Cikakken Bayani A Kan Sahur

0
429

Manzon Allah (Sallallahu Alaihi Wasalam) ya kwaɗaitar da yin sahur; har Ya ambata cikin falalar sahur a hadisin Anas Ibn Malik Radiyallahu Anhu cewa, “Ku yi sahur, domin haƙiƙa akwai albarka a cikin yin sahur” (Sahihul Bukhari 1923).

An karɓo hadisi daga Salman (Radiyallahu Anhu) cewa, Manzon Allah (Sallallahu Alaihi Wasallam) ya ce; “Albarka na cikin abu uku: jama’a, abincin rashi da kuma abincin sahur”. (Ɗabrani cikin Mu’ujamul Kabir 6127).

Manzon Allah (Sallallahu Alaihi Wasalam) ya ambaci sahur da kumullo mai albarka; kamar yadda yake cikin hadisin Al’irbadh Bn Sariyata, da Abud-Darda’a (Radiyallahu Anhu) cewa Manzon Allah (Sallallahu Alaihi Wasalam) ya ce; “Ku taho mu yi kumullo mai albarka, yana nufin sahur”.

Haka nan hadisi ya tabbata daga Manzon Allah (Sallallahu Alaihi Wasallam) cewa; “Sahur abinci ne mai albarka. Don haka kada ku bar shi, ko da ruwa ne ɗayanku ya kurɓa. Haƙiƙa Allah da mala’ikunsa na yin salati ga masu yin sahur”. (Sahih Targhib wal Tarhib 1066).

Sannan Manzon Allah (Sallallahu Alaihi Wasallam) ya bambanta azuminmu da na ma’abota littafi (Yahudu da Nasara); da sahur, kamar yadda ya ce, “Bambancin da ke tsakanin azuminmu da na ma’abota littafi; shi ne yin sahur”. (Sahih Muslim 1096).

Game da lokacin da ake yin sahur ko bari kuwa, akwai hadisai da suka zo a kai. An karɓo hadisi daga Anas Ibn Malik (Radiyallahu Anhu), daga Zaid Ibn Thabit (Radiyallahu Anhu) ya ce; “Mun yi sahur tare da Annabi (Sallallahu Alaihi Wasallam) sannan sai ya tashi zuwa sallah. Sai na cewa Anas, “Yaya tsawon da ke tsakanin kiran sallah da yin sahur ɗin yake? Sai ya ce; “Gwargwadon karanta ayoyi hamsin”. (Bukhari 1921, Muslim 1097).

Wani hadisi daga Sahl Ibn Sa’ad ya ce; “Na kasance ina yin sahur cikin iyalina; bayan wannan sai na yi gaggawa domin samun sujada (sallah) tare da Manzon Allah(Sallallahu Alaihi Wasalam)”. (Bukhari 1920).
Wannan hadisi ya nuna ana yin sahur ne dab da ketowar alfijir.

Amma yayin da mutum ke yin sahur, sai alfijir ya keto, to zai ƙarasa cin abincinsa ne; dogaro da hadisin Abu Huraira (Radiyallahu Anhu)cewa, Manzon Allah (Sallallahu Alaihi Wasalam) ya ce; “Idan ɗayanku ya ji kiran sallah alhali ƙwarya tana hannunsa, kada ya ajiye ta, har sai ya biya buƙatarsa”. (Abu Dawud 2060).

Amma a nan mutum ya yi hattara kada ya mayar da wannan ita ce ɗabi’arsa; wato jinkirtawar da zai fita daga lokaci.

Wani abin lura game da alfijir, Manzon Allah (Sallallahu Alaihi Wasalam) ya nuna iri biyu ne cikin hadisin da aka karɓo daga Ibn Abbas, Manzon Allah (Sallallahu Alaihi Wasallam) ya ce; “Alfijir iri biyu ne, na farko ba ya haramta abinci; kuma ba ya halatta sallah, na biyu kuwa yana haramta abinci, yana halatta sallah”.

A wannan gaɓar, wajibi a ja hankalin ladanai waɗanda ke kiran sallah, wato lokacin da ake daina yin sahuur; domin ba sa kula da fitowar alfijir. Misali, a kalandar Jihar Yobe; alfijir zai hudo a farkon azumi da misalin ƙarfe 4:37 a bana; yayin da a ƙarshen azumi zai kai ƙarfe 4:40. To amma za ka ga ladanai ba sa kiran sallar daina sahur (assalatu), sai misalin ƙarfe 4:55; wasu ma sai ƙarfe 5:00, alhali da yawa daga cikin mutane sun dogara ne da kiran assalatu wajen daina cin abinci.

Haƙiƙa ladanai su sani, yin hakan kuskure ne da kuma ɗaukan haƙƙin al’umma; don haka su ji tsoron Allah, da sannu za su tsaya a gabansa, kuma za a tambaye su kan dukkan abin da suka aikata.

Domin karanta cikakken bayani a kan Buɗa-baki danna nan.

Domin karanta cikakken bayani a kan Ɗabi’ar Lokaci, Saurin Wucewa danna nan.

Wannan bayanin an ciro shi ne daga Littafin Guziri Ga Mai Azumin Ramadana (Bisa Koyarwar Alƙur’ani Da Sunnah); wanda Ibrahim Baba (Ibrahim Garba Nayaya (Baban Fauzan) ya wallafa shi; Domin karanta cikakken Littafin danna nan.

labarin da ya wuceCikakken Bayani A Kan Buɗa-baki
Labarin na GabaMa’anar Azumi A Musulunci