahala ta rashin abin da za su ci, idan za su yi sahur; ko za su ci, idan za su yi buɗa-baki.

Kuskure ne alhazan ke yi, sun je, ba sau ɗaya ba; ba sau biyu ba, su ƙara niƙar gari su tafi, alhali ga mabuƙata nan a kewaye da su.

Domin karanta cikakken bayani a kan Abubuwan Da Suke Ɓata Azumi danna nan.

Domin karanta cikakken bayani a kan Falalar Azumin Watan Muharram danna nan.

Wannan bayanin an ciro shi ne daga Littafin Guziri Ga Mai Azumin Ramadana (Bisa Koyarwar Alƙur’ani Da Sunnah); wanda Ibrahim Baba (Ibrahim Garba Nayaya (Baban Fauzan) ya wallafa shi; Don karanta cikakken Littafin danna nan.

labarin da ya wuceAbin Lura Idan ‘Ɗan Ka Ko ‘Yar Ka Sun Kai Shekarun Farko Na Tashen Balaga
Labarin na GabaCiwon Suga (Diabetes)