An karɓo daga Abu Huraira (Radiyallahu anhu) ya ce:
“Manzon Allah (Sallalahu alaihi wassallam) Ya ce, “Mafificin azumi bayan Ramadan, shi ne azumin watan Muharram, Mafificiyar sallah bayan sallar farilla ita ce sallar dare”. (Muslim 1163. Ibn Majah 1742).
Domin karanta cikakken bayani a kan Azumin Tasu’a Da Ashura danna nan.
Wannan bayani an ciro shi ne daga littafin Ingantattun Nafiloli Da Falalarsu wanda Usman Abubakar Muhammad (Shehu Mansur Dala ) ya wallafa shi domin karanta cikakken littafin danna nan.