Siffofin Manzon Allah (Sallallahu alaihi wassallam)

0
820

Manzon Allah tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi ya kasance mai kyawun jiki ne, ba mai ƙiba ba ne, kuma ba siriri ba ne, ba dogo ba ne, kuma ba gajere ba ne, fari ne shi tas, kai ka ce da azurfa aka yi shi, mai tajajjen gashi ne, mai yawan gemu ne, mai yalwar kai ne da hannaye da kafafuwa.

Kuma Manzon Allah tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi, mai kyakkyawar fuska ne, kamar rana da wata, kuma fuskarsa kewaye take, kuma yana da faɗin kafaɗu. Ga shi kuma da daɗin ƙamshi.

Domin karanta cikakken bayani a kan Zancen Manzon Allah (Sallallahu alaihi wassallam) danna nan.

Wannan bayani an ciro shi ne daga Littafin Manzon Allah Annabi Muhammad (sallallahu alaihi wassallam) Kamar Ga Ka Ga Shi, wanda Abubakar Abbas ya wallafa shi domin karanta cikakken littafin danna nan.

labarin da ya wuceSunayen Manzon Allah ( Sallallahu alaihi wassallam)
Labarin na GabaZancen Manzo (Sallahu Alaihi Wasallam).