Yadda ake aikin Hajji a saukake

0
1803

Hajji wajibi ne akan kowanne musulmi sau daya acikin rayuwar mutum. Matukar akwai hali saboda umarni ne na  Allah (SWT) “….Allah na da hakki akan mutane na ziyarar daki ( ka’aba) ga wanda ya samu ikon zuwa gareshi… “. ( Aali Imraan :197).

Kuma ku cika hajji da Umra domin Allah… ( Baqara:196).
Wadanda su ke da damar yin aikin hajji, amma kuma su ka ki yi, hakika sun yi babban Sabo, hakan na nuna kafurci. Ga wanda ya sauke aikin hajjinsa nafarko to lalle ya sauke farali, kara yin aikin hajji bayan sauke farali, to wannan Karin ya zama nafila.

“Karbabban aikin hajji nawanke dukkanin zunubai”

MIKATI:Annabi (SAW) ya ce :”Wadannan kebantattun wurare ne da ake ce mu su “Mawaqit” ko mikati. Bai halatta ga maniyyaci ya wuce wadannan wurare ba tare da ya yi harama ( niyya, sa ihrami) ba.

Mafi yawan mutanen Afurika na tafiya ne ta jirgin sama, wadanda ke sauka a garin madina ko jidda, saboda haka mikatinsu daya ne da mutanen madina idan a madina suka sauka, haka kuma idan a jidda suka sauka to mikatinsu shi ne ake Kiran Shi da aljuhfa. Shi wannan wuri hamada ce ana kiran Garin  Juhfa, kamar yadda yake a hoto na kasa.

Mikatin ka ya danganta daga inda kataso ko inda zaka sauka, dan haka duk inda ka sauka sai ka tambayi mikatinsu.

HARAMA (IHRAAM ): Kowanne maniyyaci ya shiga ihrami daga mikatin da ya ke kan hanyarsa. Ga Maza za su cire tufafinsu su sa Ihrami guda biyu. Wato Gyauto da za su rufe kasan jikinsu, Mayafin kuma a rufe ragowar saman jikinsu.

Mata kuwa za su sa suturarsu ta al’ada su rufe ko ina banda fuska da hannayensu. Kuma ba za su sa liqabi ba da safar hannu.

NIYYA : Ana yin niyya ne a mikati yayin sanya ihrami, Annabi (S. A. W) ya ce :”Kowanne aiki sai da niyya ..”.
Mutum zai yi niyya a zuciya sannan ya fadi :”Labayk Allahumma Labayk. ”
Da wannan mutum ya fara rukunan umra ke nan. Kamar yadda ake bude sallah da fadin Allahu Akbar.

Ka ga mai harama zai ce :”Labayk Allahumma bi-umrah ” . Ko “Labayk Allaahumma bi-hajj ” Ga mai yin Tammattu’i wato hada umra da hajji.
Wanda duk yai harama da Umra,  dole ya kammala umararsa sannan ya cire Ihraminsa. Ya zauna ya jira a makka har sai Takwas ga Dhul-Hijjah . Sai ya sake sa Ihraminsa anan makka.
Mai yin Tammattu’i akwai bukatar yai yanka. Wato yanka dabbarsa (hadaya)  a wajen aikin hajji ranar Goma ga watan Dhul-Hajj.
“…To, idan kuna cikin aminci, to, wanda ya ji dadi da umra zuwa hajj, sai ya biya abin ya saukaka daga hadaya… “.(Baqara :196).
Rukunan farko na umra shine sanya ihrami. Sai Niyya a zuciya, sai kuma harshe ya furta “Labbayk Allaahumma bi-Umra ” ko ” Labbayk Umrah “.
Wanda duk ya shiga ihraminsa to ba zai yi wadannan  abubuwan ba,  su ne :
Saduwa Da iyali.

Sanya Tufafi dinkakke ga maza.
Ba sa Wandoriga, takalmi,  safa
Ma’aurata ba za su yi Sumba,  runguma  da ire-iren wadannan ba.
Saboda fadin Allah :
“…To,  wanda ya yi niyyar hajji a cikinsu, to,  babu jima’i,  kuma ba bu fasikanci, kuma Babu jayayya a cikin hajji… “.
(Baqara:197).Ka na gama harama sai kuma Talbiyya. Wato fadin :
Labbayk Allaahumma Labayk, Labbayk laa sharika laka Labbayk, Innal Hamda Wa ni’imata laka wal mulk laa sharika lak.  Na amsa maka Ya Ubangiji! Na amsa maka. Na amsa maka,  ba Ka da abokin tarayya. Na amsa maka. Hakika Godiya da Ni’ima duk na ka ne,  da mulki. Ba Ka da abokin tarayya.
Za ka cigaba da talbiyya tun daga mikati har zuwa makka. Za ka daukaka murya ka yi ta fada. Har ka isa makka cikin masallacin harami, ka fuskanci ka’aba. Sai Rukuni na biyu na Umra.

Dawafin dakin Allah na nufin yin zagaye bakwai. Za ka fara dawafin da ga bakin Dutse. Ka na mai fadin kabbaraAllahu Akbar ” . Sai ka cigaba da zikiri da addu’a. Idan ka zo tsakanin kusurwar Rukunul Yamani da hajarul Aswad. Sai a kowanne kewaye na dawafinka, ka dinga fadin wannan addu’ar :
” Yaa Ubangijinmu!  Ka ba mu mai kyau a duniya da Kuma mai kyau a lahira, kuma ka kiyashe mu azabar wuta “. (Baqara:201).
Idan maniyyaci ya samu dama, sai ya sumbaci bakin Dutse. Ko kuma ya shafa shi da hannunsa. Ko da wani abu sai ya sumbaci abin. Ko Idan akwai taron mutane sosai. Kawai idan ya yi nuni da hannunsa ya ma isa. Ba’a bukatar ka cutar da su. A wajen kokarin sai ka sumbaci bakin Dutsen.
Wannan dawafin Qudum shine ake kira dawafin isowa. Zagayen ukun farko na dawafin ana yinsa cikin hanzari ammafa ba gudu ba. Sunnonin wannan dawafi ga namiji ya kwaye kafadarsa ta dama. Wato ya sa tsakiyar mayafinsa karkashin hamatarsa ta dama. Gefen mayafi biyo kuma ya sa su a kan kafadarsa ta hagu.
Bayan ka gama dawafi sau bakwai. Sai ka yi sallah Raka’a biyu a bayan makami Ibrahim. Idan ba Ka samu dama ba to a ko ina ka sami fili acikin masallacin sai ka yi sallarka.
Daga nan ya je ya sha Zam-zam har ya cika cikinsa. Kuma ya zuba shi a jikinsa. Zam-zam ruwa ne mai albarka da ya ke maganin cututtuka.

Mai harama zai tafi zuwa ga wani karamin dutse ana ce masa Safa. Sai ka karanta wannan : “Lalle dutsen safa da na Marwa su na daga cikin Alamomin addinin Allah… ” ( Baqara:158).
Sai kuma ka ce : “Na fara da abin da Allah Ya fara dashi “.
Sai ka hau kan dutsen safa ka fuskanci ka’aba ka ce :
Allahu Akbar, Allahu Akbar, Allahu Akbar.
La’ilaha illal lah, wahdahu laa sharika lah,  lahul mulku wa lahul hamd,  wa huwa ala kulli shai’in qadeer. La’ilaha illal lah wahdah,  anjaza Wa’adah, wa nasara abdah,  wa hazamal ahzaba wahdah.
Babu wani abin bautawa da gaskiya sai Allah, wanda ba shi da abokin tarayya. Mulki na gareshi, kuma godiya ta tabbata a gareshi. Kuma shi mai iko ne akan komai. Babu wani abin bautawa da gaskiya sai Allah , shi kadai dinsa,  Allah Ya zartar da alkawarinsa,  kuma ya taimaki bawansa, kuma ya kayar da rundunonin kafirci shi kadai dinsa.
Sai ka yi Addu’a ko da wanne irin yare ne ko da Hausa ne kuwa.
Kuma ka kara addu’ar can ta sama. Ka sake wasu adduoinka a karo na biyu. Ka kara maimaita addu’ar can a karo na uku. Kuma ka karawa kanka adduoi.
Sai ka sakko ka wuce zuwa Marwa. Idan ka zo ga alamomin nan guda biyu. Sai ka kara daga kafa ( gudu)  a tsakaninsu. Ammafa kafin ka zo gare su. Bayan ka wuce su, sai ka yi tafiyar ka ta al’ada.
Wannan gudun ya na tuno mana yadda Mahaifiyar Annabi Isma’il Wato Hajara ta yi ta fama. Hakurinta da juriyarta domin yardar Allah.
Haka mutum zai ta maimaitawa tsakanin safa zuwa Marwa . Lalle ne mutum ya yi kokarin kaucewa  adduoin da ba su inganta ba.

Wannan shine Rukuni na hudu. Kuma na karshe acikin aikin umra. Wato aski ko saisaye. Kammala shi ne zai sa mutum ya fita daga Ihraminsa.
Aske kai gaba daya shine ya fi akan saisaye. Sai dai ga wanda niyyarsa Tammattu’i ce. To wannan saisaye ya fi ma sa. Ragowar gashin sa zai barshi har sai ya kammala Rukunan aikin hajjinsa. To sai ya sake gaba daya.
Ka na gama wannan,  to za ka aika ta dukkanin abubuwan da ba za ka yi su ba. Kamar su saduwa da iyali,  da sanya tufafi na al’ada,  da sa safa,  da hula da dai Sauransu.
( Baqara:196).
A zamanka na jiran lokacin fita aikin hajji. Za ka yawaita karatun Qur’ani , da ziyarar malamai,  da sallah a harami. Za ka yi dukkan abin da ka ke so. Ammafa banda asarar Lokaci, wajen hira da abokanai ko musu da su . Ka dage sosai wajen yawan ambaton Allah har zuwa Takwas ga wata ya zo. To sai ka sake shiga ihraminka,  harama amma a wannan karan da hajji ne.

RUKUNAN AIKIN HAJJI .

-Zaman Mina
-Tsayuwar Arfa
-Zaman muzdalifa
Takwas ga wata ake fita domin gabatar da aikin hajji. Tambayar ita ce , shin akwai bukatar mutum ya dawo mikati domin yin harama? A’a mutum zai yi haramarsa a ko ina daga inda ya ke zaune a makka. Za ka iya yi daga masaukinka (hotel )  ko daga masallacin harami.
Za ka yi Niyya a zuciyarka sai kuma fadar : “Labbayk Allaahumma bi-hajj “. Ko labbayk Hajjatan “.
Wannan ya Kawo mu wata muhimmiyar tunatarwa akan Niyya. Wasu kan yi rashin Lafiya alokacin da su ke aikin hajji. Har ya zama ba za su iya kammala Rukunan aikin hajjinsu ba. Idan haka ta kasance, to fa dole mutum ya dawo a shekara mai zuwa. Zai sake hajjinsa, Kuma yai yanka.
Sunnace mutum ya yi niyya tare da fadar wannan addu’ar. Ita Wannan addu’a za ta zama kariya daga abubuwan da za su faru ba tare da sani ba.
Addu’ar ita ce : Labbayk Allaahumma bi-hajj “.
Kuma ka kara wannan :
“Allaahumma Muhalli haisu habastani “.
Wanda duk ya yi wannan to ko da ya kasa cikatawa, saboda rashin Lafiya. To babu yanka akansa. Wato haka Allah Ya kaddarawa bawansa ba zai cikata ba.

ZAMAN MINA :Zaman Mina na farawa ne daga takwas ga watan Dhul-Hajj. Maniyyaci zai fita i zuwa Mina. Ana son ya zauna ya yi sallar azahar, da la’asar, da Magriba,  da isha,  da kuma asuba.Washegari Wato tara ga wata kuma da safe zai fita zuwa filin Arfa.

TSAYUWAR ARFA :Za ka zauna a arfa ka yi ta yin talbiyya :”Labbayk Allaahumma Labayk “. Za ka iya yin karatun Qur’ani da yawaita addu’oi, ko  da kuwa da irin harshenka ne  Hausa ko turanci .
Ka yawaita kabbara “Allaahu Akbar ” . Tasbihi, da Hamdala “Alhamdulillah “. Ba za ka bar filin Arfa ba har sai rana ta fadi. Duk wanda bai samu damar halarta arfa ba. To kuwa bashi da hajji saboda Annabi (S. A. W) ya ce : Tsayuwar Arfa ita ce Hajji “.
Abin tambayar anan shi ne,  ko dole ne mutum sai ya hau kan dutsen arfa ne? Amsar ita ce a’a  saboda Annabi (SAW)  bai yi ba. Shi ya tsaya ne akan dabbarsa ( Rakumi) a gindin dutsen arfa.

ZAMAN MUZDALIFA :Idan rana ta fadi,  sai ka taho muzdalifa. Anan za ka yi sallar magariba da isha gaba daya . Magariba yadda ta ke, amma isha kasaru ( Wato raka’a biyu). Anan muzdalifa za ka zauna har sai asuba ta yi, sai ka yi sallar asuba. Kwana a Muzdalifa wajibine saboda Allah Ya ce :” …Sa’anan idan kun taho daga Arafat, sai ku yi ta ambaton Allah a Wurin Masharil Harami,.. (Baqara :198).
Masharil harami na nufin Muzdalifa.
Za ka yi ta Hailala “La ilaha IllAllah ” Tasbihi :”SubhaanAllah ” kabbara da su talbiyya.

GOMAN ZULHAJJ: Goma ga watan Zulhajj babbar rana ce. Kuma rukunanta su ne :
Jifan Shedan
Yanka ( hadaya)
Aski
Dawafi

JIFA :Za ka tsinci tsakwankwani guda bakwai. Ka yi jifa da su kowanne jifa ka na fadarAllahu Akbar “. Daya bayan daya. Ba’a jefa duka tsakwankwani bakwai Lokaci guda.
Za ka matso kusa sosai da jamra, alokacin da za ka yi jifa. Domin ka da ka cutar da mutane da ke gabanka.
Wannan ginin jamra da ake jifa,  ba ita ce shaidan ba. Za ka ga wasu na zagi, da tsinuwa,  har da jifa da takalmi Wannan duk bai dace ba. Ana yin jifa ne domin biyayya ga umarni Allah. Ko da kuwa mutum bai san hikimar aikata hakan ba.

YANKAN HADAYA :Bayan gama jifa, sai ka taho Mina wajen yanka hadayarka. Anfi so ace kai ka yanka da kanka. Amma babu laifi ka sa wani yai maka yanka. Har ma za ka iya biyan kudin hadaya,  ta bankin Rajhu Bank da ke nan Mina.
Za ka iya yanka dabba ta kowacce irin shekara saboda Allah Ya ce : …To, Idan an kange ku, to, ku bayar da abin da ya saukaka na hadaya… “(Baqara :196)
Kun ga ashe ba’a tantance shekarunba. Haka kuma za ka iya ci daga cikin hadayarka.
ASKI : Bayan gama hadayarka sai kuma ka yi aski.

DAWAFI :Za ka koma makka ka yi dawafi guda bakwai kamar yadda ka yi farkon zuwanka. Sai dai wannan sunansa dawafin Ifadah. Shi ba’a hanzari a Zagayen ukun farko. Haka kuma babu fito da kafada. Za ka yi dukkan Zagayen dawafin ne,  ka na tafiya kawai. Za ka iya yinsa cikin tufafinka na al’ada.
Mutum na fita daga Ihraminsa ne lokacin da ya gama jifa. Haka ma za yi komai da aka hana ka yinsu. Amma banda saduwa da iyali.

RUKUNAN DA AKE GABATARWA A RANAR GOMA GA WATAN ZUL-HAJJI:

Jifa jamra Karama
Yanka hadaya
Aski
Dawafi
An tambayi Annabi (SAW)  akan yin su ajere. Ko fara wani kafin wani. Sai ya ce :”Ku yi su bakomai, Ku yi su bakomai “.
Saboda haka ma ake samun wadanda su ke cikin aikin hajji kungiya guda. Ammafa wannan na dawafinsa da safe, wannan da Rana.

RANAKUN SALLAH: Abin da ya rage ma yanzu shi ne ka zauna kwanaki uku a Mina. Menene abin yi a wannan zaman na Mina.?
A lokacin zaman Mina za ka ci ka sha. Kuma za ka yawaita ambaton Allah. Kuma za ka iya ci daga yankan hadayarka. Idan kuwa kudin ka bayar,  to ba za ka ganshi ba. Za’a yi ma sadaka da shi ne.
Wadannan Ranaku, su ne Ranakun farin ciki da jin dadi .Wato Ranakun Idin sallah.
A Rana ta uku kamar azahar. Za ka fita domin yin jifa jamra ukun gaba daya. Za ka fara jifa da ga karamar jamra. Sai ta tsakiya,  sai kuma babbar jamra. A kowacce ka yi jifa da duwatsu guda bakwai . Kuma akowacce ka na fadin :”Allaahu Akbar “.

JAMRA TA FARKO :Bayan ka gama jifa, za ka tsaya ka roki duk abin da ka ke so.
JAMRA TA BIYU : Ka dan dakata sai ka yi ta addu’a.
JAMRA TA UKU :Za ka bar wajen ba tare da yin addu’a ba.
Za ka gabatar da wannan jifa ne,  a kwanaki ukun nan. Wato 11, da 12, da 13 ga Zul-Hajj . Ana kiran wadannan Ranakun :”Ayaam Tashriq “. Wato Ranakun bushewa. Saboda yadda adacan alhazai ke shanya nama ya bushe. Su na ajiye shi har su kammala aikin hajjinsu,  su tafi gida da Naman su. Kasancewar alokacin da can Babu Na’urar sanyi ta adana Nama.
Ka na gama wannan jifa, to ka kammala aikin hajji. Za ka iya dawowa gida wajen iyalanka. Har ma ana samun wasu su dawo gida washegarin da su ka kammala hajjinsu.
Allah Ya ce :”
( Baqara: 203).
Za ka iya barin Mina tun a ranar 12 ga wata. Sai ka hada duka jifa. Wato da na 12, da 13, a Rana guda ( Duka a 12 ga wata ke nan).
Ka ga akowacce jamra za ka yi jifa da duwatsu bakwai na ranar 12 . Sai kuma ka kara wasu bakwai na ranar 13. Haka za ka yi a Karama, da ta biyu,  da jamra ta uku.
Za ka yi hakanne Idan ba ka son zaman Mina. Wato za ka koma gida. Allah Ya ce :”  ( Baqara:203)
Hakama dai ana so ( Mustahabbi ne ) ka yi dawafin bankwana ( dawafin wadaa) kafin ka tafi garinku.
Annabi (SAW) ya ce :Ka da mutum ya bar makka,  a tafiyarsa ta karshe har sai ya yi dawafin karshe a daki mai tsarki “.

MATA DA JININ HAILA A LOKACIN AIKIN HAJJI: Idan Mace ta fara jini a farkon Lokacin da ta ke gabatar da Rukunan aikin hajjinta. Ko kuma yayin da ta kusa gama aikin hajji. To fa za ta cigaba har ta kammala dukkanin rukunai. Sai dai kawai banda dawafi. Shi za ta jinkirtashi, har sai ta yi tsarki tukunna. Sai ta je ta yi dawafi.
Haka kuma ko da ta fara jini ne, da ta fara Zagayen farko na dawafin isowa ( dawafin Qudumi)  . To,  za ta cigaba da dukkanin Rukunan aikin hajji. Sai ta kammala su,  ta jira ta yi tsarki. Sannan ta yi dawafin ta na bankwana ( dawafin Ifada).
Hajji da umrarta ba su baci ba. Saboda haka jinin haila ba matsala ba ne ga mata alokacin aikin hajjinsu.
FIFIKON HAJJIN TAMATTU’I: Mafificin aikin hajji shi ne tamattu’i. Wato wanda aka hada umra da hajji. A shi ne ake samun lokaci a tsakaninsu. A lokacin umra ka sanya ihraminka. Da ga ka kammala, ka ajiye har sai lokacin hajji ka kara sawa.
Wasu za su ce, Annabi (SAW) ya yi hajjin Qirani. To kuma yaya za’ayi mu ce kuma tamattu’i ta fi fifiko?
Annabi(SAW) ya ce :” Da ace ban taho da hadayata tare da ni ba, da na cire ihramina,  sai in mayar da ita umra”.
Wato wanda ba zai cire Ihraminsa ba,  shi ne wanda ya taho tare da hadayarsa tun kafin mikati. Allah Ya ce : “..Wala tahliku…. Mahilla.. “(Baqara:196).
Annabi (SAW) bai bar sahabbansa sun yi qirani ba.
Ga wanda ya yi tamattu’i, sai ya yi hadaya a 10 ga watan  Zul-hajji. Wanda kudinsa Bai isa yai hadaya ba. Ko ya nemi dabbar saya, ya rasa. To sai ya yi azumi guda uku. Sannan Idan ya dawo gida ya yi guda 7.
Allah Ya ce : “Faman lam yajid… Hadiril masjid haraami “(Baqara:196)
Ga masu fama da talaucin da ba za su iya sayen hadaya ba. Za su azumci kwanaki uku  11, da 12, da 13 ga Zul-Hajj . Sauran ragowar azumi 7 sai  sun koma kasarsu.
Allah Yai dadin tsira da aminci ga fiyayyen halitta. Annabi (SAW)  da alayensa da sahabbansa.

Ku kasance a wannan gida mai albarka don cigaba dasamu ingantattun shirye-shiryemmu.

BAR AMSA

Please enter your comment!
Please enter your name here