KAN FASALIN ALWALA
• Wanda ya manta da wata farilla daga gaɓoɓinsa, idan ya tuno sai ya aikata ta da abinda ke bayanta, idan kuma ya yi nisa sai ya aikata ta ita kaɗai, ya kuma sake abinda ya sallata bayan faruwar abin.
• Idan kuma ya bar sunna, to sai ya aikata ta ita kaɗai ba zai sake sallah ba.
• Wanda kuma ya mance lam’a sai ya wanke ta ita kaɗai da niyya, in kuma har ya yi sallah bayan faruwar hakan toh sai ya sake ta.
• Wanda ya tuna da kurkurar baki ko shaƙa ruwa bayan ya riga ya ya fara wanke fuska, to ba zai dawo gare su ba har sai ya gama alwalarsa, sannan sai ya yi su.
• Tsettsefe ‘yan yatsun hannuwa yana wajaba, an so a tsettsefe ‘yan yatsun ƙafafuwa, tsefe gemu mara duhu yana wajaba a cikin alwala, tsefe gemu yana wajaba a cikin wanka koh da mai duhu ne.
AKAN FASALIN ALWALA (2)
• Ba ya halatta ga wanda ba shi da alwala ya yi sallah, koh ɗawafi, ko ya taɓa Alqur’ani ko da a cikin gafakarsa ne, ba da hannunsa ba sai dai idan juzu’i ne ga mai neman ilimi a cikinsa.
• Yaro a wajen taɓa Alqur’ani kamar babba yake, amma laifin yana wuyan wanda ya ba shi Alqur’anin ya taɓa.
• Wanda ya yi sallah da gangan ba tare da alwala ba to shi kafiri ne. Allah ya kiyashe mu.
Danna nan don karanta Mu Koyi Addini Kashi Na Farko
Edita; Rumasa’u M. Kallamu