Zancen Manzo (Sallahu Alaihi Wasallam).

0
482

Annabi tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi, ya kasance mai yawan shiru ne, kuma idan zai yi magana ba ya faɗar son zuciya. Allah Maɗaukaki ya ce:

1. Saboda ƙamshin jikin Manzon Allah (Sallallahu alaihi wassallam) har ma sahabbai sukan tari guminsa a kwalba, domin shafawa a tufafinsu idan sun yi kwalliya.
“Manzon Allah (sallallahu alaihi wassallam) ba ya faɗar son zuciya”
Kuma ba ya faɗar wata magana sai gaskiya, zancensa a bayyane yake daki-daki, yadda duk wanda ya zauna ya saurare shi, zai iya haddace shi, kuma ya kasance yakan maimaita kalma sau uku don a fahimce shi, kuma idan Manzon Allah tsira da amincin Allah tabbata a gare shi,
Surar Najmi, aya ta 3. yana yin magana wanda yake idonsa biyu zai ji shi, kuma mai barci ba zai farka saboda maganarsa, ba ƙari akan haka, Allah ya ba shi kalmomi masu tarin bayanai.

Domin karanta cikakken bayani a kan Karatun Manzon Allah (sallallahu alaihi wassallam) danna nan.

Wannan bayani an ciro shi ne daga littafin Manzon Allah Annabi Muhammad (sallallahu alaihi wassallam) Kamar Ga Ka Ga Shi, wanda Abubakar Abbas ya wallafa shi domin karanta cikakken littafin danna nan.

labarin da ya wuceSiffofin Manzon Allah (Sallallahu alaihi wassallam)
Labarin na GabaKaratun Manzon Allah (Sallallahu alaihi wassallam).